Kasa danne eagerness nashi yayi, cikin fara’a ya tambayeta “Does that mean I will be your first boyfriend?”
“Yes, you could be,” Ta bashi answer tana murmushi.
Nan ya bata takaitaccen labarinshi “Sunana Bassam Nuruddeen. Babana yanada mata biyu, da yara goma sha-biyar. Ni ne na uku, inada yayyu mata guda biyu. I’m 32 years old. Na karanta computer science a Bayero University, Kano. I’ve been working for almost six years now.”
“Agida ma kaine yaya babba, kaga had it been na kiraka da sunanka ai abun baiyi ba,” ta fada cikin zolaya.
Murmushi yayi yace “Ke daban, su daban. Ni matsayin saurayinki nakeson zama, ba matsayin yayanki ba.”
Dariya tayi bata ce dashi komai ba, shi ne ya sake magana.
“Anything else you want to know?”
Girgiza kai tayi kaman yana ganinta, “A’a babu.”
“Okay, your turn.”
“My turn kaman yaya?” Ta tambayeshi cikin rashin fahimta.
“Ina nufin kema ki bani takaitaccen tarihinki. Sai mufi fahimtar juna ai ko?”
“Eh hakane.”
Jin tayi shiru bata cigaba da magana ba yasa yace “Ina jinki.”
Jan numfashi tayi kafin tafara, Kaman yanda yayi.
“Kaman yanda kasani, sunana Zainab Shu’aibu. Ni ce babba, inada kanne biyu duk mata. I’m 19 years old. Nayi computer training na one year bayan gama secondary school, sai this year nasamu admission don karanta Biotechnology.”
Atake yaji ta kara shiga ranshi.
“That is impressive my dear,” ya fada full of admiration.
Cikeda kunya tace “Nagode.”
“Hostel ko agida kike?” Ya jefa mata tambayar.
“Ina gida. Abba yace hankalinshi yafi kwanciya in na zauna agida.”
“Hakan yanada kyau. Wani anguwa kuke?”
“Muna Demsawo.”
Yayi shiru yana tunani kafin yace “Yaushe zan samu ganinki?”
Zare idanu tayi, cikin sauri tace mishi “Abba baya bari inyi hira. Saidai ka bari in na gayama Ummi sai inji meye zatace tukunna.”
Jin ta ambaci sunan ‘ummi’ yasa ya razana, shi fa ba wai yana nufin zaizo gida hira har iyayenta su sanshi bane. No. Yayi tsammanin zatace mishi zasu iya haduwa awani waje daban. Ko kuma su hadu idan ta shigo school.
Cikin shakku yace “Kina nufin zaki gayawa mamanki?”
“Eh, ita ne muke kira ummi”
Kokarin gyara zancen yayi. “Haba yanmata, akan haduwan ne sai ummi ta sani? I don’t think that is necessary for now. Karki manta fah yanzu kema kin zama babba, na tabbata ummi zataji dadi idan ta san kina magana da wani amatsayin saurayinki.”
Tafara tuna irin yanda kullum maganan ummi bai wuci ace ta ga aurenta ba. Ta dauki burin duniya ta daura akan jiran wannan rana. Duk ranar da taga ko food flasks ne sunyi mata kyau, haka take siya ta ajiye tace zasuyi kyau agidan Zainab nata. Jin bayanin da Bassam ya mata, sai taga akwai alamun hikima acikin maganar.
“Sai yaushe kenan kake ganin ya kamata ta san da kai?” Ta tambayeshi cikin son jin karin bayani.
Cikeda kwarin guiwa yace “Yanada kyau mu zauna mu fahimci juna ni da ke tukunna. Just the two of us. No third parties. Ta yanda in kin kawo musu zance na, da batun aure ne zamu nufesu, ba batun soyayya da zuwa hira ba. Zasu amsa da hannu bibbiyu cikin jindadi. Hankalinsu zai zama ya kwanta don ganin yarsu ta samu wanda yake sonta fiye da komai aduk fadin duniya. Ko ya kika gani?”
