🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈
🎈🎈
🎈*BESTYN MIJINA*🎈

DAGA ALƘALAMIN:FARIDAT HUSAIN
MSHELIA(UMMU-JIDDAH).

*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*

https://chat.whatsapp.com/HsGW99EafuEG6xCUvurd2X

SHAFI NA BAKWAI.

Dariya ya fara yi ƙasa-ƙasa sanin ya samu lagon ta nan ta ke yace ta yi gida,

Jiki a sanyaye ta wuce buguzum- buguzum tamkar wacce ƙwai ya fashe ma a ciki,

Cikin sanyin jiki ta shiga ɗakin Anty iyabo wacce ta ke ƙira da Antyn Alabo ta ce"ki yi ma girman  Allah da ma'aikin sa idan karuwar mijinki ta kira polisawa kar sunana ya fito balle har a kaini chaji ofis",

Gyaɗa mata kai tayi tana jin maganganun ta na yi mata yawo a kunne dan sam bata fahimci me ta ke cewa ba balle har ta samu damar na ta amsa amma sanin halin Uwatale da ɗan banzan mita yasa ta ce"in sha Allahu ba za'a kira ba",

"Yawwa yar arziki irin albarka ki ce musu ma ni ce Lami ma wacce sam ba ta fito ko da hakuri ta ba ki ba kin ji"

Ta gyaɗa mata kai alamun "To",

Har ta juya za ta fita kuma ko me ta tuna sai ta dawo cikin raɗa ta ce mata"saura kuma kar ki tattara ya na ki ya na ki ki bar masa gida tun da ke ba ki zuciya kin yada kare ya ɗauka",

Ɗago dara-daran idonta ta yi wanda su ka rine suka dawo ja ta yi mata ƙuri dan yanzu hankalin ta ya dawo gareta,

Jin bata gwasale ta ya sa ta ci gaba  cike da karsashi"yo in ba haka ba me ne ne zai sa ki zauna namiji na wulaƙanta ki haka ko kuma raɗe-raɗen da nake ji  a gari ya zamto gaskiya ne",

Cikin rauni Antyn iyabo ta ke kallon ta tare da yi mata signal akan me suka ce"kila ba ki da uba ke shegiya ce ko kuma taurin kai ki ka yi ma iyayen ki ta hanyar guduwa daga garin aka ɗaura mu ku aure a bariki",

"sam ba haka ba ne da izinin iyayena na auri onyeye sai dai Mahaifina ya yi rantsuwa akan duk wanda ya ce zai yi zumunci da Ni zai cire shi daga ya'yan shi",

"Tabbas ba da son ran shi aka ɗaura min aure da onyeye ba kakan mu ne ya tsaya tsayin daka aka bani zaɓin raina",

"biri ya yi kama da mutum tabbas ashe shiyasa tsawon shekaru 20 ɗin da mu kayi tare amman ba mu taɓa ganin dangin ki ba ko daidai da rana ɗaya",

ta gyaɗa mata kai alamun "Eh"

ganin yanda Anty iyabo ta ke amsa mata magana da kai ya sa ta dasa aya amma sai taji sauran maganan na tsungulinta a ran ta ga ra ta furzo su ta huta"eh lallai kin ga zaɓin ran ki ganin idon ki,
shawarar da zan ba ki shine ki je ki nemi yafiyar iyayen ki saboda mijin ki ba mutumin kirki ba ne,mu muke wuni a gida a tare da shi muna ganin abinda ya ke aikatawa daidai da masu zuwa daga dangin shi da kike cewa wallahi yawanci suma karuwan sa ne,ke daga an faɗa miki gaskiya sai ki ce Hausawa munafukai ne to yanzu wa gari ya waya?",

"Ni"zuciyar Antyn iyabo ya ba uwatale amsa dan tabbas ta san ta bai ma onyeye rayuwar ta da komai nata gabaɗaya dalilin hakan ya sa ta guji gatan ta(yan'uwata)ta tare a Bariki ko garin su sam bata son zuwa kuma tun da ta zo garin Tudun bariki bata taɓa bari wani ɗan'uwanta ya zo in da take ba saboda gudun ya ga halin da ta ke ciki ya je ya faɗa ma iyayen ta dan duk da mahaifin ta yayi rantsuwa dangane da lamarin ta,mahaifiyar ta na tura yan'uwanta su je su duba mata Ni sanda muna lakwaja,

dalilin hakan yasa onyeye ya samu waje ya mayar da ni baiwar sa tare da mulkata  da baƙin zaluncin shi amma daga yau komai ya zo ƙarshe da izinin Allah,

Ɗagowa ta yi da niyyar yi ma Uwatale godiya amma sai ta ga fili nan da nan ta miƙe ta fara shirya kayanta a cikin ƙaton Ghana must go,

Wannan karon umurnin zuciyarta kawai ta ke bi saboda ta gaji da wannan wulaƙatacciyar rayuwar da ta ke buƙata,

BESTYN MIJINA Where stories live. Discover now