🎈🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈
🎈🎈
🎈BESTYN MIJINA🎈
    (MA FI SOYUWAR MIJINA).
     
 

DAGA ALƘALAMIN:FARIDAT HUSAIN
MSHELIA(UMMU-JIDDAH).

*Jiya na samu saƙo mai faranta zuciya daga yar'uwata marubuciya Zainab yar Libiya,tabbas ina son ki fisabilillah saboda Masoyin ka shi ne ke ganin kuskuren ka ya bi ka pc ya gyara maka dan haka wannan shafin na ki ne,ina godiya sosai*





*Ga mai buƙatar a tallata masa hajar shi akan saman shafi ko ƙarshen shi akan farashi sassauƙa yana iya tuntuɓar wannan numban08153144521,mai talle shi ke da riba*

SHAFI NA UKU.


Shin wa ya faɗa mata tsohon tarihin da na daɗe da binnewa acikin raina?,

Ta ya ya ta sa ni har ta ke tozarta ni cikin jama'ar unguwa?
 

"Zancen duniya ai ba ya ɓoya"

cewar zuciyarta wanda ya tallabota daga faɗawa dogon tunani maras tushe,dan haka tuni ta gasgata wannan zancen har ma ta daɗa da cewa,

"Musamman ma a irin wannan unguwa da muke rayuwa a cikinta na garin Tudun bariki,

Unguwa ce mai mai cike da tsegunguma dan haka wannan sam ba abin  mamaki ba ne"

"amma ya zamto dole  a gareni da in ɗau mummunan mataki akan Lami"

"kuma ya kamata in yi  ma tufka hanci ko dan in tseratar da mutuncin ya'yana mata guda 3 da su ke tasowa, gudun kar a zo a rasa mai auren su idan lokacin auren yazo",

tana cikin wannan tunanin ta ji an doko ƙofar cikin uwar ɗakanta da ƙarfin gaske,

har ta miƙe za ta yi ma yaranta  faɗa ta hango onyeye(mijinta)cikin ƙasaita yana jifanta da wani irin mugun kallo,

Ji ta yi cikinta ya bada wani irin sauti"ƙuuuuuuuu"alamun tana jin gudawa tunowa da tayi da bata aiko mishi da abinci daga shago ba gashi kuma ta dawo bata ɗaura sanwa ba,

Nan da nan jikinta ya fara rawa,ƙirjinta ya fara bugawa da sauri-sauri tsabar tashin hankali,

cikin mugun tsoro ta sakko daga kan gadon ta sa gwiywowinta biyu a ƙasa ta fara bashi hakuri cikin in'ina,

Sai cika yake yana batsewa ganin yana yin baya-baya tana ƙara bin shi da gwiywowinta biyu da ke daɓe a ƙasa ya sa yaji ya ƙulu,

Wani irin haushinta yaji tamkar ya shaƙeta ta daina numfashi gaba-daya dan haka ya dinga ja da baya,

Ita kuwa babban burinta bai wuce ta kamo ƙafafun shi biyu ba domin ta nemi afuwa akan Abin da ta aikata na ƙin ciyar da shi na tsawon yini guda amman yaƙi sauraronta ƙarshe da suka ƙure bango Ya ga zata taɓa shi da busashshen hannunta da tsabar wahalar dakan sakwara ya sa suka yi kanta,

kawai sai ya zaro belt ya fara dukanta,

tana ganin haka ta ƙwallara wani irin  ihun da ya janyo hankalin yaranta da ke falon nan suka haɗu suna bashi hakuri amma da yake azzalamin azzalumai ne wato sarki zalimu sai yayi kunnen uwar shegu  ya cigaba da zuba mata shi a jiki da iyakacin ƙarfin shi sai da  mata jina-jina,

Yaran da ke ƙoƙarin baiwa uwarsu kariya suma gargadi ya musu akan duk  shege ko shegiyar da ta iso sai ya haɗa da ita,

haka suna ji suna gani akayi ma Mahaifiyar su lilis ita kuka su kuka babu mai rarrashin wani,

Cikin jin haushi da yunwar da ke azalzalar shi ya ce"ki tashi ki fita ki yi min girki,minti 30 kacal na baki ki dafo min makaroni da wake ko jiki ya yi ɗumi"

BESTYN MIJINA Where stories live. Discover now