*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*25*_
*Ku zo ku sayi data a gurina sai ku cigaba da karatu💃🏽💃🏽👇🏽😘😘*
_Ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ki tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online ki kira ni ta 09077591726. In sha Allah cikin daƙiƙu ƙalilan datar da kika siya zai sauka a wayarki👌🏽_*MTN data price👇🏽*
500 MB 👉🏽 N150
1GB 👉🏽 N280
2GB 👉🏽 N550
3GB 👉🏽 N800
4GB 👉🏽 N1100
5GB 👉🏽 N1350
6GB 👉🏽 N1600
10GB👉🏽 N2500*AIRTEL data price👇🏽*
300MB 👉🏽 120
500MB 👉🏽 150
1GB 👉🏽 N300
2GB 👉🏽 N600
5GB 👉🏽 N1350
10GB 👉🏽 N2500
20GB 👉🏽 N5000*GLO data price👇🏽*
1GB 👉🏽 N500
2.9GB 👉🏽 N1000
4.1GB 👉🏽 N1500
5.8GB 👉🏽 N1950*9MOBILE data price👇🏽*
500MB 👉🏽 N500
1.5GB 👉🏽 N1000
2GB 👉🏽 N1250
3GB 👉🏽 N1600
4.5GB 👉🏽 N2000*_Na mu ba irin na su bane shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_*
https://hikaya.bakandamiya.com/lokaci-babi-na-daya/ Ƴan'uwa ku danna wannan link ɗin, kai tsaye zai kai ku page ɗin Bakandamiya hikaya domin karanta sabon labarin da ni Fareeda Abdallah nake rubutawa, sunan labarin LOKACI, daga babi na ɗaya za ku cigaba da danna *Next* zai kai ku har babi na huɗu.. Da fatan za'a nuna min ƙauna ta hanyar yin dafifi wajen karantawa, comment, yin rating ɗin labarin. Na gode😘😘😘
Kamar a mafarki, Fareeda ta ji muryar Sayyid da Shahid sun yanka wani rikitaccen kuka mai cike da ƙara da taratsi. A firgici tayi wani irin juyi ta dirgo ƙasa daga kan kujera, da sassarfa ta fice don gane ma idanunta abinda yake faruwa.
Ƙanƙance idanunta tayi da wani irin bala'in ɓacin rai tana kallon Fatima da ta riƙe hannayen Shahid da hannunta ɗaya, ɗayan hannun kuma babu tausayi babu jinƙai ko tunanin ƙaramin yaro ne a gaban Fareeda ta sake ɗaga hannu ta tsinka ma yaron mari.
Da Shahid da aka tsinkawa mari, da Sayyid yake tsaye gefe ɗaya ya ƙanƙame hannayensa a ƙirji yana makyarkyata cikin tsoro da firgici, a tare suka sake ƙwalla ihun kuka.
Ita kuwa Fareeda kawar da kanta tayi da sauri ta lumshe idanu, nan take suka cicciko da hawaye. Wani irin zafi ya lulluɓeta lokaci ɗaya, har wani ƙaiƙayi take ji a kumatunta kamar ita aka tsinkawa mari.
Da wani irin fusata da ɓacin rai matsananci ta buɗe idanunta da suka canza launi lokaci ɗaya, ta ɗaga ƙafa a fusace za ta ƙarasa gurin Fatimar sai taja ta tsaya cak, tunawa da tayi da wata magana ta Malam bahaushe da yake cewa.
"Ka so naka, duniya ta ƙi shi. ka ƙi naka, sai duniya ta so shi."Fatima da take kallon yanayin Fareeda ta ƙasan idanunta ganin ta ja ta tsaya sai ta sake ɗaga hannunta na dama fuska cike da murmushin mugunta ta sake fallawa yaron mari, sannan ta saki hannayensa haɗe da ture shi ya faɗi ƙasa yana rusa kuka.
"Don Uwarka waccan da take tsaye zan nuna maka kai ƙaramin mare kunya ne. Idan ita gantalalliya ce ta kasa baka tarbiya mai kyau ni zan koya maka."
Da gama faɗin haka sai taja ta tsaya ta riƙe ƙugunta, jira take Fareeda ta zaburo ta naɗa mata nata marukan kamar yadda tayi ga ɗanta.Sai taga ko da Fareeda ta ƙarasa gurin ɗanta ta ɗaga jikinta na rawa ta rungumeshi a ƙirjinta. Ta ƙarasa kusa da Sayyid ta kama hannunsa suka nufi ɓangarenta, har lokacin jikinta bai daina rawa ba.
YOU ARE READING
RABON AYI
General FictionLabarin ibtila'in da yai ta afkawa Fareeda matar Mukhtar a dalilin satar fita