*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_
_*10*_
Lallausan murmushi ta saki jin cewar yana ƙofar gida. Mai gadin gidan ta kira, tayi mishi umarnin a buɗe ma babban baƙonta ƙofar gida ya shigo da motarsa.
Sai kuma ta kira ɗaya daga cikin ƙannenta biyu da suke zaune tare da ita da ƴaƴanta ta bata umarnin ta shigo da baƙonta cikin falon. Daman tun tuni ta sa sun ƙalƙale ko ina an baɗe shi da turaren wuta.
Tun ɗazu ta yi wanka, zaman jiran ƙarasowarsa take yi Ramlah ta kai mata saƙonta.
Tun da ya shigo cikin kaduna ya faɗa mata ya iso, ko da ya ce mata gida zai fara zuwa yayi wanka har da kukanta na kissa.
Cikin shagwaɓa ta roƙe shi to don Allah idan ya je gida kar ya daɗe, tun ɗazu ta gama shirya mishi kayan abinci ta yi kwalliya zaman jiranshi kawai take yi.
Ta sake ƙasa ƙasa da murya tana ɗan jan hanci, kamar har lokacin kuka take yi ta ce
"Aban Twince, ka ganni zaune hannuna a kunci, idanuna sun ƙure ƙofar shigowa da kallo, babu abinda suke so da buri sai suyi tozali da kyakkyawar fuskarka mai cike da annuri da haske, irinna mai riƙo da Addinin musulunci.Hancina a buɗe yake, babu abinda yake muradi sai ya shaƙi daddaɗan ƙamshin da jikinka ke fitarwa Nawan"
Kunnuwana a burbuɗe suke, babu abinda suke kwaɗayi sai suji saukar sautin tattausan muryarka mai cike da amo da kwarjini na ingarman namiji.
Don Allah ka tausaya ma zuciyar da kullum take ta tsallen daka tana jiran isowar abokin soyayyarta.
Kar ka bari Aunty Fareeda ta tsare ka da surutunta har mu bushe ni da abincin da na shirya maka wajen zaman jiranka."
Daga haka ƙit ta katse wayar, tana jin shi yana ta sauke numfashi sama-sama tsabar yadda kalamanta suka rugurguza ɗan ragowar kuzarinshi.
Da yake ɗan halas ne, ko da ta kalli agogo yanzu sai ta ga mintuna arba'in da bakwai kenan da gama wancan wayar tasu. Lallai Mukhtar za'a je da shi.
Ashe ma bashi da wahalar sha'ani kamar yadda kullum Fareeda take cewa
"Ke ƙyale ni, Mukhtar murɗaɗɗen mutum ne. Lallaɓawa nake yi ina haƙuri don mu zauna lafiya."
Tunanin Fareeda a wannan gaɓar da tunanin irin maganganun da suke yi a lokuta mabanbanta yasa ta jan tsaki ƙasa-ƙasa."Ƙawata lafiya kuwa?"
Ramlah ta tambayeta."Ba komai ƙawata. Wani banzan tunani ne ya faɗo min arai. Ki jira ni anan pls in sallami Aban Twince, idan ya tafi sai in baki cikon kuɗin."
Ta miƙe da hanzari ta fara sabunta kwalliyarta, a fuska kaɗai za'a kalli Fatima asan tana cikin matsanancin farin ciki.
Cikin lokaci kaɗan ta rambaɗa wani ubansun kwalliya, kamar wacce za ta je gasar fitar da sarauniyar kyau ta jihar kaduna. Ta ɗauko wani ɗan ubansun leshi da aka yi mata ɗinkin doguwar riga, daga sama ya kamata tsam, daga gurin gwuiwarta zuwa ƙasa sai rigar ta baje. Ta ɗauko wani siririn gyale da zai shiga da leshin ta rataya a kafaɗa, ta yi kyau sosai.
Ƙawarta Ramlah sai zabga mata kirari take yi ita kuma kanta yana ƙara kumbura. Daga bisani ta fice daga ɗakin da salon tafiyar za tayi baza tayi ba, tana wani rangaji kamar reshen bishiya a iskar damina, hannunta riƙe da wannan turare wanda Ramlah ta karɓo mata.
A ƙofar shiga cikin falon ta tsaya ta buɗe turaren ta zuba fiye da rabi a jikinta, nan take gurin ya ɗume da wani irin ƙamshi mai tafe da ƙauri-ƙauri.
YOU ARE READING
RABON AYI
Ficción GeneralLabarin ibtila'in da yai ta afkawa Fareeda matar Mukhtar a dalilin satar fita