“Kayi meh da number na?” Ta tambayeshi.
“In bazaki damu ba, I’d like us to be friends,” cewar Kamal.
Girgiza mishi kai tayi ta cigaba da tafiya.
“Bazan iya baka ba, ni matar aure ce,” ta bashi amsa atakaice.
Hakan baisa ya daina bin ta ba. A tunaninshi ta gayamishi hakan ne don batason ta bashi ne kawai, ba wai tana da auren ba.
Tana fita shima ya shiga motarshi yabi bayanta har ta isa gida.
Two weeks later.
Farkawar Aaliyah ta duba time, taga 11:26pm. Tashi tayi ta kunna bedside lamp da ke dakin. The last thing she could remember was ta gama kwalliyarta around 9pm sai ta dan mike agado tana danna wayarta tana jiran Ridwan yadawo. Taga wutar dakin akashe, kuma tasan ta bar wutar akunne, domin bata san lokacin da baccin ya dauke ta ba. Ta tabbatar shi ne yadawo ya kashe wutan. Parlor tafara dubawa ko yana kallon news, taga komai akashe. Gashi abincin dake kan dining ma baici ba. Mamaki ne ya kamata, Ridwan yana dawowa gida ba abinda yake fara nema sai abinci. Zuciyarta ya fara tunanin ko dai yana daki baida lafiya ne. Da gudu-gudu ta isa dakinshi ta bude. Nan ma ta tarar empty, illa wardrobe da yake bude. Rufewa tayi tabar dakin takoma dakinta. Wayarta ta dauka ta fara kokarin kiranshi, anan ne ta lura da folded sheet of paper ajiye agefen pillow da tayi bacci akai. Tsayawa da kiran tayi, ta bude paper’n don ganin menene aciki.
“Baby,
Ɗazun na shigo kina bacci, you looked so beautiful and at peace that I couldn’t bring myself to wake you up. Na shiga dakina na dauki duk abubuwan da zan bukata. Kiyi hakuri, naso muyi sallama amma ganin babu amfanin tayar dake daga baccin tunda sauri nakeyi, na zauna na rubuta miki dan guntun note nan. I have a flight to catch at 10:30, idan mun sauka zan miki text in sanar dake. I will be back tomorrow evening In Sha Allah. I love you. Ki kulamin da kanki.”
Wasu irin hawaye masu zafi ne suka fara sauka daga idanunta. Ta karanta sakon, ta sake karantawa. Ta kasa yarda ko idanunta ne ke mata gizo, ko dai dagaske abinda ta karanta hakan ne. Tashi tayi cikin sauri ta sake komawa dakinshi. Wajen set na luggages nashi ta duba taga tabbas babu karamin acikinsu. Zuciyarta ya karye yana mata zafi. Ji tayi kaman zai faso yafito daga kirjinta. Saidai ko ma menene, addu’a takeyi Allah yasa ya isa lafiya.
Daurewa tayi ta mishi text message, “I got your note. Call me as soon as possible.”
Kafafunta taji sun yi mata nauyi. Da kyar ta karasa kan dining ta zauna tare da kifa kanta.
Meh Ridwan yake nufi da ita ne wai? Aganinshi note da ya bar mata zai sa ta farinciki? I love you na banza da wofi. Ta rasa wani irin tunani yake using. Akan meye zaiyi making decision ba tare da ya duba yanda abun zaiyi affecting nata ba? Yana tsammanin wani romantic gesture ne kin tashinta daga bacci? Zaiyi tafiya ai ko ma wani irin bacci takeyi yaci ace ya tashe ta sunyi sallama. Wani irin rayuwa ne wannan?
Ita kadai ta kunce wannan, ta saka wanchan. Karar wayarta ne yadawo da ita daga duniyar tunani da ta zurma ciki. Ganin sunanshi yana yawo akan screen sai taji wani sabuwar bakin ciki yazo mata har makogoro. Tana kallon wayar har ya gama ringing ya tsinke. Chan sai yasake kira.
Afusace ta dauka, “Wai dagaske tafiyan kayi!?!? Haba, haba! Ya za ayi kayi tafiya ka bar min note wai don kar ka tayar dani? Baccin mutuwa nakeyi? Ko zallar rashin mutunci ne? Kasheni kakeso kayi da ciwon zuciya?”
Shiru yayi bai katseta ba.
“Are you done?” Ya tambayeta cikin murya mai cike da gajiya.
Bata bashi amsa ba, sai huruwa da ranta yake kara yi.
Ahankali yace “Inaso ki nitsu ki saurari meh zan gayamiki. Yanzu meye abun fada anan? Zan iya tafiyana ba tare da na sanar dake ba, amma sabida kyautatawa nake gayamiki komai nawa. This is the first time I have traveled in this manner, amma sai ki kasa yi min uzuri? Na bar miki sako don in nuna miki damuwata agareki, gudun kar in barki da ciwon kan tayar dake daga bacci, shiyasa nayi hakuri na tafi ba tare da rakiya da addu’o’in nasara daga wajenki ba. Unfortunately, it backfired. Yanzu kinzo kina tuhuma na kaman da gangan nayi, ko ban damu dake ba.”
