🎈🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈
🎈🎈
🎈BESTYN MIJINA🎈
    (MA FI SOYUWAR MIJINA).
     
 

DAGA ALƘALAMIN:FARIDAT HUSAIN
MSHELIA(UMMU-JIDDAH).




*Ga mai buƙatar a tallata masa hajar shi akan saman shafi ko ƙarshen shi akan farashi sassauƙa yana iya tuntuɓar wannan numban08153144521,mai talle shi ke da riba*




SHAFI NA BIYU.

Kuma Koda lamarin zai haɗa da hukuma kuwa, saboda ko da an kwashe su,za'a je ayi belin su saboda suna tare da hamshaƙan ƴan siyasa waɗanda ke goya musu baya akan duk wata husuma da za'ayi,haka su ka cigaba da kallon su har sai da Allah ya bai wa Amaryar Ɗan ƙasa ikon ture Falmata da ke jikinta,tayi kukan kura haɗe da rugawa a guje ta je ta jijjigo iccen da ke nutse acikin ƙasa nan da nan ta yi kan Falmata wacce ke tsaye cikin shirin zaman ko ta kwana sai haki take tana numfashi sama-sama,ganin yanda ta kwasa a guje yasa Anty iyabo (Turai)saurin  sauke kayanta dan dawowar ta kenan daga kasuwa,shawo kwanar gidan su da tayi,tayi mummunan gani da yasa ta shirin tafiya a tsaye,dan haka zafin nama ta yi kan su tare da sa ƙarfi ta ƙwace dogon katakon da ke hannun maƙwabciyarta tare da yin jifa da shi,dawowa kansu tayita hankaɗata gefe guda,amman ina sai yunƙuri ta keyi domin komawa babban burinta bai wuce ta shaƙo Falmata ba wacce ke yi mata kallon mara hankali,


cikin masifa Anty iyabon ta ce"Haba Lami,ya ina ƙoƙarin hana ki neman masifa ma kan ki kina neman shiga ta ƙarfi da yaji?,"yanzu idan aka kyaleki ki kayi kisan kai a tunaninki kyale ki za'a yi ne"

"Ina ruwanki uwar tsugudidi da iyeyi idan ba shishshigi da salon tsiya ba naki a wanne?ko an kasa dake?",

"Ko ɗaya na ga gyara kayan ka baya zama sauke mu raba dake dai  al'amuranki ba kya tunani akan mai zaije ya dawo?ko kin fi son in bar ki kiyi abinda zaki dawo kina danasani?

"Eh hakan nakeso"Hakan shine babban burina in ga na raba wannan fasiƙar da rayuwarta in ya so nima a kasheni,

"Subhanallah"cewar Anty iyabo wacce ke yi mata kallon taɓaɓɓiya can ta tsinkayo muryanta tana cewa

"to wai ma ina ruwanki da rayuwata ne iyabo eyeh? shin na kasa dake ne da kike shige min hanci da duƙunƙune?"shiru kawai nayi ina kallon ta cikin tausayawa,dan macen da Allah ya yi ma irin baiwar ta tabbas abar a tausaya ma halin da

nagaji!ta furta hakan cike da ƙaraji,na kuma gaji da sanya min ido da kika yi a al'amurana, bayan kowa yana da kashin nan a gindinsa na wani ne ya fito fili har ace ke Matar ɗan giya(ta nuno ta da yatsa manuniya)zaki zo tsakiyar mutane kina min kwarmato,bayan kowa ya san kema ba mutuncin ke gareki ba"cewar Lami cike da tsiwa bakinta har wani kumfa yake yi dan tsabar masifar da ke cinta arai,

Shiru Anty iyabo tayi ta kasa cewa komai saboda yanda maganan ya buge ta,ji tayi kowani ƙofar gashi na jikinta ya buɗe amman sai ta shanye cikin kwantar da murya tace"ba ruwana tabbas,duk da gyara kayanka ba zai taɓa zama sauke mu raba ba,amman tunda haka kika nuna Allah ya baki hakuri"ta furta hakan tare da komawa inda ta sauke shirgin kayan da ta ɗauko a kanta,

neman gammon ta ta shiga yi amman bata gani ba dan maganan da maƙwabciyarta Lami ta maka mata marasa daɗi sunyi tasiri akan ta matuƙa gaya,jikinta har wani karkarwa yake yi tsabar ɓaci rai,gammon kuwa tsabar ruɗewa  ya sa bata san  sanda ta yi jifa da shi ba ta yi kan su gudun tafka aika-aika,

Ganin zai ɓata mata lokaci yasa ta nemi taimakon ɗaya daga cikin dandazon matasan dake tsaye suna kallon faɗan domin ya ɗaurata,

Sai a lokacin taji nauyin cefanen da tayo na tulin doyar da ke shaƙe cikin ƙaramin buhun shinkafa tare da kayayyakin miya,ayayin da ta ɗakko har waƙa take yi cikin Yaren Yarbanci amman yanzu sai taji ƙafafunta sun yi mata nauyi da ƙyar ta ƙarasa gida.

BESTYN MIJINA Where stories live. Discover now