TAKAICIN UBA...
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
Page 7.....
Da tsananin takaici Amma ta dinga bin Ayra da kallo, tana mamakin irin fetsarewar idanunta da har take fad'awa Hameeda hakan. Idanunta su suka rusunar da nata idanun da suka yi tsaitsaye kan Ummin. Hankalinta ya tashi matuk'a don ta dad'e bata ga Amma a cikin wannan yanayin ba na matsanancin b'acin rai. "Durk'usa ki bata hak'uri ki kuma b'ace min da gani, wani irin abu ki ka aikata haka? Ce miki aka yi tilas za 'a yi a miki auren?"
Idanunta ne kawai suke zubar da k'wallar ta zube a gaban Ummin harshenta na rawa ta ce "Ki yi hak'uri, I don't meant to hurt you." Ummin ta saki ajiyar zuciya tana d'aga mata kai, sam abinda Ayran ta yi bai girgiza ta ba, Amin yana yin wanda yafi wannan idan aka bijiro masa da maganar aure, abinda take so ta gane mai ya janyowa Ayran wannan matsanancin k'iyayyar auren, daga maganar tun ba a aiwatar ba ta shiga cikin irin wannan yanayin to ina ga ance an d'aura mata auren ba bisa ra'ayinta ba, tabbas akwai k'ura. Murya a sanyaye ta ce "Ta shi ki je Ayra, Allah ya shige mana gaba." Ta mik'e tamkar wacce k'wai ya fashewa a ciki, gaba d'aya haushin Ummeey ya gama dabaibaye zuciyarta gani take kamar tana shirin rusa mata farin cikinta ne. Ko da ta hau sama bata koma d'akinta ba don bata buk'atar hayaniyar twins direct d'akin Amma ta shige ta kullo har da murza key. Tana buk'atar kad'aicewa don samun sauk'i daga rad'ad'in da k'irjinta yake mata.Hameeda na ganin ta gama hawa Stair case d'in ta mayar da kallonta a kan Amma da kanta yake a sunkuye. Tsam ta mik'e ta dawo kusa da ita ta sake kama hannayenta a karo na biyu ta ce "nuna b'acin ranki ba shi zai kawo warwarar matsalar yarinyar nan ba, anya kuwa babu jinnu a cikin lamarinta?" Amma ta k'ura mata ido kafin ta girgiza kai murya a sanyaye ta ce "Babu wani jinnu a cikin lamarinta, illa TAKAICIN UBA da ya gigita tunaninta ya kuma saka mata tsanar maza had'e da jingina musu suna d'aya.." Amman ta fad'a wannan karan muryarta sosai ta karye ta shiga zubar da hawaye "Mahaifinta shi ya kambama tsanar maza a zuciyarta tun tana da k'uruciyarta har ta tashi da abin a ranta, ni kuma na yi sake da na barta har yanzu ban aurar da ita ba, na bar zuciyarta a kan wancan tunanin da zaton wata rana zata fuskanci ba haka bane. Na yi nadamar hakan da na sani tunda k'ank'antar shekaru na aurar da ita, ni kuma tausayinta ne ya rinjaye ni, na fi tausayinta k'warai da gaske fiye da y'an uwanta ko don k'addarar tafi girma a kanta fiye da su."
Shiru Hameedah ta yi tana son tambayarta wacce k'addara ce amma bata fiye son k'ure mutum ba, da ta so da kanta zata fad'a mata ba sai ta tambayeta ba. Madadin yi mata kutse cikin sirrinta sai ta kawar da wancan zancen ta sako wani "Da zaki amince da na ce miki matsalar Ayra koma wace iri ce ta zo k'arshe, ki amince a wannan karan kuma ki jajirce ki bani had'in kai mu had'a aurennan da sonta ko ba son ranta na san In sha Allah babu abinda zai faru sai alheri."
