1

133 13 2
                                    

*********************

TAKAICIN UBA......📝📝📝

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Na

Nazeefah Sabo Nashe..

Daga k'ungiyar Elegant Online ✍🏽

Arewa books
@nazeefah.

Wattpad
@Nazeefah381.

08033748387.

(Alhamdulillah cikin hukuncin ubangiji na sake zuwa muku da wani sabon littafi masoyana, da nake fatan ya faranta muku fiye da na baya a kullum da ku nake alfahari. Ina sake mik'a godiya ta gareku dafatan Allah ya karb'i ibadunmu.)

Daga alk'alamin marubuciyar

Me Zan yi da ita?

Da

Ya abin yake?

Mafari.................

******************************

Page 1

A zafafe ta fito daga office d'in Cikin sauri tamkar zata tashi sama. Da sassarfa sosai ta isa wajen tarin jerin motocin da suke fake a parking lot d'in da yake ma'aikatar. Ba tare da damuwa ba suke ta darewa suna bata hanya don ba sabon abu bane a wajensu  a tarin lokuta suna yawan ganinta a haka, cikin wannan yanayin mai firgitarwa. Sai da ta tattare zumbulelen bak'in hijab d'inta da ya zame mata tamkar uniform saboda duk wanda ya san AYRA GAYA da wannan shigar ta dogon black hijab mai jan k'asa ya santa, da kuma black nik'ab. Da wuya a samu mutumin da ya san zallar kamannin na AYRA GAYA in dai ba makusancinta ba shak'ik'i ko kuma daga cikin y'an uwanta sai kuwa abokanta na makarantun primary da secondary da wanda ya santa shekaru goman baya da suka wuce, don na jami'a ma d'aid'aikune suka san zallar kamannin na AYRA GAYA.

Da zafin nama sosai ta finciki kan motor,  haka yanayinta yake komai a zafafe take yinsa tamkar namiji so take lallai sai ta maye wa mahaifiyarta haushin rashin haihuwar d'a namijin da ake cewa ba ta yi ba. A gareta duk abinda wani d'a namiji zai aikata za ta aikata irinsa koma kai tsaye ta bugi k'irji ta ce zata aikata wanda ya fi shi. Ta fi yarda da cewa What Man can do woman can do better, fiye da what Man can do woman can do. Duk wanda yake cikin ma'aikatar bin ta suka yi da kallo suna tabbatarwa da kan su cewa yau ciwon AYRA ya motsa don sun fi danganta ta da mai cutar jinnu ko tab'in hankali saboda yanayin yarda take mu'amalantar mutane halayenta gaba d'aya ya farrak'a da na mutane sai dai masu shafar jinnu. Yanzu zaka ganta da sanyin hali anjima kaga ta murd'e ta zama wata iriyar mace mai bak'ar zuciya mai zafi da saurin fushi.

Ta ko ina take jefa motar har zuwa sanda Allah ya kawota unguwar Rail way inda anan ne suka tanfatsawa mahaifiyarsu gida ita da y'an uwanta su hud'u har ita cikon ta biyar d'in kafataninsu zallar mata.

Horn d'in da ta dinga dannawa Mai gadin a zafafe ne ya tabbatar masa da cewa yau Uwar d'akin nasa ba lafiya ba, don da lafiya take idan ta yi sau biyu bai zo ya bud'e ba da kanta take zuwa ta tura gate d'in ta kan ce masa "Yi zamanka Baba na san hutawa kake bana son katsewa mutum hutunsa musamman idan barci ya d'aukeshi balle kai da shekaru sun ja."

Yau kam ya san tunda take wannan gigitaccen horn d'in ya tabbata aljannun uwar d'akin nasa sun motsa. Sai da ya ja Innahu min sulaimanu sannan ya bud'e gate d'in abinda ya ke zargi ya tabbata domin dai ko glass d'in motar bata sauke ba balle ya saka ran samun gaisuwa kamar yarda duk ta saba idan tana cikin sukunin zuciya da walwala. Madadin haka ambaleshi da iska ta yi a zafafe ta kai kanta ma'ajiyar motocin gidan.

Da k'arfi ta tura k'ofar da zata shigar da kai ainahin harabar tsakargidan kafin shiga main parlour na gidan. Tun a waje dama ta shaida zuwan y'an uwanta ganin motocinsu duka a wajen.
Ta sani sun zo don su d'aga mata hankali kamar yarda suka saba su saka mahaifiyarta ta kwana tana mata mita akan rashin aurenta kamar a kansu take zaune. Kafin ta shiga sai da ta tuge nik'ab d'in da yake fuskarta sannan ta tura k'ofar. Ga hasashenta kuwa suna zaune zagaye da mahaifiyarsu, yaransu a gefe suma.
Hutun makaranta ake ta san shi yasa suka zo da su.

Takaicin UbaWhere stories live. Discover now