BESTYN MIJINA

36 1 0
                                    

🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈
🎈🎈
🎈BESTYN MIJINA🎈
🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈
🎈🎈
🎈

LABARI DA RUBUTAWA:Faridat Hussain Mshelia (Ummu-jidda).

https://chat.whatsapp.com/I0pQ7UXmYyBCNmnCWrh8yK


(Dan Allah idan kin san ba kya sharhi kar ki shigo min group,sannan group ɗina na mata ne zalla banda maza).

Ɗanɗano.
Na sha jin mabanbantan labarai a gidajen talabijin da gidan rediyo da kafar sada zumunta na zamani dangane da hamshaƙan mata waɗanda suka tara dukiya masu yawan gaske duk a dalilin mazajen su na aure,wasu sun mallaki manyan gidaje,katafarun shaguna manyan motoci na alfarma da suturu masu tsada,manyan gwala-gwalai domin yin ƙawa da kwalliya tare da fitar kece raini a tsakanin tsaranni ban taɓa jin hakan a matsayin ƙalubale a gareni ba saboda na san Ni ba MATAR BAHAUSHE ba ce waɗanda Allah ya yi ma baiwa da ɗaukaka na samun cikakkiyar gata da yanci kamar yanda addinin mu na Musulunci ya tanadar,duk da Bahaushe ya ce"idan baki da gashin wance to bai kamata kiyi kitson wance ba,Kuma gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta"amman duk da kasancewa ta talaka mai ƙaramin wacce bai kamata in haɗa kaina da ƙasaitattun matan dana ambata a sama ba,a tsararrakina wato talakawa Irin irin na san duk da haka MATAR BAHAUSHE ta yi min nisan da ban isa in kamota ba saboda ita ɗin yar gata ce wacce tana zaune a gida cikin inuwa da raɓar fanka,mijinta ke fita komin ruwa komin iska,komin zafin rana ya fita yaje ya nemo mata duk abinda zata ci tare da biya mata dukkanin wani buƙatunta na yau da kullum,na ga hakan ganin idona,tunda ina rayuwa a wata unguwa ta marasa ƙarfi, acikin wani tsakurkurin gida na marasa ƙarfi wanda baida maraba da bacha,a kullum na zauna ina tunani tare da haɗa rayuwata dana MATAR MALAM BAHAUSHE sai in ga ta min nisa,nisan da ba zan taɓa kamota ba a rayuwata,saboda Ni fita nake yi in yi aikin ƙarfi kafin in samu abinda zanci Ni da iyalina ciki kuwa hadda gansamemen ƙaton mijina,cima zaune wanda zuciyarsa ta mutu ya ke zaune a gida yana jiran in je in nemo in zo in girka in bashi yaci,duk ranar da aka samu akasi ko saɓanin hakan ya yi min dukan Kawo wuƙa kuma ya hana kowa ya kwaceni tare da yin munanan kalamai a kaina wanda zafin su ke toshe ƙofofin jina guda biyu(kunne)tare da sanya bugun zuciyata ƙaruwa a kowace daƙiƙa tare da tuna min wacece ni?

Meyasa ban da gata?

Meyasa ban fito daga cikin ƙabilar Hausawa ba?
  Tuno nice ke yima kaina komai na buƙatar yau da kullum na rayuwa yana shirin tarwatsa ma'adanan sirrin dana ke ƙunshewa(ƙirjina),idan na tuna kama daga abinci,tufafi,neman lafiya,samar da muhalli nice ƙashin bayan samuwar waɗannan buƙatu na rayuwar Ahalina har a gangari kan wahalar ɗaukar ciki da rainon sa,haihuwa da reno har ya girma ya kai yaye sannan in fara fafutukar sanya shi a makaranta domin idan ba hakan na yi ba shima wani ɗawainiya ne tunda idan ban sanya su ba ta yaya zan cigaba da neman kuɗi da goyo?,a haka rayuwata take haka na tashi naga anayi tun iyaye da kakanni saɓanin MATAR BAHAUSHEN da muke rayuwa a gida ɗaya,tsabar kusancin da ke tsakanin mu ko ƙwaƙwƙwaran motsi ta yi ina jiyota saboda katangar ɗakin mu ɗaya, kullum tana gida tana rayuwa cikin aminci daidai da ruwan da ake ɗiba a rijiya na ga an samar mata da almajirin da ke janyo mata,yaje yayi mata cefane,har a kuɗin cefanen ta samu ta zuba adashe a kullum tana zaune a gida amman tafini sutura da rufin asiri,kullum itace cikin yin hidimar biki ko suna,canjin kayan ɗaki,kuma duk waɗannan kuɗaɗen da ta ke samu ajikin mijinta bata sana'ar komai,sannan kuma ba godiya,duk da na ga wasu na ƙoƙarin yin sana'a na yau da kullum acikin gidajen su anan unguwar ta mu amman banda maƙwafciyata ita ɗin bauɗaɗɗiya ce sam ta jahilci kalmar Kyautatawa balle kuma biyayya kullum ita a botsare take ta gagara sanin halin da wasu ƙabilun ke ciki da mazajensu, duk da hakan ban taɓa duba ga waɗannan ni'imomin da ke ɓulbula daga magudananta ba na fuskanci tawa rayuwar dan haka na fita biyayya, kwalliya tare da neman aljanna a ƙarƙashin ƙafar azzalumin mijina,ban taɓa jin sha'awa ko yin bore gareshi shi ba kullum cikin yi min huɗuba ya ke akan haɗa kaina da MATAR BAHAUSHE ba saboda ita ɗin ƴar gata ce ta ƙarshen lamba,alanƙosa ce ,kuma shagwaɓaɓɓiya ce idan kuma na sake na haɗa kaina da ita tabbas zan iya rabani da numfashina tare da gimtse bututun da na ke shaƙar iska da shi(Hanci)har sai na daina motsi,Na san kaɗan ne daga cikin aikin sa na san zai aikata fiye da abinda ya faɗa ya kashe Ni ya kashe banza tare da ƙona gawata ya jefar a kogi ya cuci yayana ya maidasu marayun ƙarfi da yaji dan haka na kasance kullum cikin takatsantsan tare da babbar kyautar da Allah ya yi ma wanda bai baiwa wata ƙabila acikin wannan ƙasa ta mu ta gado Najeriya,ƙasar da ya haɗa mabanbantan ƙabilu wanda a ƙiyasi ƙabilun cikin shi sun kai 371.......

Da sannu labarin zai zo muku ta alƙalamin Masoyiyar ku, labari ne mai cike da sarƙaƙiya tare da rikici,salon labarin zai taɓo matsalar da ke addabar wani yanki da fatan za ku bini a sannu tare da bani haɗin kai ga mai buƙatar a tallata masa hajar shi a saman shafi da ƙarshen sa ya tuntuɓi sai ya tuntuɓi wannan numban 08153144521 cikin farashi sassauƙa.




Ummu-jiddah.

BESTYN MIJINA Where stories live. Discover now