2

25 4 0
                                    


'Inna wai ina shegen yaron nan yaje bai gama wanke kaya ba gashi na debo nawa zan bashi'

'Kul kar in qara ji kin zageshi a gidan nan don yayanki ne, wanki kuma ba zai sake yi miki shi ba idan har gidan nan nata ne.'

'Haba maigida' Innan ta wani harzuqo ina dalili ka kama yarinya 'yar sunnah kana zagi akan shegen da liqa mana.
Yaro dai ba ni na haifeshi ba, kuma har tsohonka ya bar duniya ba gaya mana yayi ta inda ya sameshi ba.'

Wannan maganar ta matuqar bata wa Malam Bala rai, da ba don baya so ya kasance cikin maza masu dukan mata ba da sai jikinta yayi tsami yau.

'Innar Zulai, yanzu rashin mutuncinki har ya kai kan iyayena yau. Lallai dole in dauki mataki kafin kisa in tafka babbar kuskure wata rana.'

Tsorata Innar tayi da jin kalamanshi da kuma ganin yadda idanunshi suka rine suka yi ja, ta san mijin nata akwai haquri amma akwaishi da cika alqawari idan yayi niyyar daukar mataki, Zulai din ma fecewa tayi daki kafin ta kwashi rabon duka.
Gashi yanzu saura igiyar auransa biyu suka rage a kanta kuma duk a dalilin wannan shegen yaron, ta fada a ranta.

Tashi yayi ya fita yana huci, bai tsaya ko ina ba sai shagon qaninsa Malam Habu suka yi shawarar da zasu yi ya koma gida.

        ➳༻❀✿❀༺➳

       WAYE MALAM BALA

Baba Iliya ya kasance jajirtaccen dattijo mai kamala da nagarta, matansa biyu Inna mai 'ya'ya bakwai duka mata, sai Gogo Asabe mai 'ya'ya biyar maza biyu mata uku.
Ya shimfida gidanshi akan amana da son juna da adalci dai dai gwargwado duk da ba haka Goggo Asabe ta so ba duba da cewa it's ce mai yara maza sai ta so a fifitata akan kowa sai dai maigidan ba lusarin namiji ba ne duk da haqurinsa.

Bala shi ne danta na fari kuma shi ne ya fara wuce gaba da makarantar firamare ta L. E. A duk gidan saboda matan na gama L. E. A  din ake musu aure, daga shi sai Habu sannan Ladidi, Bintu sai Laure mai sunan Inna.

Inna kuma tana da Atine, Batula, Hansatu, Mariya, Indo, Asabe takwarar Goggo Asabe sai Zulai wadda ake kira Auta, kuma wadda Malam Bala yayi wa takwara.
Sun taso cikin so da qaunar juna duk da kishin dake tsakanin iyayensu mata. Duka yaran maza da mata kowa yayi aure har da 'ya'ya. Ana cikin hidimar bikin Auta ne Baba Iliya ya fita siyayya shi da Habu ya dawo daga siyayya da jaririn da ya tsinta a hanya.

Kowa yayi mamaki matuqa amma suka yi shiru sai Goggo da ta kasa shiru.

'Malam ina kuma ka tsinto shege haka?'

'Shege kuma Asabe?? Kar in ji kar in gani, duk wanda ya sheganta yaron nan zai gamu da fushi babba ko qarami.'
Yanzu haka daga wurin Maigari nake kuma yace in riqeshi idan an zo nema ma basu.

Kwanaki sun zama satittika har aka fara watanni babu wanda yazo cigiya tun Baba Iliya na zuwa wurin Maigari ko anyi sa'ar gano danginshi amma zancen daya ne ba'a dace ba.
Da Maigari yaga yadda Baba Iliya ya damu kuma sanin halinsa ta nagarta da amana sai ya bashi damar riqeshi idan yana da niyya nan yace ya yarda aka bashi.
Dama kuma an tsinceshi da takarda mai dauke da rubutun suna FA'AZ don Habu ne ma ya karanta ma Baban tun a inda suka tsinceshi kuma da ya dawo gida ya sake tambayar Bala kuma ya jaddada mishi hakan, kuma tun a ranar Baba Iliya ya yanka rago ya rada masa sunan.

A hannun Inna Baba Iliya ya damqa amanar FA'AZ sanin halayen matansa don Inna ta kasance mai matuqar haquri da biyayya ba kamar Goggo ba. Hakan da Baba yayi bai hana Goggo tsangwama wa FA'AZ din ba duk da yaranta suna sonsa don ya kasance fari sol kyakkyawa dashi mai farin jini. Duk da taso ta cusa musu tsanarsa amma da yake babu wanda ya gadota sai ya kasance ita kadai ce bata sonshi, a haka dai ta cusa ma Kulu tsanarsa bayan Bala ya aurota.

FA'AZ na shekara goma Allah yayi ma Baba Iliya rasuwa, bayan ya damqa wa Bala amanar Bawan Allah kamar yadda yake kiranshi.
Bayan shekara uku da rasuwarsa Inna ma tace ga garinku.
Tsangwama kala kala FA'AZ ya fara fuskanta daga wurin Goggo da Kulu da kuma 'ya'yansa. Duk yadda ya so ya hana kasawa yayi babu yadda ya iya da mahaifiyarshi wadda ta kasance jagorarsu.
Bayan Kulu ta tabo mahaifinsa ne yayi shawara da Habu suka kai wurin qanin Inna da ke zaune a birnin Kaduna don rasuwarta bai rage komai ba daga zumuncinsu da danginta.
Madallah da samun tarbiyya daga nagartaccen uba.

Wannan kenan!

*Da wannan nake ba 'yan mata shawara a dage da addu'a ta samun miji mai addini da nagarta domin ko bayan ransa tarbiyyar da ya ma zuri'arsa kadai ta isa a dinga tunawa da shi, Allah yasa mu dace.*

                 ➳༻❀✿❀༺➳

Fa'az! Fa'az!! Fa'az!!!

Firgita yayi ya dawo da tunaninsa

'Haba FA'AZ! Tun dazu nake ta qwala maka kira ka shareni. Tunani dai tunani dai. Allah dai ya cika maka burinka.

'Amin Ahmad, ina zuwa ne haka?'

Gidan Big Daddy zani ko zaka biyoni kaga Ya FA'IZ mai kama da kai.

A'a wallahi, sai ka dawo dai.

'Kaji da shi, wata rana dai dole ku hadu.'

Naji dai.

FA'AZ DA FA'IZWhere stories live. Discover now