Page 13

35 3 0
                                    

  YADDA NA KE SO🌺


  BY DIJENSY

https://chat.whatsapp.com/LWLjxERDFd1JbCeDRQ7XKO

PAGE 13

   
      

   Washegari da safe ta kasance ranar da Mukhtar zai koma aiki don aurensa da Zainab ya dauki gajeran hutu ,yau ta kasance ranar komawarsa bayan ya shirya ya fito parlourn ya tarar da Zainab din ,yau ma ta Sha kwalliya cikin material dark blue dinkin doguwar riga mai slit gefe da gefe sai wando dogo a ciki ta Yi daurin turban.Gaishe shi ta yi fuskarta da murmushi,ganin sa cikin shiru ta ce "Har ka shirya ?"

  Kai ya jinjina ta dan  maida murmushinta ya gano hakan ya sa ya tambaya "Ya dai?"

Kai ta girgiza ta ce "ba komai kawai dai nasan gidan zai min ba dad'i".

Murmushi ya dan Yi ba "Bayan ga yayarki".

  Kai ta jinjina "Kuma fa hakane tohm shikenan ai Allah ya kiyaye".A fili ta fad'a a ranta kuwa tace 'A ubanta zata zama yayata'

  Ya amsa da ameen kafin ya fita ta koma cikin d'aki "Yar bakin hali tana d'aki ,ta bar shi da yunwa Allah kaimu gobe zaki ga ikon Allah ba dai kwanan naki ya fita ba".

   Ummi kuwa bayan fitarsa ta fito ta shirya abin karyawa bayan ta ci ta koma daki ta shirya ,doguwar atampa ta saka ta Sanya hijab maroon wanda ya shiga da atampar sannan ta dakko jaka ta fito ba ta damu da ta duba wajen Zainab ba ta fita , Zainab din ta hango fitarta ta window ta ta'be baki "Tinkiya".Ta furta tana murmusawa tana hango irin borar da zata maida Ummin.

  
     Bayan ta gama dafa indomienta ta soya kwai ta fito ta ci abinta ta Kai kitchen ta wanke , fitowa parlour ta Yi wani tunani ne ya fado mata ta tsinci tana San ganin irin dakin Ummin ko ya fi nata kyau ,d'akin ta nufa ta ga kofar a bude da ta tura ta shiga ,ta ga dai komai tsaf sai dai na Ummin bayan irin kamshin humran da nata ya ke yi ta murmusa hakan ya mata ta shiga dayan d'akin nan ma fitowa ta yi ta shiga kitchen ta bude fridge kayan amfani ta gani cike ,sai kasa ta ga leda ta duba ta ga kifi ne mai yawa dan bugawa ta ji yana yi ta girgiza kai "Kan uba ,uban sa ta ke Jira ya gyara mata?" Dariya tayi Zainab ta rufe ,Wanann uban kifin ma ina zata Kai shi shi da ya kawo mata ina nawan?"Ba Mai amsa mata ta fito  ta  ta zauna daga kan kujerar tana kunna TV ta soma kallo.

  ****

Ummi daga asibitin ma gida ta wuce , ta gaishe da Anty Nafisa ta fita ta je gidansu Yusrahn.Bata kirata ba sai ganinta kawai ta Yi taji dad'i sosai, Shaheeda ba ta nan hakan yasa ba ta biya ba sai bayan zuhr ta fito ta tafi gida kar Mukhtar ya dawo ya ga bata nan.A parlor ta iske Zainab lokacin ta fito daga d'aki ta dubeta Zainab din "Au fita kikai ? Na bayar kina d'aki nasan dai fitowar baya daminki nace gashii bani da number ki da na kira ".

  Yake ta Yi Ummin "Ba nisa nayi ba ai na dawo".Ta fad'a ba yabo ba fallasa.

  Kai ta jinjina Ummin bata sake magana ba ta wuce d'aki Zainab tana jin haushi bata ma kula zancen maganar number ba ta rasa wani irin girman Kai ne da Ummin.Koda tana shiga d'aki fitowa tayi kitchen din ta d'akko ruwa ta komo d'aki ,Jakarta ta Bude tana dakko maganin ta jujjuya kafin ta ballo daya ta sa a baki ta kora wayarta ta dakko ta shiga alarm ta saita kullum gudun kar ta dinga fashin shan maganin kamar yadda aka bata prescription tunanin inda zata boye take daga baya ta yanke shawara dakko wani box din sarkarta ta sanya ciki ta ajje tana tunanin abinda ta yanke din dai dai ne?

 
  
      Zainab har ta kosa yamma ta yi ta soma wa Ya Mukhtar girki ,don ta tanadi irin girkin da za tayi masa.Tun Maghreb ta ke zuba ido ,Koda ta gama girkin ta shiga wanka ta fesa kwalliya ta fito ta turara d'akin da humrah ta fito parlourn nan ma haka,ganin 7:30 yasa ta dakko wayarta ta kira shi ,dazun da rana ta kira Bai amsa ba yanzun ko zai daga?

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now