Shiru Amma ta yi tana son ta bada goyon baya, tana tsoron tashin hankalin Ayran wanda bata san mai zata aikata ba, kada ta je zancen da take ya tabbata na kisan kanta a duk yayin da ta bud'i ido ta ganta a gidan aure, don haka ta kasa amincewa Ummeey illa jinginar da kanta da ta yi jikin kujera ta lumshe idanunta a hankali ta ce "Ki bani lokaci na yi shawara, koma me kenan In sha Allah za ki ji." Ummeey ta saki hannayenta had'e da cewa "Allah yasa mu ji alheri ki yi addu'a sosai nima zan yi." Ta d'aga mata kai. Ummeeyn ta mik'e tana cewa "Bari mu tafi mun ja lokaci da yawa dafatan kema zaki kawo min ziyara kuma don Allah shawarar taki kada ta d'au lokaci." Amman tana kallonta ta ce "Yanzu kina nufin har mun gama hirar yaushe gamo? Haba Hameedah? Tun muna y'an mata fa rabon da mu had'u, baki tambayeni wa na aura ba wanene uban yara na? Baki tambayeni ya rayuwata ta cigaba da tafiya ba bayan kin tafi kin bar ni cikin matsaloli ba?" Hameeda ta sake zama had'e da dafata ta ce "Ni kaina ina son jin labarin bayan rabuwa, amma kada ki manta na sanar dake jiya na shigo k'asar nan ina da gidajen zuwa da yawa baya ga haka kuma naga alama akwai damuwa sosai a tare da ke bana son tuno miki da waccan bak'ar rayuwar, abu d'aya da zan tambayeki an ga dangin Innah bayan tafiyata? Don na san har ta rasu ba ki san kowa nata ba." Amma ta runtse ido sosai kafin ta ce "Ba'a gansu ba, har yau ko b'urb'ushinsu ban gani ba, na yarda tawa k'addarar kenan dafatan Allah ya had'amu a darussalam." Hameeda tausayi k'arara ya sake bayyana a fuskarta ta ce "Allah ya gafartawa Innah, ki yi hak'uri zan dawo In sha Allah ko kuma na ce sai kin zo. Ki gaida Kabiru tunda na samu labarin shi kika aura na yi bak'in ciki sosai amma da na tuna shine k'addararki sai na yi miki fatan nasara a rayuwa ki sanar masa Hameedah Daru ta zo." Amma ta saki wata ajiyar zuciya kafin ta ce "Rabona da Kabiru da Auren Kabiru shekara Ashirin kenan cif, ke dai labari sai mun had'u." Daga haka ta hau sama don kiran twins. Ta bar Ummeey da sakakken baki da ta'ajibin abinda kunnuwanta suke jiye mata, shin wace irin k'addarace ta raba Talatu da Kabirunta duk da dama ta san ba soyayyar sa a zuciyatta? Me ya faru haka? Bata dawo daga tunanin ba taga sun dawo da y'an biyu gaba d'aya hannayensu d'auke da manyan ledodi shak'e da sutturu na alfarma. Jikinta a sanyaye ta dinga bin Amma da ido ji take kamar ta zauna ta fasa tafiyar Amman ta bata labarin bayan rabuwa. Sai dai kuma bata son k'ure mutum akwai lokaci......
Koda ta dawo daga rakasu bata bi ta kan Ayra ba, ta shige kitchen ta cigaba da ayyukanta da Dane damun kanta zata yi har sai Ayran ta bud'e d'akin ta lallasheta, yanzu kuwa tana murd'a d'akin ta ji shi a rufe ta juya abinta ya zama dole ta nunawa Ayra lokaci yazo da ya kamata ta zubar da makaman yak'inta ta yi aure, sai dai tana tsoro k'warai da gaske ta ke tsoron barazanar da Ayran ta yi akan rasa rayuwarta idan aka mata auren dole.
Sai dare can bayan Isha sannan Ayran ta fito jikinta a sanyaye ganin yarda Amma ta banzatar da lamarinta. A falo ta samu Amman tana kallon wani sabon shiri da ake a Arewa ta zauna kusa da ita, amma Amman ko kallonta ba ta yi ba illa ma sake mayar da hankalinta kan television d'in, duk da rabin tunaninta dama yana kan Ayran ta kuma ji dad'i da ta ga ta fito sumul k'alau ba abinda ya sameta.