Ta yarda da maganarshi dari bisa dari. Deep inside, she knows bai kamata ace ta boye wa mahaifiyarta wannan batu ba. Tasan ko ba komai, zatayi murna kuma zata bata shawarwarin da ya kamata. Saidai kuma maganar Bassam yayi tasiri aranta sosai, tasan farincikin da mahaifiyarta zata shiga zaifi ninkuwa idan taji zancen aure anan kusa.
“Na yarda da maganar ka Yaya Bassam. Duk yanda kace, hakan za ayi.”
“Naji dadi da kika fahimceni,” ya fada cikin tsananin jindadi.
****
Misalin karfe biyar na yamma Aaliyah ta shirya tsaf ta fito ta rufe kofar parlor. Tsakar gida ne babba zagaye da flowers, ginin gidan is painted in grey and cream color.
Gidan ya kasu kashi-kashi. By the right shine main house, yana kunshe da parlor biyu kowanne da guest toilet aciki. Bedrooms guda shida, hade da bathrooms nasu. Dining area. Kitchen. Da kuma store.
In ka zagaya ta backyard zakaga wani daki shima hade da toilet, anan mai aikinta ‘Larai’ take zama.
Ta gefen hagu shine guest room. Two bedroom apartment ne da komai aciki.
Sai parking garage, inda akwai parking space na motoci hudu. Daga karshe kuma kusa da gate shi ne sashen mai gadi.
Parking garage ta nufa, ta shiga wata sabuwar 2018 Corolla LE. Danna horn ta fara yi tun kafin tayi reverse. Da gudu mai gadi yafito ya bude mata gate. Daga nesa ta hangeshi yana daga mata hannu bibbiyu alaman girmamawa. Tsayawa tayi sannan ta saudar da glass na window abakin gate din.
“Barka da rana Hajiya,” ya daga mata gaisuwa yana washe hakora.
Murmushi ta mayar mishi, cikin fara’a tace “Barkanmu dai Jafar, yaya aiki?”
“Lafiya kalau Hajiya. Allah ya kiyaye hanya. Adawo lafiya.”
“Ameen,” ta bashi amsa tana laluben cikin handbag nata dake ajiye akan passenger seat. Zaro dubu uku tayi ta mika mishi.
Ya karbi kudin yana sunkuyawa yana godiya kaman zai kifu da kasa.
Cikin sauri tace “Banason sunkuyawar da kakemin. Don Allah ka daina.”
“Yi hakuri Hajiya. Allah ya saka da alkhairi. Allah ya biyaki da gidan aljanna. Allah yasa daga ke babu kari. Babu ke babu zama da kishiya da yardan Allah. Allah ya kare…” Ya dinga kwararo addu’o’i.
Cikin dariya tace “Jafar kenan. Ameen ya Allah.”
Ta bata lokaci a shagon atamfofi, sannan taje ta zabi bag and shoes, sannan jewelries. Ahanyar komawa gida sai ta biya shopping mall don siyan abubuwan motsa baki.
Ta gama siyayyan ta fito sai taji ana cewa “Baiwar Allah, ji mana.”
Batayi tunanin da ita akeyi ba, ta cigaba da tafiya sai da wani agabanta yace mata da ita ake magana. Tsayawa tayi ba tare da ta juya ba, wani saurayi ne yazo daidai inda take tare da yi mata sallama. Amsawa tayi sai yake ce mata sunanshi Kamal.
“Toh sannu malam Kamal, lafiya kayi ta kwala min kira?” Ta tambayeshi.
Hular kanshi ya dan gyara, ya kaikaya keyarshi, sannan yace “Don Allah kiyi hakuri. In ban takuraki ba, phone number naki nakeso.”
Kare mishi kallo tayi daga sama har kasa. Saurayi ne bazai wuci 28-30 years ba. Gashi yayi wanka cikin white kaftan, sai kamshin turare mai sanyi yake yi. Atake taji yayi matukar burgeta.
****
©Haneefah U.
YOU ARE READING
RUDIN ZAMANI
General FictionHey guys! It has been ages. Gani na dawo muku da labari mai masifan daɗi. Two different stories. Two dilemmas. Aɓangare guda akwai Zainab, matashiya wacce take ƙoƙarin fahimtar rayuwa. Tambayar itane, wace ɗabi'a zata ɗauka? Awani ɓangare kuma ga A...