Tun daga ranan da Zainab ta fara zuwa lectures Bassam ya matsa mata akan yanaso su hadu. Unfortunately, first week duk a birkice tayi shi. Monday, Tuesday, and Thursday tana fara lectures tun 7am, ga afternoon classes. Wednesday, Friday, Saturday ne take dan samun saukin sammakon sassafe, shine take fara classes daga 9am. Tare da kawarta Jamila suke komai, ga sabbin kawaye da sukayi masu suna Zara da Fa’iza.
Ranan Sunday agidansu Jamila ta wuni, tana tayata packing don ita a hostel zata zauna. Da yamma ita da mama (mahaifiyar Jamila) suka rakata hostel suka tayata unpacking. Daki ne madaidaci na mutane shida, kowacce da wardrobe nata da kuma locker. Jamila sai rawar kai takeyi don dadi. Zainab tayi tagumi tana tuna ina ma ace tare zasu zauna, saidai tasan hakan ba mai yiwuwa bane. Har wajen maghrib mama ta sauke Zainab agida sannan ta wuce.
Shiganta gida Bassam ya kirata awaya. Ajiye wayar tayi saida tayi sallah tukunna ta kirashi. Baiyi answering ba, yana tsinkewa ya biyo kiran da nashi.
“Wani laifi nayi ma babyna ta shareni haka?” Ya tambayeta cikin magiya.
Ta rasa wani irin effect yake dashi akanta. Tana jin muryarshi sai ta manta da komai. Duk kokarin ta na ganin ta dan saka space tsakaninsu baya taba dorewa. Bassam mutum ne da ya iya nuna tsantsan kulawa, gashi da saukin kai. Tun da suka hadu sai sunyi magana on a daily basis, wasu lokutan suyi magana sau uku ko ma fiye da haka. With every conversation they have, yana kara zurfafa acikin ranta. Batasan ta inda zata fara tsamo shi ta fito dashi ba. Yayi wani gini na musamman ya zauna daram. Kuma yana saka ta fahimtar abubuwa dewa da bata tata tunanin dagaske dan adam yana jinsu gameda wani ba. Sannu ahankali suke fahimtar halin juna, tana jin lallai shi dinnan shine soulmate nata.
“Tuba nake. Ba shareka nayi ba,” ta fada cikin lallashi. “Ka kirani ina shirin yin sallah shiyasa ban daga call din ba, na idar kenan yanzu na kiraka.”
“Allah yasa dai kin sakamu cikin addu’ar,” ya tambayeta.
“Kai ne ma agaba. Kawai kace ‘Ameen.’”
Yana murmushi yace “Ameen.”
“Anya kuwa ba gudu na kikeyi bakiso ki ganni ba?” Kaman daga sama ya jefa mata tambayar.
“Mesa kake tunanin haka?” Ta tambayeshi.
“Saboda naga everyday duk muna shiga school, amma kin kasa bani ko da five minutes ne inzo in ganki. Weekend ma dama yau ne kikace kike free, nayi tunanin zamu iya haduwa, sai gashi kin raka kawarki har kin koma gida ko ki nemeni. Ko dawor dake nazo nayi ai zanji dadi tunda na ganki.”
Kokarin mishi bayani tayi.
“First week nan ina faman gane kan school din ne, ga classes. Lunch time kawai nake dashi, shima kaga da kawayena muke zuwa restaurant muci.”
“Hmm…” yace. Bai kara cewa komai ba.
Jin haka yasa ta dora da cewa “Amma ni ba gudun ka nakeyi ba.”
“Toh mene? Ko ina takura ki ne?” Ya sake tambayanta cikin sanyin murya.
“Ai nima inason mu hadu,” ta fada da sauri, harda rufe fuska kaman yana ganinta.
Ajiyar zuciya yayi, “Idan dagaske ne, prove it to me.”
“How?” Ta tambaya cikin rashin fahimta.
“Ki bani ranan da zanzo in ganki. Pick a day.”
