TAKAICIN UBA....
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Page ____6
Da sauri Ayra ta girgiza kai tana dafe da k'irjinta ta ce "Je ki kawai Amma bana son sake ganinta gabana sake tsananta bugu yake wani irin kwarjini ne da ita da kaifin idanu, masu sanya mutum rusunar da nasa idanun ko bai shirya ba."
Amma ta mik'e ita ma nata jikin a sanyaye ta nufi hanyar da zata sadaka da step d'in da zai saukar da kai parlourn k'asan.
Jin saukowa daga bene yasa bak'uwar ta yi saurin juyowa ta zubawa step d'in idanu bayan ta mik'e tsaye cike da zak'uwa da son zuwan Talatun, ta zare glass d'in idanunta tana sakin kyakykyawan murmushin da
Ya sake k'awata kyan fuskarta.Ita kanta Amman ba k'aramar juriya ta yi ba da Allah ya kiyaye bata kifa ba da ta yi ido biyu da bak'uwarta ta.
Tafiyar ta gaba d'aya a harhad'e ta isa wajenta da sauri da niyyar ta tabbatar da zahirin abinda take gani a idanunta shin da gaske ita d'in ce ko kuma gizon da ta saba mata ne a shekarun baya da suka wuce? Ta bud'e baki da k'yar ta na nunata da d'an yatsanta manuniya ta ce "Hameedah? Shin da gaske kece ko kuwa mafarkin da na saba yi ne?"
Ko kafin ta Ankara Hameedah ta kai mata runguma hakan kuma shi ya cire mata kokwantonta ta tabbatr dai Hameedah ce a gabanta, Hameeda dai aminiyarta ta k'uruciya da k'addara ta rabasu, tun bayan rasuwar mahaifin Hameedahn suka tattara suka koma k'asarsu ta Labanon bata sake ganinta ba sai yanzu. Babu abinda zai saka ta manta da fuskar Hameedan don babu abinda ta canja sai alamun girma da ya bayyana k'arara a tare da ita.
Sun dad'e rungume da juna suna sakin hawayen farin ciki, kafin Hameedan ta saketa tana kauda hawayen idanunta wanda yake nuni da zallar farin cikin da take ciki.Ta dad'e bata ga abinda ya faranta mata rai kamar had'uwarta da aminiyartata da take d'aukan ta kamar jininta.
Amma ta Saka hannu tana share mata hawayen kafin ta ja hannunta su zauna akan kujerar mai cin mutum hud'u. Sai da ta zaunar da ita sannan ta koma bakin matattakalar benen tana k'walawa Ayra kira.
Sosai Ayra ta ji Kiran har tsakiyar kanta, abinka da wanda yake a rud'e tuni rud'ewar tata ta ninka ta da. Ta manta da hijabinta ta sauko a guje tunani take wani abin ne ya samu Ammanta. Turus ta yi tana dubansu ganinsu a zaune cikin matsananciyar walwala da farin ciki. Yara mata guda biyun kuwa suka zubawa Ayra ido suna mamakin tsananin kyan da Allah ya bata da dirarren jiki ko su da suke ruwa biyu ba zasu nuna mata komai ba. Ashe a Nigeria ma akwai kyawawa da Kyansu ya kere na su.
Sai sannan Ayra ta ankare da cewa ta manta hijabinta da yake mata kariya daga kallon k'urilla.
Gabanta ya cigaba da matsanancin bugu idanunta a k'asa ta kasa jurewa kallon cikin k'wayar idon bak'uwar Amma. Dattijuwa Hameeda kuwa cikin ranta ta dinga yabon kyawun Ayra har ta ji wani lamari ya fad'o mata ta dinga Binta da kallo tana hasashen abinda zata had'a d'in shine abinda ya dace. Murmushi sosai ya dinga bayyana a fuskarta ta kalli Amma kafin ta ce "Fatabarakallahu Ahasanul khaleek'in ita ma wannan ta muce?" Amma ta d'aga kai tana murmushi kafin ta ce "Itace Autar sauran duk na musu aure." Gaisuwa sosai suka sake yi da Amma da Ayran Amman ta kalli Ayran ta ce "Wannan itace Hameeda babbar Aminiyata da nake baku labari, nake sanar da ku tun bayan rasuwar mahaifinta Mamansu ta wuce da su k'asar su Labanon." Ayra a d'an rud'e ta d'aga kai tana jin takaicin kallon k'urillar da suke Binta da shi. "Maza ki had'o musu drinks da abinci, amma ban ji dad'i ba da baki sanar min zuwanku ba, yaushe kuka shigo k'asar?" Dattijuwar ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce "Tun bayan rabuwata da k'asar nan sai jiya nazo shima d'in Baban yaran nan ne ya damu a kawosu su ga y'an uwa saboda halin rayuwa ina zuwa kuma na je ainahin main house na ku anan ake bani address d'in nan d'in." Ta fad'a cikin juyayyiyar hausarta. Amma ta d'aga kai kafin ta ce "Amma kuwa ba ki kyauta ba, ace yara ba su san dangin ubansu ba sai yanzu." Hamida ta saki murmushi ta ce "Yayansu yana zuwa ai, the