Aaliyah tana shiga daki taji wani irin kuka yana neman kufce mata. Jingina da kofar tayi ta sulale zuwa kasa. Hannu bibbiyu tasa ta rufe bakinta tana kuka mai ban tausayi.
Bayan tayi kukan har ta gaji sai ta koma parlor tanata duba channels ko akwai abinda zai dauke hankalinta daga halin da take ciki. Tsaki tayi ta kashe TV din gabadaya don haushi. Kaman da gangan channels da ta saka duk films na soyayya sukeyi. It makes her pain unbearable ganin yanda mazan suke tarairayan matansu. Bata iya jure ganin abinda ita ta kasa samu.
Phone nata ta duba taga har ya turo mata kudi, hade da “Forgive me,” written as transfer description.
Soyayyan shekara daya sukayi da mijinta Ridwan Saddam. Alokacin da suke soyayya ba abinda yafi burgeta gameda shi kaman grand gestures da yake mata. Tun farkon haduwarsu ya gayamata shi ba mai zama bane, ayyuka suna mishi yawa, saidai ba a yin sati biyu ba tare da ya turo mata shopping bags cike da kayaki da abubuwan bukata ba. Ta kuma ga tabbacin rashin zaman nashi several times idan yace mata zaizo hira, sannan daga baya ya kira yana bata hakuri bazai samu zuwa ba. She saw the signs amma atunaninta duk wannan don basuyi aure bane tukunna.
Ta tuna wani maganan da suka yi one month kafin bikinsu.
“Kasan meh yake damuna?” Tace dashi.
“Kudin gyaran jikin ne sukayi kadan? In wannan ne ba abun damuwa bane baby…”
“No, ba batun kuɗin bane,” ta katse shi. “Batun rashin zamanka ne. Zan iya kirga sau nawa kazo gida muka zauna mukayi hira na one hour ba tare da ka bani uzuri akan zaka tafi ba.”
“Wannan kamawa yakeyi, I thought you understood that, or was I wrong?” ya tambayeta cikin mamaki.
“I understand. Abinda yake damuna shine anya zaka iya bani lokacinka idan munyi aure?”
“Meyasa zakiyi irin wannan tunanin? Eh baby?”
Cikin shagwaba tace mishi “Inason in tabbatar ne kawai, ni banaso in dinga yin nesa da kai”
Murmushi yayi yana cewa “Indai wannan ne ki kwantar da hankalinki. Muna yin aure nazama naki sai yanda kikayi dani. In kinaso ma ai sai mu wuni agida tare, ba inda zanje.”
Dariya tayi, cikin jindadi tace “Nagode da wannan matsayi da ka bani. Da alama watarana dole in hanaka fita don ka dinga samun hutu.”
Ashe dai duk dadin baki ne. Gashi aurensu ko shekara daya baiyi ba, amma ta rasa farinciki da walwala awurin mutum daya da tayi tsammanin zai zama sanadiyyar share mata hawaye.
****
Cike da jindadi Zainab ta isa gida. Gida ne mai flat biyu aciki. Daya na babanta Alh Shuaibu, dayan kuma na mamanta da yaranta guda uku. Zainab ne babba, sai kannenta twins suna primary school, Amra da Faiza.
Ta tarar da maman tana girki a kitchen. Ba tare da bata lokaci ba tafara gaya mata labari akan sun karasa registration nasu. Hajiya Hindatu ta sa ma karatun albarka, ta hada da cewa,
“Allah ya saka ma wannan bawan Allah da alkhairi, meh ma kikace sunanshi?”
“Kai Ummi, Bassam fa nace miki,” ta ba ta answer tana dariya.
Jijjiga kai tayi tace “Sunayen zamanin nan da wahala suke.”
Kare ma Zainab kallo tayi, tabbas yanzu ta kai matsayin da dole ta gargadeta akan sabuwar rayuwa da zata shiga.
Cikin nitsuwa tace “Yanzu dai kin wuce stage da za ace za azauna ayi miki fada abaki tsoro. Babanku yayi matukar kokari akan baku kyakkyawan tarbiyya da karatu mai inganci. Nima nayi iya bakin kokarina wajen jan ku ajiki domin ku iya zuwa min da matsalolinku. I’m sure you can differentiate between right and wrong. Kin samu ilimin addinin da baza kice kinyi abu cikin rashin-sani ba. Ina gudun kar ki dauki halaye marasa kyau irin na wasu matan da suke university.”
“Hakane Ummi.” Zainab ta fada cikin ladabi. “In Sha Allahu zan kiyaye.”