Tsakani da Allah tana son haduwa dashi, tana son taga fuskarshi idan yana mata murmushin da ke sanyaya mata zuciya. Tana son ta ganshi, ga ta ga shi, ba wai imaginations da take using ba.
Batasan lokacin da ta furta “Tomorrow,” ba.
Bakinta bai mata adalci ba, meyasa zai subuce ya fito ba tare da ta sani ba? Yatsun hannunta ta daura akan lips nata, ta kama bakin ta rufe.
“Tomorrow?” Ya maimaita afili.
Sosai yaji dadin wannan suggestion da ta bayar.
Cike da fara’a yace “Allah ya kaimu.”
Suka cigaba da hiransu cikin nishadi har sai da Ummi ta kwala mata kira akan tazo su ci abinci.
Da safe tana shiga school sukayi magana, yace mata zaizo ya dauketa ya kaita lunch by 1pm. Nan fah taki yarda, tace mishi bazata ji dadi ta bar kawayenta ta bishi ba, saidai in zaizo ya samesu inda ta saba zuwa dasu. Yace mata shi ita yakeson gani, ba friends nata ba. Har yayi fushi yace shikenan, ya hakura da zuwan, taje da friends nata.
Abun ya dameta because she was looking forward to seeing him. Tana haduwa da kawayen nata su uku ta kwashe labarin yanda sukayi daga farko har karshe. Jamila, Fa’iza da Zara duk suka hau kanta da daura mata laifi.
Fa’iza tace “Yau na ga shirme. Wannan ba ma magana bane. Dole ranshi ya baci mana.”
Zara tace “You have to call him right now. Ki kirashi kice mishi you were wrong kuma kin yarda zaki bishi ku fita tare.”
Jamila tace “Leave her. Wai dama don mu ne zakiyi canceling date naki? Mu fa friends naki ne, we are always together. Mesa zamuji haushi don kin fita da boyfriend naki?”
Kallonsu ta dinga yi daya bayan daya tana sauraron bayanin da sukeyi. Ita tayi hakane wai don kar suce ta fifita saurayinta akan su. Sai gashi duk laifinta suke gani. Tashi tayi ta koma gefe, ta kirashi.
“Yaya Bassam,” ta fara magana cikin shagwaba. “Kayi haƙuri, ka ji?”
Iska ya furzar, sannan yace “Ya wuce.”
Kaman zatayi kuka tace “Will you come? Please…?”
Acikin ranshi yana tunani idan yayi wasa wannan yarinya zata mishi destroying duk wasu plans nashi.
Afili sai yace “Yes, zanzo In Sha Allah. Text me idan kin fito daga class.”
Tana mishi text bai wuce 10 minutes ba ya iso bakin department ya kirata. Ita kadai ta fito, su Jamila sun riga sunyi tafiyarsu da wasu classmates. Bude mata kofar yayi ta ciki yayi mata Bismillah. Ganin hanyar main gate ya nufa yasa ta dube shi tana tambayarshi ina zasuje. Dariya yayi ya tambayeta ko tana tsoron kar ya gudu da ita ne.
Kafewa tayi tana kallonshi, kaman an hada mata wani irin electric shock taji. Dariyar shi ya tafi da hankalinta. Ya tarwatsa duk nerves dake jikinta. Arikice ta cire idanunta daga kanshi ta mayar kan window.
“I am in trouble,” ta fada in a whisper.
Jin tayi magana amma bai fahimci meh tace ba, sai ya tambayeta. Girgiza mishi kai tayi bata sake cewa komai ba. She doesn’t even trust her voice around him.
****
©Haneefah U.
YOU ARE READING
RUDIN ZAMANI
General FictionHey guys! It has been ages. Gani na dawo muku da labari mai masifan daɗi. Two different stories. Two dilemmas. Aɓangare guda akwai Zainab, matashiya wacce take ƙoƙarin fahimtar rayuwa. Tambayar itane, wace ɗabi'a zata ɗauka? Awani ɓangare kuma ga A...