moment ya samu hutu yana yawan zuwa don first and second wife d'insa har third ma anan ya auresu, sune dai basa zuwa." Amma ta ce "Ma sha Allah suma sun girma su nawa ne?" Hannayenta ta d'aga tana counting shida cif But biyu maza hud'u mata." Amma ta girgiza kanta kafin ta ce "Allah musu albarka, yanzu Yayan nasu matansa har uku?" Ta fad'a tana k'ok'arin serving nasu abincin da Ayra ta kawo ta jere musu ta wuce sama. Hameedah girgiza kai ta yi tana d'an sakin murmushi kafin ta kalli y'an matan ta ce "Ku bi k'awarku sama mana kafin mu gama ganawa kun san bana son ina magana ana zaune." Da murmushi suka mik'e bayan sun d'au plate cike da snacks, Hameeda ta kalli Amma ta ce "Autannina kenan su twins ne." "Da gani babu tambaya." Amma ta fad'a tana murmushi. "Zallar kamanninsu ya isa ya bayyana kansu a matsayin twins, ya sunan su?" "Tayseer da Tasleem." Hameedah ta fad'a idanunta akan Amman da take cewa "Allahumma barik." "Su kuma naki yaran su nawa ne?" Amma tana murmushi ta ce "Hameedah kenan, kina nan da halinki abin babu kara? Madadin ki ce na ki yaran sai kice nawa yaran, su bakwai ne Shu'ayra da suke kira Ayra ce auta, sauran duk suna d'akin mijinsu itama Ayran dalili ta cunkushe a ranta da ya nuk'urk'usar da son tarayya da kowane d'a namiji a zuciyarta, idan banda haka da tuni tana d'akin mijinta." Ji ta yi kawai Hameedah na fad'in "Alhamdulillah Ma sha Allah, ki ce kaya ya tsinke a gindin kaba tabbas abinda Allah ya jefoni yi kenan." Cike da mamaki Amman take bin ta kallo, kallon da k'arara yake nuna son k'arin bayani. Gaba d'aya fuskar Dattijuwa Hameeda ya canja idanunta suka d'an canja launi daga kalar fari k'al da suke a da kafin wanzuwar b'acin ran zuwa kala mai sirki da ja kad'an a ciki. Kamar ba zata ce komai ba ta d'au cup mai cike da kunun aya mai mugun sanyi ta kai bakinta sai da ta sha sosai don gard'in kunun ayar ya ratsa har tsakiyar kwanyarta ba d'an kad'an ba ya yi dad'i. Ta dire cup d'in tana sake sakin murmushin da kai tsaye za'a iya kiransa na k'arfin hali sannan ta ce "Alfarma d'aya za ki min Salamatu, ki bawa d'anki Amin auren Shu'ayra ko dukkan matsalolinsa za su zama labari."
Sosai Amman ta razana da jin abinda ta ce mata sai dai bata bayyana hakan ba illa shiru da ta yi tana nazari a zuciyarta ya zama dole ta gayawa Hameeda wacece Ayra? Ta hakane kawai zata san cewa Ayran ba ta dace da zama maganin matsalolin d'anta ba, bisa dalilin tarin nata matsalolin da suke zube a kwanyarta. Jin shirun Amman ya yi yawa yasa Hameeda ta matsa kusa da ita sosai ta kama hannayenta gaba d'aya ta matse su cikin nata murya a sark'e kamar mai don yin kuka ta ce "Ki taimake ni Salamatu, wannan ne hope d'ina kad'ai akan rayuwar Al'amin.. Bayan aurensa da matarsa ta farko da suka so juna kamar za su mutu, anan Abuja suka had'u ya aureta ya tare anan Abujan, cikin hukuncin buwayi gagara misali ranar da tazo haihuwar d'ansa na biyu ta mutu. Lamarin da ya gigita Al'amin da kyar na shawo kan matsalarsa duk da har yanzu ba zance ya dawo normal ba ana dai gurgura rayuwar yarda ta samu. Al'amin mai son jama'a mai wasa da dariya sakin fuska da walwala gaba d'aya lokaci guda aka musanya halayensa zuwa wani irin baud'ad'd'en mutum mai saurin fushi da yawan hassala. Ya d'au tsawon lokaci yana katantawa da rayuwarsa ya kasa nutsuwa ma ya yi abinda ya dace sai da na saka aka dinga masa rok'on Allah sannan na samu ya d'an rage wasu abubuwan. Mutane da dama suka dinga ba ni shawarar na aura masa aure da son sa ko ba son sa, na dinga bin shawarar mutane ina aura masa auren sai dai abin haushi duk matar da na aura masa bata iya shawo kansa, don bata shekara suke rabuwa, yanzu zancen da nake miki tsawon shekararsa biyar rabon da ya yi aure. Yaron da matarsa Halim ta bar masa har ya shiga secondary school shekararsa sha d'aya. To yanzu na ga Ayra kuma ta dace da irin matar da duk k'in sa da aure idan ya ganta sai ta masa, tana da structure d'in da zata janye hankalin namiji ko bai shirya ba,
duk da wa'dancan 'din ma kyawawa ne amma a haka ya rabu da su.
