BEELAL BOOK 1

16 0 0
                                    

❤️❤️❤️❤️❤️❤️

*BILAL*

💦💦💦💦💦💦💦

                NA

    MAMAN AFRAH

   FCW

    Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai.Godiya da yabo sun tabbata ga Allah maɗaukaki da ya bani ikon fara wannan littafi Allah bani ikon kammalawa cikin aminci amin.

*This book from the beginning to the end is a dedication to BEELAL YUSUF MUHAMMAD May God bless us and bless our lives with all Muslim children.I love you my child so much* 😍😍😍

Book 1

        Page1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣

  "Ina suka tafi mini da ɗana, ina suka kai shi?" Cewar Fatima cikin muryar kuka dan jin Hajiya Laɗifa na cewa an tafi da Beelal sai ta warce wayar daga hannun Yayarta ta.

"Dan Allah ki yi haƙuri, ni kaina ban san inda suka kai shi ba, kawai dai Alhajin ya ce musu su fitar da shi daga unguwar to yanzu sun ma daɗe da dawowa daga kai shin" Ya faɗa cikin sanyin murya jin yadda Fatimar ke kuka da kuma yadda rauninta ya bayyana a muryarta za ka fahimci hakan. Sakin wayar Fatima ta yi ta cigaba da cewa

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un Allahuɓma ajirni fi musibati waklifni kairan minha"

  Cikin sauri Hajiya Laɗifa ta ɗauki wayar,  Nasira kuma sai ta yi ka Fatima da ta ga ta yi tangal-tangal za ta faɗi, tana ƙarasawa kuwa kamar jira Fatima take ta tafi za ta faɗi Nasirar ta tare ta sai kuwa ta faɗa jikin Nasirar yif a sume.

   Hajiya Laɗifa gabaɗaya abu ya taru ya mata yawa hakan ya sanya ta yi ta maza ta danne kukan da ya taho mata dan ganin ƙanwarta tilo babu numfashi Nasira ta jijjigata da kiran sunanta hakan ya bala'in ɗaga mata hankali. Tana tsoron ta rasa ƴar uwarta da ta shaƙu da ita, a gefe ɗaya kuma ga tunanin yadda za a tafi neman  Beelal yaron da ba cikakkiyar lafiya ba gareshi ta san ko da a ce za a taimakashi ne to fa ba kowa ne zai taimakeshi ba saboda nakasar da ke tare da shi, dan wani gudun wahala da ɗawainiya ma ba zai bari ya taimaka masa ba, bare yanzu ma a wannan zamanin da kowa ke ta kansa saboda hali da matsi na rayuwa iyalin mutum ma da yaya bare kuma ya ɗauki ɗawainiyar bare, ba ma wannan ba shin wane loko da saƙo za a tafi neman Beelal? Waye ma zai tafi neman nasa? Ta ina ma za a fara nemansa? Tabbas neman mutum a gari mai girma kamar gari Kano ba abu bane mai sauƙi, cikin wannan saƙe-saƙen da zuciyarta ke mata ta tsinkayo maganar Mai tsaron ƙofa ta cikin wayar yana cewa "Hajiya bakya ji na ne?"
  Hannu ta fara kaiwa ta share hawayen nata kafin ta ce "Mai tsaron ƙofa ina suka kai mana Beelal? Shin ka san ya Beelal yake a wurinmu?" Ta sake jefa masa wata tambayar ba tare da ta jira ya bata amsar tambayarta ta farko ba.

  "Hajiya babu yadda zan yi ne, Allah ne ma fa ya taimaka da yaron nan bai bayyana cewa mahaifiyarsa na cikin gidan nan ba"

"To ai wallahi gwara ya faɗi cewa mahaifiyarsa na cikin gidan nan, in ya so a mana duk abin da za a mana a ƙarshe dai na san bai wuce aurena ya mutu ba, a kan a ce an jefar da Beelal babu ta inda muke da tabbas ɗin samun yaron nan" Ta faɗa hawaye na zubo mata.

  Ajiyar zuciya Mai tsaron ƙofa ya sauke, jin muryar Hajiya Laɗifa ya san kuka ita ma take sannan ya ji lokacin da Nasira ke kiran sunan Fatima tana kuka tana ambaton ba ta numfashi, tabbas ya kamata ya yi wani abu a kai a matsayinsa na namiji dan su duk mata ne mata kuma akwai su da rauni ga zuciyarsa ta kasa barshi ya yi sukuni da tunanin Beelal saboda tana tariyo masa kukansa a lokacin da za a ɗaukeshi yana jin lokacin da yake cewa

"Jakar kayanmu, ku barni na ɗauki jarkarmu" Amma ko sauraron yaron basu yi ba suka sanyashi a mota.

 

Default Title -BEELALWhere stories live. Discover now