FAIDA DAGA ALQUR'ANI

2 0 0
                                    

FA’IDA DAGA AL-ƘUR’ANI…16

Allah s.w.a Ya ba mu labarin yadda babanmu Annabi Adam a.s da matar shi Hauwa’u suka kasance a Aljanna a farkon halittarsu, da yadda shaiɗan ya yi musu waswasi  har suka zakkewa abinda Allah Ya hane su;

((وَعَصَىٰٓ ءَادَمُ رَبَّهُۥ فَغَوَىٰ * ثُمَّ ٱجۡتَبَٰهُ رَبُّهُۥ فَتَابَ عَلَيۡهِ وَهَدَىٰ)) سورة طه، آية ١٢١-١٢٢
{Kuma Adamu ya saɓa wa Ubangijinsa ya bar shiriya * Sannan Ubangijinsa Ya zaɓe shi, sai Ya yafe masa Ya kuma shirye shi}. Suratu Ɗa-ha, aya ta 121-122.

Dubi yadda annabi Adamu a.s da Hauwa’u suka yi gaggawar tuba zuwa ga Allah a kan laifin da suka aikata wanda aka hane su da su yi, sun yadda cewa lallai su masu laifin ne kuma yafiyar Allah suke nema. Hakan ta sa Allah cikin rahamar Sa da gafarar Sa Ya yafe musu, har ma Ya ɗaukaka darajarsa Ya sanya shi cikin zaɓaɓɓunSa Ya kuma sake shiryar da shi.

Kar mu yi ƙasa a gwiwa wurin tuba na gaskiya ga Allah a kan laifukanmu, wannan shi ne halin babanmu Annabi Adamu a.s, don haka mu yi koyi da shi.

🖊Malama Zainab Ja’afar Mahmud
5th Rajab 1444A.H
27th January 2023

101 QURAN STORIES AND DUAWhere stories live. Discover now