ƴa MACE

3 0 0
                                    

KE ƊIN NAN KI YARDA KE MAI TSADA CE A ADDININ MUSULUNCI❤️

Daga taskar Shaikha Zainab Ja'afar Mahmud

Mace a addinin Musulunci a matsayin ta na UWA Allah Maɗaukakin sarki ya bata gata na musamman domin ya sanya yi mata biyayya da ƙyautayi a gareta hanya ce da zata gadarwa da mutum zuwa Aljanna ko samun Aljanns madaukakiya .......

KE ƊIN NAN a matsayin ki na 'ya bai yarda a tozarta kiba ko a wulakanta kiba ko wofantar dake ba,
Ballama ya sanya cewa kula dake da tarbiyantar ki da ɗauke buƙatun ki da aurar dake a hannun nagartancen namiji dalili ne da zai gadarwa da wanda da yayi wannan aiki samun Aljanna

Domin Manzon Allah
S A W yace duk wanda ya kula da ya'ya mata guda biyu ya dauke bukatun su da larurorin su ya tarbiyyartar dasu zasu zamto mishi kariya daga wutar jahannama ranar gome kiyama

KE ƊIN NAN  addinin ya sanya ki a matsayin ƴar uwa da za'a kula da ita a sa'ilin da akace babu uba a raye,
Ba'a yadda ki tsaya ki rasa inda zaki sa kanki ba,
Ba'a yarda ki fita kije kiyi aikin karfi da kwanji da wahala ki nemo kici ba sai a ka sanya ragamar ki ajikin dan uwan ki namiji wanda Allah Maɗaukakin Sarki ya ɗora mai wannan nauyi kuma zai tambaye shi akan shi ranar gobe ƙiyama

KE a matsayin ki na matar aure addinin musulunci ya sanya kulawa dake da ɗauke Miki nauye nauye da wahalallu na rayuwar ki a matsayin dole a wuyan wanda Allah Maɗaukakin Sarki ya sanya a matsayin abokin rayuwar kine ko mijin ki ne

Allah maɗaukakin sarki yace لينفق ذوسعة من سعته

Kowa zaiyi ne gwargwadon hali da yassarewar da abin hannun da Allah Maɗaukakin Sarki ya bashi

Mu'amala ma ba'a yarda ayi Miki bisa muzanci ba,
Allah Madaukakin Sarki yace  وعاشروهن بالمعروف

KE ƊIN NAN  Ni Maryam Ayagi ina baki shawara ki nemi wannan Muhadaha da Malama Zainab Ja'afar tayi saboda kiji tagomashin da gatan da addinin Musulunci yai Miki da babu wani addini da yayiwa ƴa mace irin wannan gata

A karshe ina rokon Allah sakawa Malama da Alkhairy ya kara mata Albarkaaa ikhlasi da ilimi mai Albarka

101 QURAN STORIES AND DUAWhere stories live. Discover now