"Haba Zainab, yaya kikeyin abu kaman ba jami'a kike ba? Karki badani mana. Anya kuwa kina sona?" cewar Bassam da ke ƙoƙarin riƙe hannunta.
Tura hannun cikin gyale tayi, ta ɗaga kai ta kalleshi. Acikin ranta tana mamakin wannan hali. Ita dai bata daɗe da haduwa dashi ba, sabida haka batada masaniya akan halayyarshi, amma dai a ido bata taɓa tsammanin jin wadannan kalamai daga bakinshi ba. Yau sati uku kenan da haɗuwarsu, kuma yau ne zuwanshi na biyu hira awajenta.
Murmushin yaƙe tayi sannan tace "Ba batun ko ina sonka ko bana sonka bane, kaima kasan ba haka bane, amma dai..." Sai kuma tayi shiru.
"Yes? Amma dai meye? Ƙarasa maganarki"
"Amma dai gaskiya I don't feel comfortable with you touching me, ai ba sai ta nan bane zai tabbatar maka cewa ina sonka. Kalamai da nake gayamaka basu isa ba? Ko kuwa nuna damuwata agareka shima ba sign bane?"
In a split second taga yanayin fuskarshi ya chanza, ahankali ya sake ƙoƙarin matsowa kusa da ita, cikin murya ƙasa-ƙasa yace "Words alone aren't enough, my darling. Bakiji ana cewa 'action speaks louder' ba? Kaman baki yarda dani bane, in ba haka ba, ai ba komai don na taba jikinki, wannan is completely normal."****
"Najib kenan," ta faɗa cikeda fara'a, "Kanada abun dariya wallahi."
"Ai ni duk duniya banda abinda yake sani tsananin farinciki kaman inji kina walwala."
"Kasan ɗazun da na kiraka, har ga Allah hawaye ne yake zubowa a idanuna, amma cikin ikon Allah gashi in one minute ka sa na manta duk wani baƙin cikin dake yawo cikin raina"
"Aaliyah..." Ya kira sunanta cikeda shauƙin soyayya, "Inason kasancewa tare dake, raina yana mugun sosuwa idan na tuna yanda wanchan mutumin baisan darajan abinda yake dashi ba"
Ajiyar zuciya ta sauƙe, ta buɗe fridge dake dining room ɗin ta fitar da goran ruwa. Komawa tayi ta zauna ta kurɓi ruwan, cikeda damuwa tace "Toh ya zanyi? Mijina ne amma kullum in na zauna sai yasa inyita tunaninka. Jiya haka muna zaune yanata danna laptop alokacin da ya kamata yazauna yayi hira dani. I couldn't help but think to myself, idan kaine nasan bazaka taɓa shareni haka ba, bazaka ganni nasha wanka sannan ko sannu bazaka ce ba. Bazan maka magana ka dinga amsani kaman bakason magana dani ba. In ba don kai ba, inaga da tuni baƙin cikin Ridwan ya kasheni."****
©Haneefah U.
YOU ARE READING
RUDIN ZAMANI
General FictionHey guys! It has been ages. Gani na dawo muku da labari mai masifan daɗi. Two different stories. Two dilemmas. Aɓangare guda akwai Zainab, matashiya wacce take ƙoƙarin fahimtar rayuwa. Tambayar itane, wace ɗabi'a zata ɗauka? Awani ɓangare kuma ga A...