BABI NA ASHIRIN DA BIYU

195 25 1
                                    

*RABON AYI*

*©Fareeda Abdallah*

_*22*_

*Ku zo ku sayi data a gurina sai ku cigaba da karatu💃🏽💃🏽👇🏽😘😘*
_Ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ki tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online ki kira ni ta 09077591726. In sha Allah cikin daƙiƙu ƙalilan datar da kika siya zai sauka a wayarki👌🏽_

*MTN data price👇🏽*

500 MB 👉🏽 N150
1GB   👉🏽 N280
2GB  👉🏽 N550
3GB 👉🏽 N800
4GB 👉🏽 N1100
5GB 👉🏽 N1350
6GB 👉🏽 N1600
10GB👉🏽 N2500

*AIRTEL data price👇🏽*

300MB 👉🏽 120
500MB 👉🏽 150
1GB 👉🏽 N300
2GB 👉🏽 N600
5GB 👉🏽 N1350
10GB 👉🏽 N2500
20GB 👉🏽 N5000

*GLO data price👇🏽*

1GB 👉🏽 N500
2.9GB 👉🏽 N1000
4.1GB 👉🏽 N1500
5.8GB 👉🏽 N1950

*9MOBILE data price👇🏽*

500MB 👉🏽 N500
1.5GB 👉🏽 N1000
2GB 👉🏽 N1250
3GB 👉🏽 N1600
4.5GB 👉🏽 N2000

*_Na mu ba irin na su bane shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_*

Washe gari Fareeda ta tashi lafiya ƙalau, babu wani ciwo ko ƙanƙani da take ji a jikinta.

Amma saboda ɗoki da zakwaɗin cikin jikinta da Mukhtar yake yi haka ya dinga tarairayarta, duk inda ta saka ƙafa yana biye da ita. Duk aikin da ta kamo haka yake saka hannu ya tayata suyi su gama.

Ba yadda baiyi da ita ba kan ta zauna ta huta ta ce a'a! Ita baza ta iya kwanciya ba tare da ta gyara ɗakunanta ba.

Ya ce ta barshi yayi aikin, nan ma ta ce a'a! Baza ta iya zama tana kallonshi shi kaɗai yana aiki ba.

Wannan shi ne dalilin da yasa ya saka sauƙaƙan kaya marasa nauyi ya dinga taimaka mata. A yinin wannan rana, sun sabunta soyayyarsu fiye da yadda ake zato.

Minti ɗaya biyu zai kalleta da faffaɗan murmushi a fuskarsa ya ce
   "Ina son ki Fareeda."

Idan ya faɗi haka wani irin girma kanta yake yi kamar zai fi ƙarfin gangar jikinta, zuciyarta ta cika ta tumbata da matsanancin farin ciki, har takan manta yanzu ba ita kaɗai ce da shi ba.

A yangace cike da ƙasaita take mayar mishi da martanin murmushinsa.
  "Nima ina son ka Uban ƴaƴana."

   "Allah ya barmu tare"

   "Ameen thumma Ameen"
Suke haɗa baki su biyun gurin amsa kyakkyawar addu'ar da yayi musu. Sai su ƙara musayar murmushi sannan su cigaba da aikin da yake gabansu.

Irin kalaman soyayyar da ya dinga faɗa mata a wannan rana, kamar lokacin da ta samu cikin farko ne, tana Amarya.

Suna bala'in mararin juna tun gishiri bai fara sauka daga kan kaza ba.

Da an ɗauki ƴan mintuna zai riƙo ta zuwa jikinsa, cikin salon soyayya yake shafa lafaffen cikinta da in banda likita ya tabbatar tana da ciki babu wanda zai ce akwai ajiyar ɗa a ciki saboda shafewarsa.
   "Baki gaji ba Matata? Ba na so ku wahala ke da Babys ɗina..."

Ta zazzaro idanu a tsorace ta ce
   "Babys ɗin har guda nawa Habeebee?"

   "Uku mana! Wancan karon kin bani biyu rayayyu kuma lafiyayyu yanzu ba sai ki bani uku ba?"
Ya raɗa mata a kunne, har lokacin yana shafa cikinta.
  
   "Ban yarda ba, ni dai gaskiya ban yarda ba Habeebee. Haihuwa wahala, ko ɗaya Allah ya bani Allah ya saka mishi ko mata albarka."
Kukan shagwaɓa ta sakar mishi bayan gama maganar tana bubbuga ƙafafunta a ƙasa.

RABON AYIWhere stories live. Discover now