Takaicin Uba.....
Na
Nazeefah Sabo Nashe
08033748387.
3...
Littafin Takaicin Uba.. paid book ne, 500 ne kacal ga masu buk'atar karanta shi za su iya biyan ku'din su ta wannan account 'din a saka su a paid group..2118666253 U B A.
Akwai kuma special people masu son a bisu har gida a tura musu privately ba ruwansu da hanyaniyar group, ko turo min inda aka wuce ni a kullum aka yi posting zan tura musu privately. Ku biya 1k kacal.
Sai masu turawa groups 'din su ku kuma ku biyo ni gida mu yi ciniki. Kada ku manta littafin mai zafi ne fiye da ME ZAN YI DA ITA? Da YA ABIN YAKE?
Sai na jiku pages 12 ne kacal free pages.
—————————
Ko a wajen rakiyar da Amman ta musu, kashedin da Amman ta sake musu mai tsauri ne, don yau kam Ayra ta gigita tunaninta gani take a condition d'in da ta tarar da ita tsaf zata kashe kan nata. Ta sake jaddada kashedinta ga Zainab musamman kasancewar ta fi su tsaurara lamarin.Zainab ajiyar zuciya kawai take saki don dai ita da za'a bi ta tata da Tuni Ayra ta dad'e a d'akin miji gani take duka zancen kisan da take rainin hankaline don ta ga suna biye mata ne. A tunaninta wancan kuskuren mahaifin nasu bai zama dalilin da zai rinjayi zuciyarta ta gicciyar da lamarin aure lokaci guda ba. Ta d'auke kanta bayan ta tabbatar wa da mahaifiyarsu ba zata sake tsoma baki game da lamarin Ayran ba sai dai tana rok'on Ubangiji ya ganar da su abinda ita tuni ta dad'e da ganewa. Bata wani jima a wajen ba ta ja tawagar yaranta ta bar gidan ranta a matuk'ar b'ace don idan ta zauna tabbas duk wanda ya takaleta zata iya sauke takaicinta a kansa.
Ko a mota mitar da take kenan sai da Babbar y'arta ta dinga tausar zuciyarta kafin ta samu ta lafa daga b'acin ran da take ciki.___________
Da wani irin farin ciki ta tashi da safiyar kashegarin ranar da abin ya faru. Zuciyarta wasai ta tabbata a yanzu ko da ganganci babu mai sake mata maganar aure tunda Amma ta Riga ta gindaya sharad'i mai zafi game da lamarin auren. Ta sani sarai suna shakkar mahaifiyarsu ba sa son bijirowar b'acin ranta ko misk'ala zarratin.
A tsaye take a gaban mudubi tana sake cancad'awa fuskarta kyakykyawan make up. Da ya sake bayyana wani irin sihirtaccen kyanta ko ba ta yi kwalliya ba dama mai kyau ce balle ita ma'abociyar son kwalliya ce da duk wani k'yalek'yale. Eyelashes d'inta ta sake bi da mascara ta tusa musamman kasancewar su zara-zara kamar na kanti sai dai nata ne daga Indallahi (naturally). Kyakykyawan lips d'inta ta gogawa pink lipstick sai ya sake bayyana tsananin kyanta ta d'aura d'ankwalin black material da yake jikinta sai dai bai b'oye zara-Zaran gashin da suke kwance luf-luf a gaban goshinta ba. Ta d'an fesa turarenta mai matuk'ar k'amshi da tsada na kamfanin lulu. Sannan ta d'au gogaggen hijabinta bak'i sid'ik wanda ya zame mata gado ta ratayashi da nik'ab da hand bag d'inta ta fice Falon gidan.
Kamar kowace safiya gidan an gyarashi tsaf da taimakonta da na mai aikinsu sai baza k'amshin turaren sandal wood yake mai asalin k'amshi. Saman Dinning ta zauna tana had'a coffee ga al'adarta duk safiya sai ta sha coffee kafin ta ci komai, musamman kasancewrta ma'abociyar k'in abinci tsakaninta da abinci akwai gaba mai girman gaske. Ta zari salted biscuit guda biyu ta fara sha da coffee d'in.
Amma ta bi hannunta da kallo "Yau ba zaki ci ko chips d'in ba, sarkin k'in cin abinci." Girgiza kai ta yi tana cuno bakinta "Wallahi Ammaty yau Abincin nan ba zai samu shiga ba, wannan ma is okey idan na ci abincin ba zan iya hassala komai a office ba, kuma ina da aiki mai tarin yawa." Amma ta girgiza kai "Madalla da Agogo sarkin aiki shi yasa ga ki nan kullum jiya I yau." Mik'ewa ta yi tana tuntsira dariya cikin farin ciki ta rungumi Amman kafin ta zura hijab d'inta da nik'ab ta kuma zurmuk'a hannayenta a aljihu ta sake rungumar Amman murya k'asa ta ce "Amma yau may be zan iya kaiwa past 4:00 saboda muna da meeting." Amma ta matsa hannayenta tana murzasu kad'an-kad'an cikin kulawa ta ce "Allah ya yiwa nemanki albarka Auta. Ya tabbatar min da ke kan tafarkin sirad'il mustak'eema." Feck ta bata a kumatu ta fice da d'an hanzari ganin 7;30 tuni ta wuce Amma ta sake Binta da wasu addu'oin a zuciyarta "Ubangiji ya yaye miki wancan tunanin a zuciyarki, ya kawo miki mijin aure na gari da zaki goge tabon k'iyayyar maza a zuciyarki, har ki furta da kanki wata rana MAZAN SUNA SUKA TARA." Irin Addu'oin da Amman take Bin ta da su kullum kenan a cikin sallolinta guda biyar. Ta tabbatar kuma Allah yana jinta abubuwan duka za su wuce da ikon Rabbi sai dai jinkiri. Kowanene Mijin Ayra? Shine tambayar da kullum takewa kanta take kuma burin ganin Mijin Ayran kafin a kaita kushewa.