4

24 3 0
                                    

TAKAICIN UBA...

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

https://arewabooks.com/book?id=6455383e1c910f5cf9785c27

(Kada fa ki bari a yi tafiyar nan ba ke! Takaicin Uba yanzu aka fara wani irin mur'dadden labari ne mai sanya tausayi takaici ga uwa ba tsantsar k'iyayyar da take juyewa ta koma makauniyar soyayya. Kun sani sarai bana kawo muku labaran banza.
Za'a sha dariya, Za'a goge hawaye duka a cikin labarin.

Zai zo muku Akan 500 kacal.

Sai special people manyan matan nan masu aji da ba sa son hayaniyar group, suna kan kujerar su za'a tura musu har cikin wayarsu ba ruwansu da an tsere min turo min. Za su biya 1k kacal duk da Naga Akwai Hajiyoyin gimbiyoyin mazajensu da suke tura min yafi haka. Tabbas gaisuwar ku daban ce.. samba'do ku'dinki ta wannan account 'din 2118666253 U BA..
Y'ar mutan makwarari ke cewa Marhababikum Lale Lale ana uhibbukum billah 😊😊😊❤️

4_____________


Da walwala sosai a fuskarta take duban sakatariyar tata duk da bata ganin fuskarta amma a muryar shugabar tata ta fahimci tarin farin cikin labarin da ta zo mata da shi, na zuwan bak'uwar da ta dad'e tana tsimayin zuwanta. Aminiyartace sosai da karatu ya farrak'a su shekarun da suka wuce ita ta koma rayuwar egypt  saboda admission da ta samu a can, yanzu ma hutu ta zo don ta samu aikin koyarwa a can egypt d'in.

Tunda ta mata waya zata zo take cikin murna da zakwad'i da son ganin aminyar tata Saboda tsawon lokacin da ta d'auka bata ganta ba. 

Saleemah Sa'ad ta shigo cikin wata irin k'Saitacciyar shiga, fuskarta d'auke da matsanancin murmushi tana bin office d'in AYRA GAYA da kallo. Shigar da take jikin Ayran ce ta sa ta ware ido tana kallonta so take ta ga fuskar Ayran da nik'abi ya mata shamaki. Da hanzari Ayran ta tuje nik'abin fuskarta ganin sakatariyar ta ta ta fita cikin farin ciki da murna ta isa wajen Saleema ta kai mata kyakykyawar runguma. Salima ma murmushi take tana sake duban Ayran da ta k'ara wani irin fitinannen kyau fatarta sai kace glass don taushi da sulb'i. Sai dai yanayin shigarta ya bawa Salima mamaki. Ayra dai Ayra da ta sani y'ar gayu mai yawan saka English wears sanda suna secondary school ita ce sanye da wannan shigar me ya faru? Me ya mayar mata da Ayra haka? Bata yarda ta zauna ba har sai da ta cillawa Ayran tambaya "Malama yaushe kika yi aure ban sani ba? Kuma wani rik'akken Malamin kika aura da ya mayar da ke haka?"

Ayra ta saki murmushi tana jan hannun Salima,suka zauna a kan katafariyar kujerar mai taushin gaske da take can gefen office d'in. "Questioneer Allah ya dawo min da ke, ban yi aure ba Allah Kuma Kada ya k'addara min aure a rayuwata, ba na fatansa ko misk'ala zarratin daga yau kuma bana son naji kin sake danganta ni da kalmar matar aure please and please." Ta fad'a tana had'e hannayenta waje d'aya alamar rok'o. Wani irin kallo galala Saliman take mata na tsananin mamaki da takaicin Ayran, ashe har yanzu wancan bahagon tunanin yana nan a zuciyarta babu abinda ya canja sai ma dad'a bun k'asa da lamarin ya yi. Tun suna yara ta sha fad'ar haka sai dai sam suna d'aukan abin shirme a
Kullum kuma suka tambayeta dalili sai dai ta yi murmushi ta runtse ido tana rawar murya zata ce "Dalilina mai k'arfi ne kuma gamsashshe amma babu buk'atar ku ji shi." Daga haka zata goge k'wallar idanunta a kuma tsayin ranar ba zaka sake
Ganin walwala tattare da ita ba, wannan dalili ya saka Saliman sam bata cika damunta da tambayar son sanin mak'asudin k'iyayyarta da aure ba.

