🎈🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈🎈
🎈🎈🎈
🎈🎈
🎈BESTYN MIJINA🎈
    (MA FI SOYUWAR MIJINA).
     
 

DAGA ALƘALAMIN:FARIDAT HUSAIN
MSHELIA(UMMU-JIDDAH).

GODIYA.
Ina mai farawa da sunan Allah mai rahama mai jinƙai ,ubangiji buwayi gagara misali sarkin da baya bacci kuma gyangyaɗi bai taɓa kama shi ba,miliyoyin salati su ƙara ninkuwa ga masoyin raina Muhammadur-Rasulullahi(SAW)da iyalan sa tsarkaka da sahabban sa zaɓaɓɓun Allah.
  Ina godiya ga Allah da ya bani ikon fara rubutun wannan littafin mai albarka,ina kuma roƙon sa da ya bani ikon rubuta daidai ya sa rubutun nan da xan yi ya zamto silar shiryuwar dubannin ma'aurata ya kuma bani ikon kammalashi cikin ƙoshin lafiya.

ARASHI.
Wannan labarin Ƙirƙirarren labari ne ban yi shi don cin zarafin wani/wata ba,ban kuma yi shi dan cin zarafin wata ƙabila ba sai dan fito da darasi ga Matan Hausawa ƙalubalen da wasu mata ke fuskanta a kudancin ƙasar nan,dan haka duk wacce/wanda ya yi daidai da rayuwar sa yayi hakuri arashi ne,Sunayen gari ko unguwa duka ƙirƙira ne.

GARGAƊI.
Ban yarda wani ko wata su juya min labari ba zuwa wani sigar sai da izinina.

