BEELAL BOOK 1

15 1 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️

*BILAL*

💦💦💦💦💦💦💦

                NA

    MAMAN AFRAH

   FCW

    Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin.

*This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* 😍😍😍

Book 1

        Page1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣

   '''Beelal'''

   Tun yana kukan da iya ƙarfinsa har ya gaji ya yi shiru, sai ajiyar zuciya yake sauke wa a kai-a kai, ga yunwa da yake ji dan tun abincin da suka ci da safe kafin su taho bai ci komai ba gashi har la'asar ta wuce. Yana nan zaune a jikin bishiyar sai ya jingina bayansa yana hango wasu yara suna ta wasan guje-guje yana ta kalllon su  har dai bacci ya fara kaiwa idanunsa ziyara. Gyangyaɗi ya fara, yana yi yana ɗan zabura ya buɗe idanun har dai baccin ya ci ƙarfinsa ba tare da ya kwanta ba a zaunen yake kayansa. Wata tsohuwa ce da bishiyar da Beelal ke jikinya a ƙofar gidanta take, fitowarta kenan tana ƙoƙarin kulle gidan sai idnunta suka yi arba da Beelal da farko tsoro ya bata ganin tsananin kyan yaro amma da ta ƙarewa ƙafafunsa kallo ta ga ba kofaton aljannu sai ta ji tausayin yaron ya wani irin daki loko da saƙuna na zuciyarta, cikin sanɗa-sanɗa ta ƙarasa wurin da yake ta tsaya ta ƙare masa kallo tsaf a ranta ta ce.

"Iko sai Allah, haƙiƙa ubangiji ba ya haɗa maka komai kuma ɗan adam tara yake bai cika goma  ba. Duk irin kyau da yaron yake da shi amma kuma cikin iko da ƙudura ta lilllahi sai yaron ya zamana nakasashshe. Ba komai ya ƙara mata tausayinsa ba sai ganin yana bacci a zaune kuma fuskarsa da jurwayen hawaye gashin idanunsa a jiƙe da alama dai kuka ya gama kafin baccin ya ɗaukeshi.

Da Bismillah ɗauke a bakinta ta sanya hannu ta dafa kafaɗarsa tare da ɗan jijjigawa, firgigit Beelal ɗin ya yi amma sai bai buɗe idon ba da yake baccin ya ci ƙarfinsa  ne, ɗan ƙara jijjigashi ta yi aikuwa yana buɗe idonsa ya sauke su a kan tsohuwar nan kallonta kawai yake irin na rashin sani, kana ganinsa kuma ka san a tsorace yake da ita dan gani yake cutar da shi za ta yi tun da bai san ta ba.


"Yaro ya sunanka? Kuma ina ne gidanku?" Cewar tsohuwar har lokacin tana duƙe a kan sa.

  Shiru ya yi yana ta kallonta.

"Za ka iya gane gidanku? Dan na ga ban san ka a nan unguwar ba dan duk yawanci yaran wajen nan duk na san su. Beelal dai bai ce mata uffan ba har lokacin.

  "Ko dai yaron nan kurma ne" Ta faɗi hakan a zuciyarta.

  "Akwai karnuka a wajen nan kuma ka ga an fara kiran magriba duhu zai shiga ka tashi ka tafi gidanku ka ji sabo...

  Ai jin ta ambaci kare Beelal ya zabura da sauri ya tashi tsaye har yana neman faɗuwa, dariya ce ta so ƙwacewa tsohuwar ashe yana gani shegantaka ce kawai.

  "Ni, ni, ni suna na Beelal" Ya faɗa cikin in'innarsa, tausayin sa ne ya kama tsohuwar jin in'innar da yake a magana to ko hakane ya sa ba ya son yin magana saboda wahala wajen furtawa.

  "Beelal sunanka?"

Kai kawai ya gyaɗa mata, yana ta waige-waige da alamar tsoro a fuskarsa, ta san hakan bai rasa nasaba d karnukan da ta ambata.

Default Title -BEELALWhere stories live. Discover now