Yanzun ma jan ajiyar zuciya ta yi kafin ta ce "Allah ya kyauta, ni kuwa yanzu shirin auren ne ya dawo da ni Nigeria na ga kuma ba wacce ya kamata ta shige min hidimar bikina idan ba ke ba. Tunda duk k'awayen namu sun yi aure daga ni sai ke ne dama mu ka yi jinkiri."

Tuni duk wata walwala da take fuskar Ayra ta Kau, murya a shak'e ta hau girgiza kai had'e da fad'in "Idan kin amince mai zumbulelen hijabi da nik'abi ta ja ragamar bikin ki sai na ce you are welcome." Kallon cikin ido Salima take mata kafin ta ce "As how Malama? Kada dai ki ce min duk in da za ki da wannan shigar ki ke zuwa?" Ta girgiza kai cike da tabbatar mata "Bayan ku na kusa da ni da muka yi secondary tare ba wanda ya san kamannin Ayra Gaya ko mutanen da muka yi jami'a tare tsirari ne suka sanni, bari na sanar miki k'arshe mutanen companyn nan ba su san zahirin kamanni na ba, da wannan shigar suka sanni na ci sa'a companyn na mu ne ba wanda zai takura min akan shigata. Ko yanzu ba ki ga sai da ta fita sannan na bud'e miki fuskata ba?" Saliman ta sake dubanta tana mamaki da al'ajabi da wani ne da kyan Ayra cike da fariya zai dinga nuna shi amma ita kyan ne ma bata son a dinga gani ta 'dan jijjiga kai kafin ta ce  "Kada dai ki ce min duk don kada ki samu miji ki ke aikata haka?" Ayra ta d'aga kai tana sakin murmushi "Ko Shakka babu, tunda na taso na lura maza suna son d'aga min hankali Saboda fuska da kyawun jikina na gwammace na zama haka, ba su ganni ba ma balle su kwad'aitu da so na." Saliman tana sakin wani irin bahagon murmushi ta ce "Sai dai idan ubangiji bai nufa ba, da ikon rabbissamawati sai alkadarinki ya karye soonest za ki aure." Wani irin kallo Ayra take mata da idanunta da suke bayyana tsagwaron b'acin ranta ta janye hannunta daga kafad'arta cikin b'acin rai ta nuna ta da yatsa "Matuk'ar kin San irin alkaba'in da za ki dinga janyo min kenan, na rok'eki kada ki sake bayyana fuskarki a a idanuna sabida komai ma zai iya faruwa siblings d'ina ma ina samun mummunan sab'ani da su a duk lokacin da suka min irin wannan." Hawaye ne fal idanunta ta mik'e ta shige toilet d'in da yake office d'in. Jikin Salima Sa'ad ya yi sanyi sosai har ta ji tana nadamar furucinta ita kanta hawayen ne yake son zubo mata. Fitowar Ayran daga toilet ya saka hankalin Saliman ya sake ta shi ganin yarda idanunta suka jirkita saboda tsananin tashin hankali. Sai dai da murmushi ta ke kallon Saliman da alamun son