5

21 4 0
                                    

TAkAICIN UBA...

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Biya 'dari biyar kacal don a yi tafiyar Ayra Gaya da ke...

Ko ki biya special people (Mutane na musamman da ake tura musu kai tsaye cikin wayoyinsu. Akan Naira dubu kacal. Ta wannan account 'din 2118666253 U B A)

Page 5___

Da wani irin wawan haushi suka nufi kansa, in da hakan ya saka shi wani irin rawar d'ari da firgici k'afafunsa suka shiga rawa. Ya nufi bakin gate da sauri da niyyar fita, sai dai tuni suka cim masa, bai san sanda ya saki fitsari a wandonsa yana ihu da tumami. Sai da Ayra taga suna nufin yagalgalarsa sannan ta dakatar da su ta hanyar  kad'a musu harshe irin yaren da take musu kenan idan tana so su bar abu. Cak suka tsaya sai dai suna zazzalo harshensu idanunsu a Kansa da yake mutsu-mutsu ya kasa nutsuwa sam ga ni yake kamar kwanansa ya k'are. Rok'on Mai gadi yake da ya bud'e masa gate d'in ya samu ya fece amma Ayra ta k'i bada damar hakan. Cikin takun isa ta k'araso wajen idanunta cikin nasa ta tsaya a gabansa tare da nuna shi da yatsa. "Ina baka shawarar kada ka sake tunkarar gidan nan, idan ba haka ba Wallahi ka sake zuwa sai na basu damar da za su yagalgalaka. Idan ma Shine ya turoka ka d'agawa uwata hankali ka gaya masa ya shirya tafiya kotu ne? Don wallahi sai na makashi a kotu bisa tarin laififfukansa na baya don ba zan bari wani abu ya samar min mahaifiya ba matuk'ar ina raye."  Jikinsa sake b'ari yake yana tattare rigarsa ganin suna son sake nufarsa Ayra ta dakatar da su sannan ta saka Baba Maigadi ya bud'e masa gate d'in kafin kace me Hadi ya arce da gudu kamar mai gudun tsere da gaske karnukan sun firgita shi. Dariya Sosai Ayra ta yi kafin ta mayar da gate d'in ta rufe ta mayar da kallonta kan Baba Mai gadi. "Kada a sake bud'ewa Mutumin nan gate doka ce na saka." Gyad'a kai Baban ya yi don bai hango wasa a lamarinta ba illa tsananin b'acin rai da ya hango a kan fuskarta. Ya bi bayanta da kallo tana shigewa cikin gidan. Mamaki Baba Mai gadin yake jin cewa wai mahaifinsu yana da rai har ma yana cikin wahala amma sun kasa taimaka masa, ya shiga tunanin wani irin girman laifi mahaifin nasu ya musu da har suka shafe labarinsa a duniyar su. Ya saki nauyayyiyar ajiyar zuciya yana tunanin koma menene Lamarin Mai girma ne.

________________________

Ko da ta shiga Amman tasu tana d'aki hakan ya sa bata damu sosai ba don ta san bata ji duk abinda ke faruwa ba barcin k'ailula take na bayan azahar zuwa la'asar. Zubewa ta yi kan kujera barcin take son yi amma bata son shiga d'aki tunanin da ta saba ya mata rufdugu musamman mutumin nan da yazo ya sake dawo mata da abinda ya wuce take ganin kamar a lokacin abubuwan suke faruwa. Ta runtse ido wani irin zafi take ji k'irjinta yake yi bata san Waye ya nuna masa gidan ba.....
Da sauri ta rarumi wayarta a hasalance ta shiga kiran Dijah Yayarta da take bi, tana zaune a unguwar shara'da. Sai da ta yi ringing sosai kafin Dijahn ta 'daga. Ayra ta sauke ajiyar zuciya kafin ta gyara zamanta ta ce  "Mutumin can da Yake amsa sunan mahaifinmu kin san yau ya turo Mak'ocinsa Hadi Gidan nan?" Da sauri Dijah ta zaro ido kafin ta ce "kan Uban can again? Har yanzu bai hak'ura da nacin mu yafe masa ba kenan tsawon shekara uku idan ban mance ba rabon da ya sake aikowa." Ayra ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce "To yau ya aiko ni kuma na rakaka Hadi da kare a yarda ya tsorata na san kuma ba zai sake waiwayo gidan nan ba." Dijah ta yi dariya sosai kafin Ta ce "Amma Ayra kin kyauta min, sai dai Kada ki sake ki gayawa Yaya Zainab don kin san har gobe ita burinta mu manta abinda ya wuce mu yafewa Baba.." Ayra ta ja tsaki ta ce "Abinda ba zai tab'a faruwa a rayuwa ba kenan ba yafiya tsakanina da Baba wallahi." Dijah ta ja ajiyar numfashi ita kanta zuciyarta ta fara cunkushewa da b'acin rai balle Ayra da lamarin Uban nasu ya fi shafarta murya a sanyaye ta ce "Relax Ayra ba wanda zai ce ki yafe masa ba ke ba ko ni babu yafiya tsakanina da wannan mutumin da yake kiran kansa da sunan mahaifinmu." Ayra tana sakin wata irin ajiyar zuciya ta kashe wayar ha'de da kishingi'da ta runtse idanunta da k'arfi Ko sunan mahaifinta bata son tunawa balle ta jingina shi da sunanta shi yasa a makaranta ma kowa da AYRA GAYA ya santa kai da dama zata iya mayar da sunanta AYRA TALATU. Don shine Sunan ka'dai da ya kamata ta jingina sunanta da shi.. cikin tsananin zuzzurfan tunani wani irin barci mai nauyi ya 'dauketa.

Takaicin UbaWhere stories live. Discover now