page 2

19 0 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️

        *BEELAL*

     💦💦💦💦💦💦
         
  
                 NA

    MAMAN AFRAH

   FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

    Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai.Godiya da yabo sun tabbata ba Allah maɗaukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin.

*This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* 😍😍😍

       Page 3️⃣➡️4️⃣

.
   Cikin raunin zuciya da sagewar ƙafa jin furucin Beelal, na sanya hannu na tashe shi tsaye, tsayawa ya yi amma har lokacin hawaye na zuba a idanunsa da alama ma idanun a kumbure suke saboda kukan da ya yi.Rungume Beelal ɗin na yi a gefen hannun damana, hagun ɗin sai na rungume Hameeda ƙaran sheshshekar kukan da suke na taɓa min zuciya ji nake kamar in maida damuwar tasu cikin raina duk da na san yadda nake ji a raina ya linka yadda suke ji.Sai dai babu wani abu da zan iya yi a kai wanda ya wuce in lallashe su in basu haƙuri tare da addu'ar Allah ya kawo mana ƙarshen wannan hali da muke ciki da kuma ƙalubalen rayuwa da muke fuskanta tun da dukkan tsanani yana tare sa sauƙi babu wani dawwamammen abu daɗi ko wuya, duk masu wucewa ne.Haka na ja su muka shiga cikin gidan dan na san Hameeda ma babu inda za ta tafi har sai ta ga Beelal ya daina kukan dan duk lokacin da yake cikin ƙunci haka take kasancewa tare da mu har sai ta ga walwalarsa, al'amuran yarinyar tamkar wata babba haka take yin abubuwa ga sanin ya kamata.

Muna shiga cikin gidan na zaunar da su a kan tabarma na shiga lallashin su har sai da na ga sun saki ransu sannan na tafi domin in iza wutar da na ɗora abincin.

"Mama kin ga fa har takalminsa ya tsinke da ƴan makarantar suka biyomu" Muryar Hameeda ta katse min hura wutar da nake, ko ma in ce ta dawo da ni daga tunanin da na lula dan a zahiri ina hura wutar ne amma zuciyata tana can wani waje da ban, dan kuwa na tafi tunanin mahaɗin abincin da zan basu, domin kuwa ko ɗigon mai bani da shi a gidan bare yaji gishiri kawai nake da shi.Tsaye na miƙe daga sunkuyen da na yi ina fifita wutar da mafici na kama ƙugu tare sa sauke wata ajiyar zuciya na ce.

"Babu komai Hameeda zan san yadda za a yi"

"Za ki siya masa sabo" Ta ƙara jefo min tambaya.

"Idan Allah ya hore min zan siya masa idan kuma ban samu kuɗi ba zan baiwa mai gyaran takalmi ya gyara masa" Na ce ina maida kallona kan Beelal da ya yi tagumi da hannun hagun ɗinsa dan shi ne mai lafiyar, yana bin mu da ido.

"Ma...ma ki ba da ...aaaa ...gyara min na san baaaa...ki...da ku...kuɗi" Ya ƙarashe maganar cikin sanyin murya.

  Shiru na yi ina jin tausayin  Beelal na tsarga min saboda yaron akwai hankali idan ya yi wata maganar ma ba za ka taɓa tunanin yaro ne mai ƙarancin shekaru ya yi ba.

"Kawai ka bari idan ta samu kuɗin ta...

"Assalamu alaikum" Sallamar Umma Hafisa wato Ummar Hameeda ta katse maganar da Hameedar ke yi.

'Wa alaikumus salam" Na amsa ina ƙirƙiro murmushin yaƙe.

"To sarkin surutu kina nan kina ta zuba ko?' Ta faɗa lokacin da ta ƙaraso tsakar gidan.

"Umma ba fa zuba nake ba magana nake yi" Hameeda ta faɗa tana washe haƙora.

"To na ji dai, Beelal kuka ka yi ne?" Ta tambaya tana kafe Beelal ɗin da ido fuskarta na nuna alamun damuwa.

Default Title -BEELALWhere stories live. Discover now