Cikin kuka tace “Nasan baka taba tafiya bansani ba. Abinda nake tsoro shine duk sauran issues da muke fama dasu ahakan suka fara. Daga sau daya ne, sai yazama shine normal. Na tabbata wannan din ma ba ayau zai kare ba. In ka gaji da zama dani ne ka sallameni in koma gidanmu mana, akan wannan zaman takaici da nakeyi agidanka.”
Dogon ajiyar zuciya ya sauke yace “Look, I’m exhausted. I am not in the mood for whatever big fight you are looking for. Shikenan bazan iya samun nutsuwa daga wajenki ba? I understand ranki ya baci, but I did what I thought was best. Hayaniyan nan tayar min da hankali yakeyi. Na tabbata bazamu iya magana mu fahimci juna yanzu ba. Zamu karasa maganar idan na dawo.”
Bata sauraren abinda yake faman fahimtar da ita, kaman yanda shima ya kasa fahimtar ta.
“Idan zuciyana ya buga na mutu kafin ka dawo, ai ka huta. Sai kayi rayuwanka ba tare da hayaniya na ba.”
Bata jira meh zai sake cewa ba ta yanke call din. Shi kuma bai sake kira ba.
Minti kadan ta jaa tsaki “Aikin banza. Sai kace shi ne autan maza. Har yanada bakin cewa ni ne mai hayaniya. Lallai tabbas Ridwan yazama wani mutum daban da na kasa ganewa.”
Daga karshe sai kiran tsohon saurayinta mai suna Najib tayi. Dama tun da tafara samun matsala a rayuwar aurenta sai ya zama babban aboki agareta, kuma mai share mata hawaye aduk lokacin da Ridwan ya saka su zubowa.
“Hello, lafiya kam?” Tambayar da ya fara mata kenan.
“Ba lafiya, Najib. Ina ji kaman numfashi na zai dauke. Jini na tafarfasa yakeyi. Na rasa yanda zanyi. Na rasa wanda zan kira sai kai. Na tayar dakai daga bacci ko?”
A razane yace “Subhanallah. Meke faruwa?”
Nan ta kwashe komai ta gayamishi. Ranshi in yayi dubu toh ya baci. Bata hakuri ya dinga yi yana lallashinta.
“This man doesn’t deserve you,” ya furta cikin bacin rai.
Wani tsakin ta sake jaa. “Ka ma san meh yafi bani takaici yanzu?
“A’a, meh daya?”
“Duk abubuwan da Ridwan yakeyi dinnan, wallahi har yanzu ina sonshi. Na rasa inda zansa raina. In ba don haka ba, da tuni na kashe auren nan na koma gidanmu.”
Ranshi ya sosu. Yaso yaji tace ta gaji da auren, ko kuma tace ta tsani mijin nata.
“Tunda hakane, ga hanya mai sauki. Wuka zamu samu mu nemi inda wannan soyayyan ya makale aciki, mu yanke muje mu jefar awata duniya daban,” ya fada cikin dauriya da tsokana, amma acikin ranshi yana tunanin how he wishes zai iya hakan.
“Najib kenan,” ta fada cikeda fara’a, “Kanada abun dariya wallahi.”
“Ai ni duk duniya banda abinda yake sani tsananin farinciki kaman inji kina walwala.”
“Kasan dazun da na kiraka, har ga Allah hawaye ne yake zubowa a idanuna, amma cikin ikon Allah gashi in one minute ka sa na manta duk wani bakin cikin dake yawo cikin raina”
“Aaliyah…” Ya kira sunanta cikeda shaukin soyayya, “Inason kasancewa tare dake, raina yana mugun sosuwa idan na tuna yanda wanchan mutumin baisan darajan abinda yake dashi ba”
Ajiyar zuciya ta sauke, ta bude fridge dake dining room din ta fitar da goran ruwa. Komawa tayi ta zauna ta kurbi ruwan, cikeda damuwa tace “Toh ya zanyi? Mijina ne amma kullum in na zauna sai yasa inyita tunaninka. Jiya haka muna zaune yanata danna laptop alokacin da ya kamata yazauna yayi hira dani. I couldn’t help but think to myself, idan kaine nasan bazaka taba shareni haka ba, bazaka ganni nasha wanka sannan ko sannu bazaka ce ba. Bazan maka magana ka dinga amsani kaman bakason magana dani ba. In ba don kai ba, inaga da tuni bakin cikin Ridwan ya kasheni.”
****
©Haneefah U.
YOU ARE READING
RUDIN ZAMANI
General FictionHey guys! It has been ages. Gani na dawo muku da labari mai masifan daɗi. Two different stories. Two dilemmas. Aɓangare guda akwai Zainab, matashiya wacce take ƙoƙarin fahimtar rayuwa. Tambayar itane, wace ɗabi'a zata ɗauka? Awani ɓangare kuma ga A...