*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*27*_
*Ku zo ku sayi data a gurina sai ku cigaba da karatu💃🏽💃🏽👇🏽😘😘*
_Ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ki tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online ki kira ni ta 09077591726. In sha Allah cikin daƙiƙu ƙalilan datar da kika siya zai sauka a wayarki👌🏽_*MTN data price👇🏽*
500 MB 👉🏽 N150
1GB 👉🏽 N280
2GB 👉🏽 N550
3GB 👉🏽 N800
4GB 👉🏽 N1100
5GB 👉🏽 N1350
6GB 👉🏽 N1600
10GB👉🏽 N2500*AIRTEL data price👇🏽*
300MB 👉🏽 120
500MB 👉🏽 150
1GB 👉🏽 N300
2GB 👉🏽 N600
5GB 👉🏽 N1350
10GB 👉🏽 N2500
20GB 👉🏽 N5000*GLO data price👇🏽*
1GB 👉🏽 N500
2.9GB 👉🏽 N1000
4.1GB 👉🏽 N1500
5.8GB 👉🏽 N1950*9MOBILE data price👇🏽*
500MB 👉🏽 N500
1.5GB 👉🏽 N1000
2GB 👉🏽 N1250
3GB 👉🏽 N1600
4.5GB 👉🏽 N2000*_Na mu ba irin na su bane shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_*
_LOKACI mai zuwa da baƙin al'amura💔 Tarihi ba shi tausayi komai kayi za'a bada labari walau na kirki ko akasin haka😪 Mai jini a jika yakan ji shi kamar babu wanda ya kaishi izzah💪🏽 Shi yasa yake cin karensa babu babbaka ba tare da tunanin LOKACIn da zai girbe shukar kyawawan ayyukansa ko akasinsu na nan zuwa ba💔. Wannan a dunƙule tsokaci ne dangane da Labarin LOKACI wanda ni Fareeda Abdallah nake rubutawa. Masu karatu wai yaya ne? Cikakkiyar ƙaunar da za ku nuna min shi ne kuyi dafifi wajen siyan labarin lokaci a N500 kacal a Hikaya Bakandamiya. Wani ƙarin garaɓasar shi ne, da wannan ɗari biyar ɗin da za ku biya za ku samu damar karanta littattafan manyan marubuta irinsu Sumayya Abdulƙadir, Rufaida Umar, Lubnah Sufyan, Fatima ibrahim garba ɗan borno, da sauransu. Ku sauke app ɗin Bakandamiya hikaya a play store, duk wacce bata iya reg ba ta tuntuɓeni a 07039080978 zan koya mata yadda za tayi. Na gode🥰
https://hikaya.bakandamiya.com/lokaci-babi-na-daya/ 👈🏽 Domin karanta ɗanɗanon labarin, a danna wannan link ɗin.Kwanansu Shahid biyu a asibiti aka sallamesu, Alhandulillahi sun warke garas, kamar ba su ne aka fice da su ranga-ranga ba. Daga asibiti kai tsaye Hajiyarmu gidanta ta wuce da su ba tare da neman shawara ko amincewar Mukhtar ba.
Shi ɗin ma dai bai ja da zafi ba, ganin yadda Hajiyar ke ciki da shi lallaɓawa yake yi su rabu lafiya. Bai gane tara shi take yi ba sai da aka sallamesu daga asibiti suka koma gida. Wankin babban bargo tayi mishi ƙal kan yadda ta fuskanci yana tafiyar da lamuran zamantakewar iyalanshi.
Ta kuma ƙara da faɗa mishi matuƙar bai zama jajurtaccen namiji mai iya danne zuciyarsa lokacin fushi ya dinga bincike a nutse lokacin da aka faɗa mishi faruwar wani abu tabbas zai rusa gidanshi da kanshi.
Sunkuyar da kanshi ƙasa yayi yana bata haƙuri har ya fahimci ta gama. Da gaske kuma ya gano kuren da ya aikata wajen yanke ma Fareeda hukunci, amma in Allah ya yarda zai kiyaye gaba wajen sake ɗaukar mataki da gaggawa kan duk abinda zai ji daga sama.
Acan gidanshi kuwa, wani irin zama ne ake yi mare daɗi ko kaɗan tsakaninshi da matan biyu. Gagarumin fushi yake yi da Fatima, duk yadda ta kwashe kwana tana jinyar shaƙan da yayi mata kallo bata ishe ba. Ya kulle duk wata ƙofa da zai bata damar da za tayi mishi wani bayani nata da yake ɗauka na ƙarya da rainin wayau.
Ɓangaren Fareeda kuma shi yake cusu cikin kwantai. So yake su shirya da gaske, ita kuma ta ƙi bayar da damar hakan. Bata kuma fito fili kai tsaye ta nuna mishi fushi take yi mai tsanani da shi ba, wani irin gashin ƙuma take yi masa sannu a hankali. Wasarere take yi da al'amarinsa kamar auren dole aka yi mata da shi.
YOU ARE READING
RABON AYI
General FictionLabarin ibtila'in da yai ta afkawa Fareeda matar Mukhtar a dalilin satar fita