YADDA NA KE SO🌺
Tana kitchen ta jiyo muryar Lubabatu kasa tana gaishe da Zainab,sauri tayi ta fito kasan tana murmusawa Lubabatu ta karaso gunta.
"Anty Ummi Ina kwana".
Amsawa tayi tana fadin "Hawo sama mana ya kika tsaya daga Nan ,mu je sama".
Bayanta Lubabatu ta bi Zainab ta bisu da ido tana nazari ta koma ta zauna tana cigaba da kallonta.A sama kuwa lemo da ruwa ta dakko ta kawo wa Lubabatun tana godiya ta Mika mata yar ledar da ke hannunta ta ga dabino ne me yawa ta amsa tana budewa tayi godiya .
"Anty Ummi na je fa Niger shekaranjiya na dawo".Ta fad'a Lubabatun Ummi ta waro ido "Lubabatu shine ba labari".
"Kiyi hakuri wlh ba jimawa nayi ba ".
"Ziyara ko me?"
"Eh..to Anty Ummi fa an sa ranar aure na shine na je gaida yan uwan Ummana kafin biki".
Baki ta Bude tana kallonta can Kuma ta harareta "Lubabatu auren naki ma a makare zan ji? Ni yanzu komai a karshe nake ji Kun yada ni ko kin samu sabuwar Anty Nafisa tace kin koma gunta".
Marairaicewa tayi Ummi ta ke ganin sake gogewarta ta yi murmushi "Amarya gashi har kin fara glowing Allah ya kaimu ya sa albarka yaushe ne".
"Wata biyu ,a kure aka sanya lokaci".
"Dan garinnan ne?"
"Bauchi ,dan uwan Baba ne". Lubabatu ta amsa.
"Kina son shi kuma?"
Murmushi tayi a kunyace Ummin ta jinjina kai "Iye kina so tohm Allah tabbatar kin fitar mana da anko ko ?"
"Anty ai sai yadda kika ce zuwa nayi ki tayani za'ba ".
Yar dariya tayi tohm "Tohm bari na je na karasa mana abincin ko".
Lubabatu ta ce zata tayata,ta bita a baya Zainab tun a kasa tana ta sake sake.Ummi suna girkin suna hira Koda suka kammala ta zuba musu tare suka ci , Lubabatu tana ta Jin nauyi tana mamakin yadda rayuwa ta sauya ne idan da za a ce mata akwai sanda Ummi zata ci abinci da ita bazata yarda ba sai gashi , Ummin ta gano haka tace "Ki saki jikinki Lubabatu".*****
Ummi ganin Lubabatu yasa ta samu dama tayata suka canja labulen dakin da sauya zanin gadon sai d'akin ya canja ta kunna turare.Jin ta Daina Jin muryoyinsu yasa ta haurawa saman , tana lekawa ta ga basa parlour .Jakar Lubabatu ta duba ta karasa cikin sauri ta dauki Jakarta wayarta da ke hannunta ta zira sai agogo ciki tana rufewa tayi gyaran murya tana kiran Ummin a daki ta fito.
"Ahn..Ummi nace bakuwarki daman akwai wani Abu da nake San kyauta dashi ba damuwa ki aikota ta amsa".
Dan jim tayi ta ce Tohm ,kiran Lubabatu tayi Daman sun gama aiki tace bari tayi wanka ta bi Zainab din zata Bata Abu.
Murmushi mugunta tayi Lubabatu kuwa ta bita,Dan duba locker tayi har d'aki ta kira Lubabatun ta Ciro wasu kayanta "Kinga,gwada idan ta miki abaya ce".
Zainab ta fad'a tana fita Lubabatu ta ji banbarakwai ganin ta barta d'akin shiryawa ,ko da ta gama ta fito ta sami Zainab din fuskarta dauke da farawa tace "Tayi min kin ga".
Kai Zainab ta jinjina Lubabatu ta Yi godiya ta koma ta cire ta Bata Leda ta Sanya ta komo wajen Ummin da ta gani tayi tsaki "Ke Kuma kika karbo?"
Shiru tayi Lubabatu Ummi tace "Ki bada shi me zaki da kayanta ? "
"Anty Ummi fa ba komai wlh ai sabo ne".
Ummi ta dage bazata Saka ba tace ta barsu ma bazata fita da su ba da kyar ta yarda Lubabatu zata tafi dashi amma bazata saka ba..
YOU ARE READING
YADDA NA KE SO
General FictionYADDA NA KE SO burin Ummi ta auri mijin novel ,Mai arziki ba ta son talauci ya rayuwa zata juyawa mata a sanda ta rasa gatan mahaifiya ta tsunduma cikin rayuwar aure da namijin da baya cikin tsarin lissafinta,ga Zainab ta samu mijin da ta ke so shin...