3

13 2 1
                                    


                 ➳༻❀✿❀༺➳

Zaune suke suna hira irin da uwa da d'a gwanin ban sha'awa.

'Mum, yaushe yaran nan zasu zo ne ni fa nayi missing dinsu.'

'Fa'iz kenan! Tunda har kayi magana na san daga zuciyarka kayi kewarsu, amma ka san kai da ganinsu sai sun yi hutu ko ba haka ba.'

'Sannu Mum, hira kuke kuka barni a sama cikin kadaici', ta fada a shagwabe tana saukowa daga stairs.

Ai yana ganinta ya daure fuska tamau, shi kanshi ba zai iya cewa fa dalilin da yasa ya tsani Fadeelah ba.
Wataqila halinta na ballagazanci ne ko kuma shishshiginta.
Duk da dai dama bai da sakin fuska sai idan yana tare da Mum ko Hanan da Hilwa.

'Ahhh sannu da saukowa Fadeelah 'yar hutu' inji Mum.

'Mum ni zan je wurin Ammar sai na dawo'

'Toh Fa'iz a dawo lafiya'.

'Mum wai me yasa Ya Fa'iz ya tsaneni ne, ko dan mun dade sosai bamu hadu ba?' Ta fada idanunta na kawo ruwa duk da tana typing abu a waya.

'A'a ki daina fadin haka ni na san bai tsaneki ba, raini ne dai baya so da kun saba yanzu zaki fa yana sake miki sosai ke ma.'
'Bari in ma kira a zo a miki kitso'.

'Kitso kuma Mum? Ai saloon zan je ayi min fixing.'

'Fadeelah kenan, karki maida al'adu na masu sa'bon Allah abin koyi, ko baki sani ba ne cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbatata agareshi yace:

"Allah ya la'anci mai qarin gashi da wadda take yi mata qarin gashin."

Kin ga kuwa kamata yayi mu guji duk abinda zai janyo mana fushi da la'antar Allah idan har muna so muga daidai.'

'Amma Mum shi ke trending fa yanzu, idan baki sawa yanzu sai ace you're not civilized.'

'Fadeelah, a wannan zamani na yanzu if you want to make it in Hereafter, you'll have to forget about western civilization and what's trending and focus on the goodness that Allah has given us.

Allah yana son mu kasance masu nuna godiya a garesa akan abubuwan da ya bamu ko da ba hakan muka so ba domin Yace:

"Idan kuka nuna godiya, zan yi muku qari.

Kin ga kuwa jikinmu, complexion dinmu, gashinmu, dukiyarmu da komai ma namu abubuwan da zamu nuna appreciation ne zuwa ga Mahaliccinmu sai kiga ninki har abinda baki taba tsammani ba ma. Da zaki ji shawarata da kin shiga Islamiyyar dake nan kusa damu kin ga before kuyi resuming school ma kin yi nisa in yaso sai ki cigaba da attending wasu every vacation. With time kina kammala degree dinki sai ki koma zuwa islammiyar full time zaki ga fa'idar yin haka in shaa Allah.'

'Thanks Mum, Allah ya qara girma. Zan yi joining this weekend in shaa Allah.'

                    **✿❀○❀✿**

'𝙎𝙖𝙡𝙖𝙢𝙪 𝙖𝙡𝙖𝙮𝙠𝙪𝙢'

'𝙒𝙖 𝙖𝙡𝙖𝙮𝙠𝙪𝙢𝙪𝙨 𝙨𝙖𝙡𝙖𝙖𝙢'
Sannu da zuwa Yaya, ya hanya?

'Lafiya lau Fa'az, ya mutan gida?'

'Kowa lafiya Yaya'

'Alhaji na nan kuwa?'

'Eh Yaya bari in gaya mishi ka zo'

'Haba Alhaji Bala naga dai kai ba baqo ba ne amma har yau baka taba shigowa har sai ka aiko' inji Alhaji Mahmoud da ya shigo guestroom din bayan Fa'az ya yo kiranshi.

'Babu komai ai hakan ne ya dace, ya iyali?'

'Duk suna lafiya yanzu ma zaka ga Hajiyar don na aika a gaya mata zuwanka, ya ka baro su Gwaggon?.'

Ae yana rufe baki sai ga Hajiya Aisha ta shigo cikin shiga ta alfarma ta gaidashi cikin fara'a tana tambayarshi gida.

'Kowa lafiya lau Alhamdulillah, ya yarana?'

'Suna nan lafiya sai Khaleed 'yan boarding.'

'Ahh kuce autan Hajiya makarantar kwana ya koma. Ma shaa Allah Ubangiji ya basu sa'a.'

Aameen ya Allah.

Masallacin dake maqale da gidan suka wuce don yin sallar la'asar bayan sun kammala cin abinci, bayan sun ida suka fito sai suka koma bangaren Alhaji don tattaunawar yaushe gamo su kuma Fa'az da Ahmad da wani abokinsu Ammar suka wuce bangarensu.

'Alhaji dama nazo ne in tambayeka ne har yanzu ba'a dace ba maganar yaron nan?'

'Har yanzu fa Alhaji Bala, in da rabo sai kaga an ganosu. Ni kam ko ba'a ganesu ba ma na daukeshi da don ya kai duk yadda ake son da nagari. Kuma dama ina da niyyar tuntubarka nan gaba ma na bashi 'yata Asma'u na gaya mata ma ita da mahaifiyarta kuma sun yarda sun amince dama jira nake idan na shigo Gaya in tuntubeka tunda Fa'az din yace sai yadda kace.
Ai yaro ko baka san asalinsa ba idan har bai kasance gurbatacce ba bai kamata a qyamaceshi ba. Koda ma bai da hali na qwarai ma kamata yayi ayi jihadin cetoshi daga halaka.'

'Haka ne Alhaji kuma naji dadin wannan hadin kuma na amince, Allah ya qara hada kanmu. Nasan Habu ma zai yi farinciki sosai.
Allah ya kaimu lokaci'

'Aameen ya rabbi, nagode da amincewarka Alhaji Bala. Allah ya qara qarfin zumunci. '
Nan dai suka ci gaba da tattaunawa abinsu.

With love,
Sara. ❤

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 28, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

FA'AZ DA FA'IZWhere stories live. Discover now