kawar da waccan damuwar daga ranta. Ko bakomai Saliman bak'uwace shekara nawa ba su had'u ba bai kamata ta bak'unceta da wannan yanayin ba. Ta dafa kafad'arta tana sake wawuro murmushin duk da k'ok'arin kufce mata da yake son yi ta saki ajiyar zuciya. Idanunta cikin na Saliman ta ce "Kada ki damu K'awata komai ya wuce raina ne ya b'aci, bana Iya controlling temper d'ina a duk lokacin da aka bijiro min da waccan maganar dafatan za ki kiyaye please." Da sauri Saliman ta d'aga mata kai tana sakin tata ajiyar zuciyar had'e da fad'in "Alhamdulillah, wallahi na zata kina fitowa shak'eni za ki yi." Murmushi Ayra ta saka had'e da sake mayar da nik'ab d'inta ta sakeshi ya rufe mata fuska ruf jin ana mata knocking sannan murya a kaurare kamar yarda ta saba kaurarata don bata son ko dad'in muryarta ya ja hankalin maza, balle su so sanin fuskar mamallakiyarta, ta bada izinin shigowa. sakatariya ce take sanar da ita zuwan wani bak'on costomern su da ya saba zuwa siyan kayan k'awata toilet. Tana ba shi izinin shigowa Saliman ta mik'e tana fad'in "Ayra bari na wuce Zan shigo Gida In sha Allah don ina son ki taya ni zab'an outfits da zan amfani da su lokacin biki, may be jibi tunda week end ne ki ganni ki turo min address d'in gidan." Ayra ta zura hannu a jaka ta ciro mata compliment card da address d'in gidansu yake jiki ta mik'a mata. Saliman ta sa hannu ta amsa tana nazarin yarda take jin sunan unguwar ta railway, jin shigowar mutumin yasa cikin azama Saliman ta mata sallama ta fice. Tsawon mintuna suna k'ulla harkar kasuwanci da mutumin ba tare da ya san yarda fuskarta take ba, har mamakin yarda take k'udundune fuskarta yake don ko k'wayar idanunta baya gani, ya sha tunanin wani irin miji take aure mai matuk'ar tsanani da takura har haka da ko yatsun matarsa bai amince a gani ba. Sau tari ya kan ja ajiyar zuciya ya kuma jinjinawa mijin nata a zuciyarsa don ko bakomai ya yi maganin masu zalamar kallon mata irinsa, duk ga tunaninsa Ayran matar aure ce. Yau d'in ma siyayya mai yawa ya musu sannan ya mata sallama bayan ya tura mata takardar da take nuna shaidar ya biya kud'in. Ayra ta bi bayansa da kallo tana mamakin yarda yake kafeta da ido ta tabbata da zata bari ya ga fuskarta ba abinda zai hana shi nuna mata zalamarsa a fili, ta ja dogon tsaki had'e da jin tsanarsa a ranta ta tsani kallo ta kuma tsani duk namiji mai kallon mata irin kallon da ake kira kallon k'urilla.

