BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA

197 28 2
                                    

*RABON AYI*

*©Fareeda Abdallah*

_*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_

_*21*_

Duk da matsananciyar yunwar da yake ji, ɗan kaɗan ya tsakuri abincin ya kora da ruwa. Duk ƙamshin da naman yake baɗawa ko buɗe ledar baiyi ba balle ya ɗanɗana.

Abu ɗaya da ya iya yi shi ne saka ledar naman a cikin firij, saboda kar ya canza ɗanɗano zuwa safe tunda akwai kayan haɗi a ciki.

Yana gama cin abinci ya shige cikin ɗakinsa. Hanci ya buɗe sosai ya shaki wani ƙamshi mai bala'in daɗi na turaren wuta, wanda a ɗazu sa'adda ya shiga duba Fareeda hankalinshi yayi gaba, sam bai ji ƙamshin ba.

   "Hmmm! Fareeda ba dai son ƙamshi ba."
Ya faɗa a fili sa'adda ya buɗe banɗakin nasa ya ji ƙamshin turaren wutan ya daki hancinshi.

Yana gama biyan buƙatarsa bai ɓata lokaci wajen yin shirin barci ba, ya gama komai ya canza ƙwan lantarki zuwa mai duhu ya bi lafiyar gado.

Jikinsa a saɓule, wayarsa ya janyo ya danna mata kira, nan take kamfani suka faɗa mishi wayar a kashe take. A dole ya haƙura ya kwanta ba don ransa ya so hakan ba.

Allah ya sani yau ya saka ran jin ɗumin jikinta, yayi kewarta, irin sosai ɗinnan. Sai a lokacin ma yake tunawa ashe rabonshi da ita tun dawowar da yayi ya zo mata da zancen zai auri Fatima.

Tun lokacin ta raba musu makwanci. Shi kuma duk ƙulafucinta da yake yi bai taɓa nuna mata ya damu da raba makwancin ba.

A sannu ya runtse idanunsa, yana jin yadda wani matsanancin kewa da sha'awarta ke ƙara lulluɓe shi. Zuciyarsa cike da fatan nannauyan barci yazo yayi awon gaba da shi.

Bayan tsawon lokaci yana juye-juye daƙyar ya samu barci ya ɗauke shi a wahalce.

****

Motsin da ya ji a kicin yasa shi ƙarasawa da sassarfa. Ita ya gani, tana tsaye gaban cabinet  tana fasa ƙwai a cikin roba.

A firgice ta juya jin anyi ma ƙugunta wani wawan damƙa. Ganinshi yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta kwaɓe fuska, tayi narai-narai da idanunta ta ɗan tura baki gaba
   "Ashe kai ne, ka tsorata ni..."

Cikin salo ya juyo da ita suna fuskantar juna. A sannu a hankali yana riƙe da ita ya dinga matsawa da fuskarsa zuwa tata, ita kuma ta dinga ja da kanta baya har sai da ta kusa kwantar da kanta kan Cabinet ɗin
   "Abee ka bari mana don Allah, za ka sa inyi ɓari fa."
Tayi maganar tana zazzaro idanu ƙirjinta na bugawa. Bata san me yasa ba sam ba ta son ya sumbace ta.

Hannayensa ya ɗaga daga ƙugunta zuwa bayanta ya tallabota dakyau, a hankali ya janyota ya matso da ita tsakiyar kicin ɗin, har lokacin yana riƙe da ita.

Murmushi ya sakar mata. Ita kuma ta ƙara daidaita yanayin fuskarta zuwa ba yabo ba fallasa.

   "Jiya, na zaci zan tarar kin shirya min kyakkyawan tarba? Me yasa kika ƙi zuwa ɗaki na? Kuma nai ta ƙwanƙwasa ƙofarki kina ji na kika ƙi buɗewa"

Idanunta ta wulƙita kamar tana harara, kamar kuma tana kallon gefe da gefe.
   "Abincinka, da duk wani abu da na san za ka buƙata na ajiye maka. Ɗakinka duk da ko wane lokaci a gyare yake sai da na sake ƙalƙale shi. Me kuma kake buƙata bayan waɗannan Habeebee?"

   "Ke"
Ya amsa kai tsaye.
  "Ke nake buƙata Fareeda! Allah ya sani ina kewarki..."

Katse shi tayi ta hanyar sakin wata irin dariya a sakalce.

RABON AYIWhere stories live. Discover now