Jikin Ayra a sanyaye ta ce "Sannu Amma." "Yauwa" kawai Amman ta ce ta cigaba da jan carbinta ba tare da ta sake bi ta kan Ayran ba. Take hawaye ya yankewa Ayran a idanu ta sake jin tsanar Ummeey a ranta da duk ita ta janyo mata wannan matsalar. "Kada ki saka ni gaba da kukan jin da'di ban hanaki Kukanki ba amma ki koma cikin 'dakinki, don ban ga abinda aka miki ba, aure ne ba kya so to falillahil Hamdu, sai ki tanadi amsar da za ki bawa ubangiji sakamakon b'ata min rai da kika yi." Hankalin Ayra ya sake k'ololuwar tashi ta tabbata yau ta kai Amma tik'ewa, ina ma zata iya da ta yi shahada ta amince da auren ko da na wuncin gadi ne, ba zata iya ba tana jin zuciyarta zata fashe a duk ranar da ta had'a makwanci d'aya da 'da namiji balle ta kai g ya kusanceta. Ta runtse idanunta tana ganin abin kamar ma ya faru, zuciyarta ta dinga bugu kuka sosai ya kece mata, da sauri ta 'dora kanta a saman cinyar Amman tana kuka na gigitar hankali. Duk dan ta yi nasarar 'daga hankalin Amman sai dai bata nuna mata ba, ta dai cigaba da kallonta tana jin tausayinta yana tsirga mata sosai, a hankali ta cigaba da jan addu'oi a bakinta da niyyar Allah ya sauk'ak'awa Ayran ta samu sauk'in zuciya. So take ta rarrasheta amma tana gudun aikata hakan, gani take kamar wannan hanyar data b'ullo shi zai saka Ayra ta amince ta yi auren ko bata so. Kukan sosai ta yi kafin ta share hawayenta ta mik'e a sanyaye karo na farko a rayuwarta da take kuka a gaban Amma bata rarrasheta ba abinda ya ki'dimata kenan a sanyaye ta koma kan kujera ta lafe, ba zata iya cin abinci ba duk da yunwar da take sasik'ar hanjinta. Amman ta bita da kallo kafin cikin k'arfin hali ta sake d'auke kanta ta cigaba da jan Addu'oin da suke bakinta.********************************
A bakin faffad'an windown mai d'auke da glass mai girman gaske yake tsaye hannayensa sanye cikin aljihun jibgegiyar rigar sanyinsa, don garin canada akwai muku-mukun sanyin da har dusar k'ank'ara yake zubarwa (Snow). Sanyin yake ji sosai sai dai ya kasa barin wajen windown duk da windown ba'a bud'e yake ba. Yana tsaye yana hango yarda ko ina ya lullub'e da dusar k'ank'ara kamar ma ba'a halicci k'asa a wajen ba. Ya saki ajiyar zuciya tunawa da ya yi marigayiyar matarsa ta fi k'aunar yanayin fiye da komai, saboda yarda take kanainaye jikinta a nasa kamar mage. Ya lumshe ido a hankali ya ambaci sunanta a saman lab'bansa "Hibbah!" yana jin tamkar ta amsa cikin duhun idanunsa yake hango fuskarta tana sakar masa kyakykyawan murmushin da yafi so daga gareta. Ya da'de idanun a lumshe yana tuno memories d'in su masu da'di da suka kasa barin kwanyar kansa. A hankali ya bu'de idanunsa da ya ji sun masa nauyi kamar 'dan maye wani feeling na muguwar sha'awa na taso masa. Yanayin da ya da'de bai riski kansa a cikinsa ba tun bayan aurensa na uku da Lubna ta ribace shi ta saka masa desired tablet a cikin coffee 'din da ya saba sha duk dare. Tabbas ranar ta samu kansa domin kuwa kasa mallakar kansa ya yi sai da ya kusanceta sai dai abin haushin ya tarar da ita fanko ma'ana bata kawo budurcinta ba, kamar dai wancan Auren da yayi na Sa'eeda itama fankon ya tarar da ita shikkenan ya saka wa kansa cewa duka y'an matan yanzu hakan suke, ai kuwa ta jawowa kanta daga ranar ya saketa yana takaicin ha'da jikinsa da nata da ya yi.
Da sauri ya fa'da toilet baya son yanayin ya cigaba da zagaye jikinsa yazo yana rasa inda zai saka tsananin buk'atarsa. Ruwa sosai ya sakarwa kansa kafin ya fito ya zari car key 'dinsa ya fice daga gidan bayan ya gama k'arewa hotonsu da Hibba kallo.