Daga wannan takaicin ta ji aikin ma ya gundureta gaba d'aya ta yi switching system d'inta had'e da mik'ewa ta fara tattara komatsanta da niyyar tafiya gida.


_____________

A harabar gidan nasu da yake railway tsaye kusa da maigadi Mal. Hadi ne yake masa magiyar a bar shi ya shiga. Mai gadin ya kafa ya tsare a kan dokar gidan da Ayra ta kafa masa na rashin amincewa duk wani namiji shiga gidan sai da sanin ta matuk'ar ba d'aya daga cikin surikan gidan ba, shima ta jaddadawa mai gadi idan da wasu suke tare ya tbbata ya sanar da ita zuwansu kafin su shiga cikin gidan, duk wannan tana yi ne a k'ok'arin killace kanta daga idanuwan duk wani namiji.

Dannowar kan motar Ayran ya bawa Baba mai gadi damar fad'in "Alhamdulillah ga Hajiyata nan ma ta zo idan ta amince ka shiga sai ka shiga." Malam Hadi ya hau gyara babbar rigarsa da ta sha guga daga shekara sai shekara yake sakata, ranar idi Amma yau ganin gidan da zai zo yasa ya cancad'e kwalliya cikinta shine har da nad'a rawani. Gyaran murya kawai yake yana shaidawa Maigadi "Yanzu zaka ga ko wanene ni? Zaka san
Ka wulak'anta ni saboda ni da mahaifin yaran nan ba mu da wani banbanci." Hankalin Maigadi ya d'an tashi ga zatonsa duka abinda Hadin ya fad'a da gaske ya ke. Tun da ta yi parking bata fito daga cikin motar ba illa k'urawa mutumin da yake tsaye kusa da mai gadi ido da ta yi. Ba zata mance da shi ba, ba zata manta wannan fuskar ba, fuskar makusancin aminin mutumin da ya kira kansa da sunan mahaifinsu. Ta runtse idanunta ta bud'e tana sake sauke magananta a kan mutumin, wani b'acin rai da tashin hankali yana sake ziyartarta ta tsani duk wani mutum da yake da alak'a da wancan mutumin mai amsa sunan mahaifi a wajensu. A hankali ta cigaba da dukan sitiyarin motar cikin mabayyanin b'acin rai. Ji take tamkar ta fisgi motar da gudu ta je ta take shi ta huta da ganin fuskarsa da take tuna mata da fuskar wancan mutumin.

Tsawon lokaci tana cikin motar ba tare da ta san me ya kamata ta aikata ba. Tabbas ta san idan ta bari ya shiga gidansu yau mahaifiyarta Ammaty ba zata kwana lafiya ba, sai ya tayar mata da tsohon mikin da yake zuciyarta. Dabara ce ta fad'o mata, hakan ya sa ta daddage ta sakarwa Baba Mai gadi wani irin gigitaccen horn, da ba shiri ya saka shi tahowa wajenta a sukane. Da kyar ta sauke glass d'in motar idanunta a rufe ta watsowa Baba mai gadi tambayar "Me wancan mutumin ya ke yi a gidan nan?" Baba Mai gadi da bai san dawar garin ba, cikin in ina ya ce "Wai wajen Hajiya yazo." Ta ciji leb'enta na k'asa da k'arfin gaske kafin ta murza yatsun hannunta suka bada k'ara k'as-k'as "Ka sanar da shi kafin na irga Biyar ya bar cikin gidan nan idan ba haka ba, ko ma me ya faru da shi ba ruwana."

Da sauri kuwa Baba Mai gadi ya koma wajensa ya sanar da shi sak'on, sai dai madadin ya tafi wata dariya ya tuntsire da ita cike da tabbatarwa ya ce "Ka koma ka sanar da ita ba inda zan je sai na ga Hajiya."

Tana daga cikin mota tana kallon yarda yake da hannunsa alamar da gaske yake abinda yake nufi ba ta yi magana ba illa ficewa da ta yi ta isa inda suke cikin tsukakkiyar fuska duk da ba 'a ganinta kafin ta isa wajen ji take tamkar ta waska masa mari sai dai bayyanarta wajen ya canja mata tunaninta ganin yarda mutumin yake kallonta shek'ek'e kamar ya ga kashi. Ba tare da ta gaisheshi ba ta nuna masa gate cikin dakiyar murya ta ce "Cikin lumana Alhaji ka fita daga gidan nan."

Cikin izgili ya ce "Idan na k'i fa tabbatacciya wad'anda suka d'ebe kayansu daga gaban ma'aiki, kuna nan cikin daula kun bar ubanku cikin bak'in talauci wallahi ku kiyayi ranar had'uwarku da Allah." Cikin matuk'ar b'acin rai ta zare nik'ab d'in idanunta fuskarta ta bayyana sosai kamanninta suna nan ba su b'ace masa ba Auta ce. Ya dinga mamakin girmanta da murd'ewar halinta yarinyar da da ko hannu ba zaka saka mata a baki ta ciza ba. Ta sake nuna masa gate "Na had'a ka da Allah ka fita,ko kuma na saka fita ta dole."
Wata dariya ya saki yana sake gyara zamansa kan kujerar robar da yake zaune a kai. "Fitar da ni ta dole" a zafafe ta juya ta nufi can baya inda Ke jin karnukansu suke na police dogs guda uku manyan gaske, da sauri ta sake su ta nuna musu gate.

Takaicin UbaWhere stories live. Discover now