*SHAFI NA ƊAYA*

Ƙasar Najeriya ya haɗa mabanbantan ƙabilu wanda a ƙiyasi ƙabilun cikin shi sun kai kimanin 371,ina ɗaya daga cikin ƙabilar data fiito daga masarautar da ke ɗefin arewacin Najeriya (Kwara),Sunana Hafsat amman iyayena suna ƙirana da Turai,
an haife Ni a ilorin wacce ta kasance helkwatar mulki ta jihar Kwara,sannan fadar ilorin tana da nisan kilomita 450 idan aka bi hanyar ilorin zuwa Makwa,zuwa Bidda,zuwa Minna,zuwa babbar birnin tarayyar Najeriya(Abuja),idan kuma aka bi ta hanyar lakwaja,zai yi kusan kimanin kilomita 500 zuwa Abuja,na fito daga masarauta mai cike da abubuwan al'ajabi sannan wani yanki ce acikin tsohuwar Daular Oyo,daula mai tsohuwar tarihi.
  Garina ilorin birni ne kuma matattara ce ta yarurruka mabanbanta waɗanda suka dunƙule suka zama abu guda,Yarbanci a matsayin babban yare,Fulani a matsayin sarakuna(al'adar Yarbawa itace babbar al'adar garin,sannan Fulani suke sarautar garin tare da faɗa aji tun a lokacin da duniya ke kwance)wannan dalilin ya sa aka bashi cikakkiyar damar da ya taɓa zama a babbar cibiyar cinikayya sannan masaukin attajirai kuma rundunar mayaƙa kasancewarsa shine ɗefin arewacin Najeriya(kasancewar garin na ilorin a ƙarshen Arewa ta Kudu,kuma ƙarshen kudu ta arewa)sannan kuma a ƙasar yarabawa ya ke,gari ne mai albarkar noma a dalilin hakan ta samu cikakkiyar damar haɓakar tattalin arziki,bunƙasar ilimi,tasirin siyasa dss.
  Kafuwar masarautar mu ya biyo bayan ayyana jihadi  da wani mashahurin Malami yayi a 1823 bafillace ne kamar yanda kakana ya bani labari,shima kakansa ya bashi labarin,bayan an haɗa karfi da ƙarfe an fatattaki baƙin zalunci da mummunan danniya da tsohuwar Daular Oyo ta ke musu, inda jama'a da  suka haɗa da yan kasuwa waɗanda haraji ya addaba,bayi  da ake musguna musu,Fulani makiyaya da kuma asalin maharban da ke zaune a wannan yanki,so bayan an fatattaki tsohuwar Daular sai aka ɗaura ɗamarar yin jihadi da wanzar da adalci bayan an  fatattaki duk wani zalunci,al'ummar da ke gefen garin duk suka koma ƙarƙashin mulkin masarautar mu ta Fulani,duk da an fuskanci barazanoni da dama ta ciki da waje saboda yanda ya ɗaura ɗamarar ɗaura wannan masarauta akan turban addinin Islama dan har ma  sai da aka nemi haɗewa da daular Shehu Usmanu 'Ɗan fodiyo,aka kuma haɗen sannan aka nemi mataimaka daga Hausawa,Fulani, Yarabawa,dan haka masarautar mu ta naɗa Sarkin gambari (Sarkin Hausawa)wanda shike kula da dukkannin abubuwan da suka shafi Hausawa kamar kasuwancinsu da saura manyan sadaukan Hausawa (mayaƙa),da yan gudun hijira duka shike kula dasu,sai sarki Arɗo(Sarkin Fulani) wanda ke kula da dukkannin Fulani makiyaya dake warware a jejena na wannan yankin musamman kudu da birnin na ilorin,sai Bologun alamanamu(Sarkin Yarabawa)shima an naɗa shi domin sauke nauyin duk da ya shafi ƙabilarsa dan haka mulkin masarautarmu yana tafiya akan tsari da wanzar da adalci a tsakanin al'umma.
   Fitowata daga cikin wannan ahali mai cike da tarihi na alfahari sam bai sanya Babana ƙin bani nagartaccen ilimin addinin musulunci da na boko ba,dan haka na yi primary da secondary duka a jihata kafin inje jami'a in karanci fannin girke-girke har na zamto babbar chef wacce ke shige da fice domin tsayuwa akan ƙafafuwata kamar yanda aka san dukkanin wata macen ƙabila,dan a yare ne kawai na ke bahillata amma a zahiri idan ka ji harshena da shigata zaka ɗauka ni Bayarbiya ce,dan haka tun tasowata na gina kyakkyawan alaƙa da gidan Bologun gambari(Sarkin Hausawa),mahaifiyata ta kasance aminiya ga surukar gidan dan haka duk wata al'ada ta Hausawa anan na ke ganin shi,har naji ina sha'awar ziyartan Arewacin Najeriya domin al'adar su ta killace matansu guri guda yana burge ni matuƙa gaya, babban burina in yi aure a Arewa amman sai Allah bai yarje min ba inda Allah ya haɗa ni aure da wani kilallallen ɗan duniya mai suna Nafi'u,ibira ne ɗan garin okene inda ya nuna min soyayya matuƙa,sam iyayena ba su amince da shi ba amman na yi tsalle na dire na ce sai shi,an samu ɓaraka sosai dangane da lamarin aurena saboda riƙon Fulani da al'ada ga kuma irin gidan da na fito ta sarauta, amma da ya ke kakana na gurin Mahaifi na raye sai ya ce abar ni in auri zaɓin raina aikuwa ya biya komai na al'ada aka ɗaura mana aure da onyeye(sunan shi na al'ada),ya ɗauke ni sai cikin jahar shi ta lokoja anan na ga ƙazantacciyar rayuwa mai cike da ƙyama da gusar da hankali, saboda yanda aka maida zina tamkar ado ko kwalliya ma zance,gasu dai Musulmai a baki amman sam-sam al'adunsu ya saɓa da Tsaftatacciyar addinin mu ta Islama dan haka a karon farko na fara danasani wanda Bahaushe ya ƙirata da ƙeya,na ji ina ma zan'iya maida hannun agogo baya tabbas da na koma gaban iyayena na bari har Allah ya fito min da wani daban,matsala ta biyu dana fuskanta itace ƙabilanci,dan gaskiya basu so na su ya auri wani yare ba dan haka na dinga fuskantar matsala tare da kyara da tsangwamar da ya tilasta Mijina yin gudun hijira daga garin shi ya koma Garin Tudun bariki wanda gari ne da ke da maƙwaftaka da Abuja,kuma ya zamto cibiyar Kasuwanci a ƙarƙashin jihar Neja,anan komai ya fara,nan ne tushen kowace matsalata,ganin dare ya tsala yasani kwanciya saboda idan ban runtsa ba ni da ƙara kwanciya sai daren gobe idan mai duka ya kaimu.
Wannan kenan.


BESTYN MIJINA Where stories live. Discover now