ki taimaka min ki ba shi aurenta mu yi tuwo na Maina."Tsit Amma ta yi tana murzar goshinta. Wannan fa shine ga bikin zuwa babu zanin d'aurawa, don dai Hameeda bata san wacece Ayra ba shi yasa ta bijiro da wannan zancen. Ta d'au mintuna tana aikin tunani tana Tufka tana warware wa ta kasa bawa Hameeda gamsashshiyar amsar da ta dace. Da kyar ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce "Ayra ba matarsa bace, saboda sam bata dace da shi ba, idan aka yi auren komai k'ara damalmalewa zai yi madadin abubuwa su gyaru. Dukkanninsu akwai wani ciwo da dafi a zuciyarsu wanda zai tarwartsa duk wani farin ciki da zai tunkarosu a rayuwar aurensu. Ayra ta k'udirce ba zata tab'a aure ba a rayuwarta haka zata zauna, yayin da Amin ya zama mijin matacciya. Ta yaya kike tunanin Ayra zata yi abinda har zai gusar masa da tunanin waccen matar tasa alhali itama ba ta son auren? Don haka ki yi hak'uri ki bar maganar kada ayi abinda zai zo
Ya lalata mana zumunci. Akwai bak'in fentin y'ay'a maza a zuciyar Ayra wanda yasa ta tattara duka maza ta saka su a ma'auni d'aya. Allah ya ba shi matar da zata dace da shi."
Hameedah ta dinga girgiza kai ba don ta gamsu ba sai dai ta'ajibin lamarin. Me zai janyowa Ayra tsanar aure da y'aya maza haka? Ko ma menene tabbas lamarin mai girmane sai dai sam ba zata janye k'udirinta ba, ta san Ayra da zarar taga Amin zata ji tana sonsa don yana da duk wasu tarin qualities da zai saka mace ta so namiji ga nata hasashen fa kenan? Bata san Ayra ta yi nisa bata jin kira ba, ko da gold aka k'irk'ireshi bai zama lallai ta so shi ba. "Ki bari na gwada da kaina zan mata magana In sha Allah za'a dace." Amma ta saki murmushin takaici kafin ta ce "Shikkenan tunda ba ki yarda ba, bari na kira miki ita." Daga haka ta haye matattakala don kiran Ayran da take can tana kallon twins sun baje sai hira suke kamar da can sun santa. Ba su san haushi suke bata ba, don ita bata son mutum mai yawan surutu. Shigowar Amma da kiranta ne yasa duk suka sauka k'asan a tare.Hameeda na ganinsu ta nuna musu hanyar sama alamar su koma ba da su zata yi magana ba. Gaban Ayra na fad'uwa ta zauna daga gefen kujerar da take kusa da dattijuwa Hameedan, tana jin k'irjinta kamar zai tsage zuciyarta ta fito.
Da murmushi sosai dattijuwar take kallonta kafin ta gyara zamanta ta ce "Haba daughter na matso nan kusa da ni, magana za mu yi mai mahimmanci bana son kowa ya ji." Zuwa lokacin ba k'irji ba kad'ai hatta gangar jikin Ayra kad'a wa take da mugun k'arfi, bata son mafarkinta ya tabbata bata son mugun mafarkin da ta yi a barcin ranar ta ya tabbata, ta dinga jin kamar ana kad'a mata gangi. Kasa matsawar ta yi illa baya da ta yi ta rab'e jikin kujerar cikin rawar murya ta ce "Nan d'in ma is okey Hajiya." Murmushi Hameeda ta yi ta ce "Kada na sake jin kin kira ni da Hajiya ki kirani da sunan da yara suke kirana da shi Ummi tunda kema y'ata ce." Ayra gyad'a kai ta yi tana wasa da zobban da suke hannunta idanunta a k'asa Ummi ta d'an matsa kad'an kusa da ita ta ce "Ki yi hak'uri da abinda za ki ji daga bakina, ki sani komai muk'addarine daga Allah, sannan ina son shaida miki a shekarunki ba abinda ya dace da ke irin a gan ki a d'akin auren sunnah, me zai saka d'an Sunna ya ce baya son Sunnar Manzon Allah ai aure ibada ne.....don haka nazo ki taimaka ki auri Yayanki Al'amin...." Cak maganar ta tsaya ganin yarda Ayran ta mik'e da sauri idanunta a waje tana mata wani irin duba nunata kawai take kafin ta durk'ushe a wajen tana fad'in "Ya ubangiji ka d'auki raina kafin tabbatuwar mafarkina, bana son aure kuma ba zan aureba da na yi aure gwara na ganni a cikin kabarina, Hajiya ina ganin girmanki please kada ki bari girmanki......" ta cije leb'enta tana tauna leb'enta cikin jirkicewar launin idanu ta fara kwararar da zafafan hawaye. Ummi Hameeda tsoro ne sosai ya kamata bata san lamarin ya kai girman haka ba.........Jikar Nashe.❤️❤️✍🏽