9

85 5 0
                                    

TAKAICIN UBA.......

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.



8....

Driving yake yana sauraron Karatun Alkur'ani daga k'ira'ar sudais. Shi ka'dai ne abinda yake saurare ya rage masa zugi da ra'da'din rashin Hibbarsa. Ko da ya yi parking a makeken wajen shak'atawar kasa shiga ya yi ya shiga cusa hannayensa cikin tarin sumar gashin kansa da ya gadota daga gurin Ummeeynsa. Ya dinga cukuikuye gashin yana jin kansa na sara masa kafin ya mayar da seat 'din kujerar ta sa ya koma ya kwanta tunanin rayuwarsu da Hibba na sake bujiro masa....

K'arar da wayarsa ta yi ne ya farkar da shi daga wancan tunanin, ba sai ya kalli screen 'din wayar ba ring tone 'din ya sanar da shi wacece 'Ummeey' ya fa'da yana sakin murmushin gefen kumatu kafin ya jawo wayar ya kanga a kunnensa. Cikin muryar shagwab'a kamar yarda ya saba mata magana ya ce "Hayateey!" Ummeey daga 'daya gefen ta saki murmushi tana jin da'din sunan da yake kiranta da shi. "Amin ya gida hope dai kana lafiya, muma kwanan mu uku a Nigeria." Ya 'dan yi dum da waya a kunne kafin ya ce "Nigeria kuma how comes? Ya aka yi Abeey ya barku kuka je?" Dariya ta yi sosai kafin ta ce "Da kansa ya sauko ya ce mu je. Yauwa ba wannan yasa na kira ka ba, Amin bu'de kunne da kyau ka ji lokaci ya yi da ya kamata ka yi aure." Wani irin dum ya ji k'irjinsa ya buga, Ummeey zata sake janyo masa wani jidalin kenan shi tun yaushe ya cire maganar aure a rayuwarsa, ya Riga ya gama da wannan babin an gama samun mata na gari tun bayan da Hibba ta rasu. "Ba ka ji ni ba ne?" Ummeey 'din ta fa'da with a serious tone. Sakin ajiyar zuciya ya yi kafin ya ce "Na ji Ummeey, amma ina neman alfarma, not now please, wallahi ban shirya aure ba, ko kuma na ce na gama buk'atarsa a rayuwata tunda dai Hibba ta haifa min mai yi min addu'a." Cikin b'acin rai Ummeey ta ce "Ko da nice nake so?" Muryarsa a cunkushe ya ce "Don Allah Ummeey a bar maganar, please!"

"Ka yi k'arya kuwa in bar maganar aure, haka kawai da ranka da lafiyarka in dai ba mu'amala kake da matan banza ba ai ya kamata ace zuwa yanzu ka ajiye iyali, don haka magana 'Daya da zan maka na samar maka mata y'ar aminiyata ta yarinta da nake yawan baku labarinta wato TALATU, don haka umarni na baka ba shawara ba.." kafin ya ce komai ta katse wayar don ta san idan ba haka ta yi masa ba,
Ba zai 'd'au zancen serious ba.

Gaba 'daya ji ya yi zuciyarsa ta karye, ya tabbatar tunda ta fa'da 'din sai ta cika alk'awarinta. Ya runtse idonsa yana tunanin menene mafita? Wannan karan kam ya zama dole ya bijirewa umarninta, shi kam da zata bar shi haka ma tsaf zai iya rayuwarsa har ya koma ga lillahi babu aure. Wajen shak'atarwa da bai shiga ba kenan, ya da'de a zaune a motar kafin ya ja motar da sauri ya fice daga garden 'din.


____________

Tun Asuba da ta mik'e bata farka ba, ta shiga gyaran gidan da abincin da ta san Amma ta fiso, gurasar larabawa da alkubus sai kunu da k'osai. May be idan Amman ta ga wannan hidimar da ta mata ta sassautawa zuciyarta daga fushin da ta tsiri yi da ita tun jiya da bak'uwarta da ta kira bak'ar bak'uwa ta zo gidan.

Sai da ta jera kayan akan dinning table da taimakon mai aiki. Sannan ta kunna sunnah t.v tashar da ta san Amman ta fi muradin kallo a koda yaushe.

Tsaf ta fito cikin shigar alfarma. Ta dinga bin falon gidan da kallo ganin yarda aka canja masa tsari. Ga dadda'dan k'amshi da aka baje falon da shi, na abinci da na k'amsashshen turaren wuta mai sanyaya ruhi na mutanen chad. Murmushi ne ya so sub'uce mata sanin cewa Ayra ce duk ta shirya hakan sarai ta san neman sulhu take tun jiyan tana lura da ita fushin da take da ita yana damun zuciyarta, sai dai ba zata bari ta fuskanta ba.

Ta zauna tana sake addu'ar fatan alheri ga Ayran kamar yarda ta kwana tana yi a cikin sujuda, ji take kamar warwarar matsalar Ayran ce ta zo. Ita kanta ta ji tana son Ayran ta yi wannan auren ko da sonta ko ba son ranta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 25, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Takaicin UbaWhere stories live. Discover now