Page 12

30 3 2
                                    

YADDA NA KE SO🌺

  BY DIJENSY

Page 12

TALLA! TALLA !

   *Ina ma su son tallata hajar su ku garzayo ku tuntu'bemu ta wannan number 08035584120 domin jin 'karin bayani*

 

        Yaye fuskarta Zainab ta yi ,ita da yan matan da aka bari suka  fito parlour suna dan magana 'kasa 'kasa ta zauna kujerar parlour,d'aya budurwar ta fito hannunta d'auke da kaskon turaren wuta tana kewaye parlourn da wani kamshi mai dad'i.

   "Humm amarya ta ango ,amarya 'kanshi gidanta 'kamshi Zainab kin ganki kuwa?"

  Fari ta yi da ido tana 'kasa da kai "Ni kuna sa ni jin kunya Allah".

  Shewa sukai sai Kuma sukai shiru jin kamar an shigo sauri sukai suka samu guri suka zauna ta rufe fuskarta ,daga shi sai Abdool suka shigo ,ba wani jimawa sukai ba addua kawai sukai Abdool ya tafi da yan matan kai su gidajensu.

    Sussunne kai ta hau yi tana jin kunyar ya Mukhtar din ga kuma bangaren na zuciyarta fal da kaunarsa.Dakin Ummi ya shiga ya ga ta kashe fitila alamar ta kwanta ya kunna ya ga ta lulluba garin da dan sanyi sanyi karasawa ya Yi ya taba kafarta ta bud'e ido don ba baccin ta ke ba "Ummi ,bacci ? Yi hakuri ki taso ina son muyi magana ga can abokiyarki a parlour".

   Gudun kar ya ce ko tana kishi ne ya sa ta mikewa zaune ta yaye zanin gadon ta taso ta fito parlour Yana gaba ta na biye dashi ta sauke idanunta kan Zainab da sai faman sunne kai ta ke ,zama ya bukace ta da tayi ta zauna ya ce.

"Zainab ga Ummi".

Zainab ta dago Ummi tana kallo ta ta ga yarinyarnan ce ,ta dan Yi turus   reaction din Zainab din ya sa ta dawowa daga tunani.

"Sannu Anty fatan an wuni kalau?"

  "Lafiya lau alhamdulillah, sannunki".Ummin ta amsa tana mamaki a ranta tambayoyi fal a cikinta.

   Mukhtar ne ya soma magana ,ya rokesu da su hada kai baya son tashin hankali sannan kuma su dauki junansu kamar yan uwa , Zainab sai tohm ta ke a yayinda Ummi ba ta ce kala ba ya rufe da addua Ummi ta yi musu sai da safe tana komawa d'aki.

     Rufo kofarta ta Yi ta Yi guntun tsaki 'Ga yarinya daman itace ?'

  Kwantawa ta yi baccin ma ya gudu ta neme sa ta rasa ta yi tsaki tana dakko wayarta ta shiga chat bata ga Yusrah online ba ta ajje ta shi  ta kashe hasken fitilar d'akin tana komawa bacci ta rintse idanunta duk ba dadi ta ke Jin kanta.

    

  Washegari bayan ta Yi sallah subh komawa ta Yi baccinta sai to 11 ta farka ,wanka ta yi ta dan gyara d'akin nata ta fito parlour kitchen ta shiga ta duba abinda zata dafa.Doya ta fere ta dafa sannan ta soya da kwai ta hada tea ta Kai dining ta ajje ,nan ne ta ga food warmer wanda ya nuna alama Umma ta kawo wa amarya abinci.Hakan bai dameta ba ita ma an kawo mata sabida haka ta kawar da tunanin ta ci abincinta ta tashi ta tattare kwananta ta kai kitchen ta dauraye ta fito.

   A parlor ta yi turus da Zainab ta Dan yamutsa fuska ganin Ummin,  sanye ta ke cikin jar atampa me black da white touches tayi kwalliya mara nauyi kamshin humra sai tashi yake a jikinta.

  "Ummi ,yawwa so nake na tambaya ko kina da paracetamol ko declofenac?"

   Kai ta jinjina "Sai dai paracetamol,ki duba yana fridge dina"Ummin ta fad'a kai ta jinjina Zainab tana kallon Ummin ta wuce ta shiga kitchen din Ummin ta tsinci kanta da tunanin me zatayi da magani waiwayowa tayi tana kallon tafiyarta ba shakka da biyu ta ke yi baki Ummi ta ta'be ga dukkan alamu so take ta nuna muamala ta shiga tsakaninta da Mukhtar din kenan?

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now