Page 18

25 1 0
                                    


YADDA NA KE SO🌺

BY DIJENSY

PAGE 18

Fitowarta daga class ke da wuya ta ga kiran Mukhtar din ,ko da ta daga ta ji ya tambaya ta tashi daga school ne tace masa yanzu dai zata fito yace mata yana bakin gate jiranta.

Kallo ta bi wayar dashi tana tunanin shikuma biyowa yayi yau? Bayan tayi sallama da wanda take tare da su ta nufi wajen tana ta dubawa ina zata gansa ba ta ga Mukhtar ba ,wayarta ta ji ta Yi ringing ta dauka "Ban ganka ba".

"Nikuma ina ganinki".Ya fad'a ta dage gira tana dube dube ba ta taba tsammanin ba ta gansa cikin wata mota honda accord a gidan gaba alama shi ke tukawa.Ta ma rasa me zatayi ,me hakan yake nufi ?ya sayi mota kenan?

"'Karaso mana Hajiya?"Ya fad'a ta taka a sanyaye ta kewaya gidan gaban ya bude mata ta ciki ta shigo tana rufe kofar.Ita duk mamakinta yaushe ya iya mota?"

"Are u surprised ne ?"

Kai ta jinjina "Ban San ka iya driving ba ,Kuma ...yaushe kayi mota?"

Murmushi yayi "Shiyasa kika kasa tahowar tsoro kike kar ki hau motar dan koyo?"

Kai ta girgiza da murmushi a fuskarta "Congratulations, Allah ya sa albarka ".

"Ameen".

"Yaushe ka siya ko ta dade nuna min ne bakai ba?"

"A a ,kawai dai na fara koyon driving gun Abdool tun tuni". Ya amsata cikeda Jin dadin yadda take kokarin hira dashi.

"Ohkay,tayi kyau sosai".

"You're welcome ko na baki ki tuka mu?"

Tayi suarin girgiza Kai "Ina na iya ?"

"Really?"Ya tambaya Yana ta da motar ya hau titi tana duban yadda yake driving a nutse Yana magana.

"Ban iya ba tun can baya na so koya ya Abdulbasit suka ki koyamin". Ummi ta fad'a.

"Ayya ,sai na koya miki idan na gaji ki dinga tukamu".Ya fad'a tayi murmushi tana tunanin yadda yake maganar kamar ita kadai ce matarsa? Sai ta ji ina ma babu babun Zainab din da kamar rayuwar zata fi dad'i har tana tunanin da da Zainab din za fa ta iya sa rigima bazata zauna baya ba? To waye zai zauna bayan? Tab!

"Ummi".Ta ji ya kira ta juyo ya hade gira "Wai tunanin me kike kwana biyu?"

Kai ta girgiza "A a fa kawai na shaafa ne ,just thinking yadda zan koya din nake".

"You can do it ke da baki da tsoro".Ya furta.

Kallonsa tayi tana son auna zancen nasa na bata da tsoro? Kallon da yake mata ne? Toh.....

Wayarta ce tayi ruri yasa ta kawar da tunanin tana cirowa a jaka ta ga Anty Sa'a ce ko da ta daga tace mata ai sun zo gidanta ne Kuma Basu sameta ba amma dai sun tarar da kishiyarta tace musu tayi nisa don haka suka wuce , Ummin Bata ji dad'i ba ko meyasa zata Yi hakan?

Ganin sauyin fuskarta yasa ya tambaya ta fad'a masa amma bata ce Zainab din ta fadi wani Abu ba.Yace ta je wani satin ta amsa da toh.

Zainab a gida tana zaune ta ji tura gate mota ta shigo duk ta bayar Abokin ne ko baki ta ga Ummin ta fito daga motar malolon bakin ciki ya tsaya mata tambayar ta yaushe Mukhtar yayi mota bata sani ba sai Ummi ta fara sani.Rurin wayarta taji ta ga Mukhtar dinne ta daga yace "Amarya fito kiga wata amaryar ".

Hade Rai tayi ta katse da kyar ta iya saita kanta ta fice wani murmushi ta yafa a fuska ta nufi gun tana hugging dinsa ta gefe ta dubi miyar ta hau ma Sha Allah ta nufi Ummi tana tallafota "Yar uwata my Taya mijinmu murna Allah ya tsare ya sake budi".

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now