🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈
🎈🎈
🎈*BESTYN MIJINA*🎈

DAGA ALƘALAMIN:FARIDAT HUSAIN
MSHELIA(UMMU-JIDDAH).

*ZAFAFA WRITERS ASSOCIATION*

https://chat.whatsapp.com/HsGW99EafuEG6xCUvurd2X

SHAFI NA TAKWAS.

HAJIBULLAH POV.

Murmushi ya yi kafin ya ce"gidan su Falmata za mu saboda Ni na je amma ta ƙi fitowa hatta kuɗin asarar da lami ta yi mata na aika mata amma ta ƙi ta karɓa"

Turƙashi!cewar ɗan ƙasa,

"har kasa na ji gabana ya yanke ya faɗi"

"Raggun banza,to yanke ka yar",

Hararar shi ya yi ya fashe da dariya"kai da alama ai ba ka shirya auren nan ba kila Ni ne zan shiga daga cikin nan",

Wani naushi ya kai masa ya kauce saboda kishi jin yana danganta kan shi da falmata,

hakan ya sa shi  fesar da wani huci saboda yanda ya ji zuciyarsa na tururi nan da nan ya fara haɗa gumi,

Tattakawa Sani ya yi har ya iso gare shi cike da gwarzanta ka da muryan da ba alamun wasa a cikin ta ya ce,
"Ya kamata ka dawo cikin hayyacinka Hajibullah dan matuƙar kana son Falmata kuma kana son zama da Lami totabbas sai ka zamto jajirtacce",

"dan haɗa mata biyu bana ragwgwo ba nechakwakiya iya chakwakiya mu ke fuskanta dan mata ba su da daɗi kuma tunda kana son more rayuwa to tabbas ka fuskanci ƙalubale",

"dan haka zuwa gurin Falmata ba abu ba ne mai wahala,shawo kan ta abu  ne da za ka magance shi da fatar baki",

"Haka  ne tabbas ,zancen ka dutse abokina"

"Mu je ko"

"A'a,sai mun sauke farali dubi agogo ka ga lokaci ya yi

Duba ya kai kan agogon hannun sa ya ga ƙarfe ɗaya da kwata da ido ya yi ma Sani nuni da su tafi,


Alamu ya yi masa da ƙofar da zai fidda shi waje ba sai ya shiga cikin gidan ba ya yi saurin murɗawa ya fice,

Shi kuwa ya shige cikin gidan shi domin sallamar matan shi yayin da Hajibullah ke can waje yana gyara tsayuwar shi tare da soka hannun shi biyu a cikin aljihun wandonsa yana jiran fitowar Sani dan su shige masallaci,

Ji ya yi ya matsu da ya fito amman shiru ka ke ji tamkar Malam ya ci shirwa,jin har an fara ƙiraye-ƙirayen sallar kuma bai fito ba  ya sa ya shige cikin masallacin ya yi zaman shi,

Sai da aka tada iƙama sannan Sani ya shigo yana rarraba ido can ya hango Hajibullah a sahun gaba dan haka ya gyara tsayuwar shi haɗe da bin liman har aka idar,

Harara Hajibullah ya ke ta maka masa shi kuwa yana bin shi da murmushi sanin halin abokin na shi ya sa ya nuna mi shi babur ne ya tsayar da shi dan haka kai tsaye gidan su Falmata suka nufa sai dai suna shan kwanar gidan Hajibullah ya yi tozali da abinda ya sa jin shi da ganin shi ya ɗauke na wasu y'an daƙiƙu.

**** **** **** **** ****
TURAI POV

Anty iyabo wacce ke zaune a cikin motar da zai kai su garin ilorin rasa wani takamammen tunani ya kamata ta fara yi ta yi saboda shekara 20 ba kwana 20 ba ne,

Ta bar danginta na tsawon wannan lokacin ba tare da ta taɓa waiwayar su ba saboda son zuciya da biye ma zugar maƙiyin ta shaidan,

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 02, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BESTYN MIJINA Where stories live. Discover now