Page 22

32 3 4
                                    

   YADDA NA KE SO🌺

BY DIJENSY

PAGE 22

  Dai dai wajen da yake parking ya tsaya da motar shi yana fitowa,tunda ya shigo gidan ya ga yanayin Zainab din kamar mara lafiya ,ya tambaya tace kawai ba ta d'an jin dadi ne.Danwake Zainab din tayi masa tasan abinda ya ke so ne ,ta kai dining komai da take kamar kwai ya fashe mata a ciki tana lura da yadda Mukhtar din ke kallonta time to time ta zauna adjacent da shi tana serving dinsa.Sai da ta ga ya d'an Yi nisa da cin abincin ta d'ana tarkon da ta shirya ,rike ciki tayi ta dafe kai ta furta 'Washh' ya dubeta "Lafiya?"

  Kai ta girgiza "Cikina".Ta furta a hankali  ya ajje cokalin yana tasowa  "Zainab me ke miki ciwo? Jikin ne?"

  Kai ta jinjina tana sake squeezing mararta "Ciwo ,cikina kasan marata tun dazu nake dan ji yanzu ya karu ".

     "Tashi mu tafi asibiti ya kamo hannunta ta mike tsam ta rike hannunsa Yana tafiya ta ce "Yaya tsaya ,wani abu na ke ji kam...."

Yadda tayi planing ta san kanta tana da rushing a period balle idan day 2 dinta ne ,ta kalli kasan tiles din da yake ruwan madara mai kyalli sai ga d'igon jini tar tar tar "Yaya jini wayyo Allahna  me yake faruwa?"

   Komawa tayi ba shiri ta zauna tana karkarwa hawaye na bin kuncinta ,Zainab is so dramatic queen gabadaya Mukhtar ya rikice bai da experience akan ciki sam ganin jini dai ya san ba lafiya ba cikin da ko fitowa bai ba?

   "Tashi mana Zainab ya zaki koma ki zauna? Ya fad'a a rikice .

Daga murya yayi "Ummiii! Ummi!"
Ya hau kwala kiran sunanta ,kasa kasa ta ji yo muryarsa ta ajje wayar da take dannawa tana tasowa ta leko ta Saman benen stair case din "Ummi ki sakko Zainab bata da lafiya zamu je asibiti".

"Subhallah me yasameta Kuma?"Ta furta ba mai amsa mata.

  Sakkowa tayi ba shiri Ummin ta waro ido da ta ga jini ,d'akin Zainab din ta nufa ta dakko hijab dinta itama ta je ta zira nata basu tsaya ko ina ba sai asibiti tun da ta fara zuwa can din yasa ya je asibitin banda haka niyyarsa ya kaita wanda yake da HMO.Tun a gida ta riga da tayi magana da Nurse din da take da hadin baki gunta ,ita ta taresu gashi asibitin shiru likita ya fita sai nurses masu night d'aki suka shiga da ita ta bukaci da su tsaya  daga waje Ummin.Su biyu kawai suka tsaya kanta ,ankai kamar minti 15 suka fito ita mutuniyar Zainab din Nurse Amina ta dubi Mukhtar.

"Yallabai yanzun doctor baya nan ya fita amma na dubata cikin jikinta yana nan sai dai gaskiya ta kula ta  daina aiki  sosai sai tayi a hankali don yana hadari a kodayaushe zai iya samun matsala jinin da ta zubar yanzu bashi dai dayawa amma za a rubuta muku magani".

  Kai ya jinjina Mukhtar din "Amma me ya kawo hakan?"

Dan jin tayi "Wannan zaka zanta da matarka ta bukata da zata fad'a maka da kanta kar mu Fadi dalilin faruwar hakan ,hope dai na wata matsala ko yallabai ?"Amina ta fad'a tana bin Ummin da kallo sannan ta dubesa Bai gama fahimtar ta ba dai ya jinjina Kai  bayan ta tabbatar da zasu iya shiga su ganta ta wuce,d'akin ya fad'a Yana ganinta kwance.

"Ni fa wannan asibitin Bai min ba ta ya a wannan lokacin kaf asibitin ace likita bai zo ba matsalata da irin asibitinan Zainab"

Ya'ke tayi daga kwancen alamar ciwo ,ta ce "Yaya kar fa ka damu komai lafiya fa tace kawai zan Dan samu hutune".

Shiri yayi yana son tambayarta maganar da zata yi dashi kan abinda ya haddasa ciwon sai ya ga da Ummi ba mamaki bazata so fad'a tana nan ba yace "Allah ya kara sauki  yanzu sai ba Kya jin ciwo ko?"

Kai ta jinjina ya gid'a Kai Ummin ta matso daf da ita "Sannu Zainab ,Allah kara sauki".Ta furta.

Ameen ta amsa,wajen karfe tara suka  komo , Mukhtar ya so su jira likita Zainab ta 'ki yarda tace sam ya kyaleta suka dawo gida sai dai ya tabbatar mata sai sun canja asibiti ta dai masa shiru tayi lamo gaban motar.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now