“Ba wai ina nufin duk aka taru aka zama daya ba,” Ummi ta cigaba. “Idan nace hakan toh na jahilci abun. In kin kama kanki sai ki gama lafiya kalau baki zubar da mutuncinki ba. Mu dai ba binki makarantan zamu dinga yi muna bibiyan duk abinda kikeyi ba. Ba don mu zaki kiyaye kanki ba, don tsoron Allah zakiyi. Ki saka Allah aranki. Mukuma zamu biki da addu’ar Allah ya kareki daga kowanni sharri.”
“Nagode. Allah yabani ikon zama muku abun alfahari,” cewar Zainab.
Ummi ta amsa da “Ameen.”
Zainab ne da kannenta tana tayasu assignments bayan sun gama cin abincin dare. Call din Bassam ne ya shigo wayarta, batasan lokacin da murmushi ya subuce mata ba. Tashi tayi ta barsu a parlor takoma dakinta.
“Salamu Alaikum,” taji wani husky voice ya furta. Zuciyarta ne ya amsa kafin taji ya zagaya jijiyoyin jikinta, sannan taji kwakwalwarta ma ya dauka.
“Wa’alaikum Salam,” ta amsa mishi cikin karamin muryar da batasan tanada shi ba. “Ina wuni?”
Ajiyar zuciya ya sauke yace “Masha Allah. Tun dazun nayi niyyan kiranki amma nace bari dai in hakura in barki ki huta tukunna. Ya mutanen gida?”
“Ayyah, nagode. Gida lafiyansu kalau. Ya aiki?”
“Alhamdulillah.”
Sai duk sukayi shiru. Gyaran murya yayi sannan ya sake cewa “Can we talk? Ko kina cikin mutane? Inaso muyi wani magana.”
“Yes, we can. Ina daki.”
“Okay,” sai kuma taji shiru.
Tafara tunanin ko dai network ne ya dauke, tafara cewa “Hel…”
“Sorry, ina tunanin ta inda zan fara ne,” ya katseta cikin kunya. “Tsakani da Allah tun da na ganki naji kin burgeni. Dafarko nayi niyyan in taimaka miki ne kawai, amma da na lura da nitsuwarki nasan gaskiya bazan iya hakura ba. Idan na barki kika tafi nayi ma kaina asara. Yanzu da naji muryarki kuma na kara tabbatar da cewa ina sonki.”
Jin wadannan kalamai daga bakinshi ya sakata cikin farinciki mara misaltuwa. Ta tashi tayi tsalle ne? Tayi ihun dadi ne? Ta fitar da zuciyarta ta mika mishi don yaga yanda yake bugawa domin shi ne? Toh yaya ma zatayi? What is she supposed to say to him?
Iyaka abinda ta iya cewa shine “Uhm, ehm.”
Pleadingly yace “Ina jinki. Nasan mata da jan aji, ki rufamin asiri karki ce sai kinyi tunani. Ki tausaya ma bawan Allah, please give me a chance.”
Dariya ma ya bata, wai wannan hadadden guy ne yake roko tayi soyayya dashi. Sai taji kaman mafarki ma takeyi. Pinching hannunta kadan tayi, nan ne ta tabbatar yes she is wide awake.
“Kayi hakuri, ba wai ina maka mummunan zato bane, amma ba abinda nasani akanka. Ai ya kamata in sanka tukunna ko?” Ta fada mishi cikin tantama.
“We can remedy that. Zaki iya min duk tambayar da kikeso, zanyi answering.”
“I have a confession to make, kar kamin dariya.”
Guntun dariya yayi yace “Bazan miki dariya ba.”
“Ka dai san yanzu ne na shiga University, secondary school kuma daga makaranta sai gida. Ba wai jan aji nake maka ba. Bantaba yin saurayi ba. I have no idea how these things work.”
Alokacin ne abubuwan suka mishi clicking. Yayi suspecting bata taba yin relationship da babba ba, amma dai baiyi tunanin awannan zamanin akwai wacce har ta gama secondary bata taba soyayya ko da na yarinta ba. Her behaviors suddenly make sense. Part of him started wondering anya kuwa zai iya? Another part of him is telling him she is perfect, yarinyan da batasan komai ba? He can mold her to be exactly what he wants.
****
©Haneefah U.
YOU ARE READING
RUDIN ZAMANI
General FictionHey guys! It has been ages. Gani na dawo muku da labari mai masifan daɗi. Two different stories. Two dilemmas. Aɓangare guda akwai Zainab, matashiya wacce take ƙoƙarin fahimtar rayuwa. Tambayar itane, wace ɗabi'a zata ɗauka? Awani ɓangare kuma ga A...