HAUSA

1 0 0
                                    

FA’IDA DAGA AL-KUR'ANI... 17

Allah s.w.a Yana bada labarin yanayin da ranar Al-Ƙiyama za ta kasance da abubuwan da za su faru a cikintai, daga ciki;

{وَجِاْيٓءَ يَوۡمَئِذِۭ بِجَهَنَّمَۚ يَوۡمَئِذٖ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ وَأَنَّىٰ لَهُ ٱلذِّكۡرَىٰ *يَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي قَدَّمۡتُ لِحَيَاتِي} سورة الفجر، آية ٢٣-٢٤.
{Aka kuma zo da Jahannama a wannan ranar. To fa a wannan ranar ne mutum zai tuna (sakacinsa), ta yaya wannan tunawar za ta yi masa amfani? * Zai ce: “Kaicona, ina ma da na gabatar (da ayyukan alheri) a rayuwata!”} Suratul-Fajr, aya ta 23-24.

Nadama mafi girma da muni da mutum zai tsinci kan shi a cikinta kenan!! Yi iya bakin ƙoƙarinka bisa rahamar Ubangiji kar ka samu kan ka cikinta!! Ka dage wurin yaƙar shaiɗan da son zuciyarka domin gina tabbatacciyar rayuwa mai kyau.

✍🏽

101 QURAN STORIES AND DUAWhere stories live. Discover now