Page 27

29 4 1
                                    

YADDA NA KE SO🌺

 

    PAGE 27


    A hankali ta shigo cikin gidan tana maida kofar ta rufe tasan kwanan Ummin ne don haka ba mamaki yana saman ,dakinta ta wuce tana dire jakarta kan gadon bayan ta tabbatar ta rufe kofa.Tuna maganganun bokan ta shiga yi tana tuna maganar Maman Suhaila 'Ka da ki mance ba a kauce sharudan muddin hakan ta kasance za a iya samun kuskure wani mugun abu kuma zai iya biyo baya' Magungunan ta baje kan gadon tana dubasu ta ga wata laya kanana tana tuna sharadinta da yadda zatayi amfani da ita.

     Knocking din da ta ji a 'kofa ya sata saurin boye kayan a kasan pillow ta nufi kofar tana budewa idanunta suka sauka kan Ummi da ke tsaye duk a diririce Zainab ta ke jinta don gani ta ke kamar zata gane.

  "Ya Mukhtar ne ya ke son lemon tsami yace ki  dashi".Ummi ta fad'a Zainab ta jinjina kai  ba ta ko tambaya mai zai dashi ba ta fito kitchen din tana dakko wa ta bata duka ta koma d'aki Ummi ta tafi ganin Zainab din bata ce mata komai ba ta na mamaki ta wuce  samanta.Tashin zuciyar da ya ke damunsa ya sanya shi bukatar lemon tsamin.A ruwa ya yanka ya na dan sha.

   'Ba a magana ,har sai kin tauna layar sannan ya kasance mutum na farko da zaki wa magana'Ta tuna da maganar bokan ,wajen boyo me kyau ta samu ta ajje su da niyyar duk sanda ta jiyo shigowar Mukhtar din zata sanya a bakinta kafin ta Yi magana dashi ta 'kosa gobe tayi kwananta ya shigo domin aiwatar da sauran ayyukan.

****

  7:01pm tana zaune kiran wayar Yusrah ya shigo ,fuskarta dauke da raha ta dauka suna gaisawa.

"Mutanen America kin buya ,ban ganinki chat kwana biyu".

"Hmm kawata da tuni sai dai ki ji mugun labari fa , miscarriage na samu kwana nayi cir asibiti  bansan inda nake ba Ummi".

Ummin tana shingide kujerar ta tashi "Subhallah ,me ya faru?"

  "Fad'owa nayi daga stair case fa ,wlh missing step nayi Kuma benen gidanmu aikam sai asibiti Ina ta bleeding sai da aka min allura barci na samu hutu"

"Allah ya baki lafiya kawata ya kiyaye gaba sannu ba labari kawata how many month?"
  
  
"Just 8 weeks fa".

"Allah sarki Allah ya musanya alkairi anyi discharging dinki?".

"Eh Ina gida da sauki".Ta amsa Yusrah.

"Tohm alhamdulillah"Ummi ta fad'a.

"Ina Zainabu?"Ta tambaya Ummi ta kalli Mukhtar da ke kwance kasa kasa tace "Tana lafiya".

  "Ko mutumin na kusa ,bari toh mayi chat anjima ki gaisheshi".Cewar Yusrah ta gano Ummi ba ta son jan zancen don haka sukai sallama.

"Yusrah tana gaisheka".Cewar Ummi yace Yana amsawa nan yake tambayar me ya sameta ta bashi labari yayi mata Allah ya kiyaye gaba.

  Wajajen isha yayi sallah ya leka gurin Zainab din ,a kulle yaji kofar d'akin ya kwankwansa Yana mitar ta rufe kofar.Kiran sunanta da yayi ya sa ta ji muryarsa saurin sakkowa tayi daga gadon tana dakko layar ta sanya a baki ta karasa kofar tana budewa.

"Mene na rufe kofar kuma ?"

  Murmushi ta yi tana takatsantsan kar ya ga alamar komai ta taune layar "Ya Mukhtar,sorry dazu ne da na rufota ashe ta shiga key".Ta furta murya a dan cije.

  "Na dawo ba kya nan ina kika je ban sani ba?"

  Tayi tsammanin tambayar don haka tayi saurin amsashi "Makota fa na shiga Maman Suhaila ce Bata jin dadi wayarka na kira busy".

  "An shiga makota naki mijin ba lafiya ba? Da kika dawo kinsan Ina gidan ai baki nemeni ba".

  "Subhallah "Ta furta tana kwalalo ido cikeda nuna damuwa "Yaya me ya sameka?"

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now