2

602 15 5
                                    

*SHU'UMAR MASARAUTA*

       ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba.

   SHAFI NA BIYU

    Ras! Ta ji gabanta ya yi mummunan faɗuwa, lokaci ɗaya ta nemi yawun bakinta ta rasa. Cikin firgici ta buɗe baki za ta yi magana Fulani Umaima ta katse ta. "Me kike yi a nan kuma uban me kike leƙe?" Maimuna ta zube a ƙasa jiki na rawa ta furta. "Ki yi mini aikin gafara uwar gijiyata, na zo na ji ko Fulani nada buƙatar wani abu kafin na tafi." Da hannu Fulani Umaima ta nuna mata hanya, sum sum sum Maimuna ta fice jiki na karkarwa. Fulani Umaima ta leƙa Fulani babba da ke kwance, ta saki murmushi mai ɗauke da ma'anoni a hankali ta furta. "Mu zuba mu gani idan tusa na hura wuta, in dai ni ce yanzu kika fara gani." Daga haka ta fice daga ɗakin.

   Fulani babba ta jima a haka sannan ta farka, a hankali take sauke ajiyar zuciyata. Duk da a mafarki ta ga Mai martaba yana kusantarta abin ya yi mata daɗi, ta ji farinciki matuƙa saboda idan ba mantawa ta yi ba rabon da wani abu ya shiga tsakaninta da Takawa tun cikin jikinta bai fi wata biyu ba. Danshin da ta ji a jikinta ne ya sa ta kai hannunta, da mamaki take kallon makwancin nata. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi nan take fitsarin da ke naɗe da zaninta ya fara ɗiga, da farko ta yi tsammanin ko faya ce ta fashe mata tun da a halin da take ciki tana iya haihuwa a kowane lokaci, musamman da take jin ciwon mara sama-sama. Sai dai zarni-zarnin da ta ji ne ya sa ta shinshina hancinta. A hankali ta furta. "Fitsari? Ni kuma? Kai ina jin dai faya ce ta fashe." Gudun wasu-wasi ya sa da kanta ta ɗebo ruwa ta sa a katifar ta sauya kayan jikinta amma har lokacin gani take faya ce ta fashe mata. Banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito sannan ta ɗan ci abinci, a hankali ta ji mararta na ci gaba tsikararta daga baya bacci ya sake yin awon gaba da ita.

   Fulani Umaima kai tsaye sashenta ta wuce don a ranar ba ta jin sha'awar zuwa wurin Mai martaba. Da shigarta babu jimawa sai ga Jakadiya ta shiga ɓangarenta da saƙon Mai martaba na gayyatarta zuwa turakarsa, ba don ta so ba haka ta amsa mata. Jakadiya har za ta tafi Fulani ta dakatar da ita. "Jakadiya ba na son ki yi nisa da sashen Fulani babba." Jakadiya ta amsa mata sannan ta fice. Cike da kissa Fulani Umaima ta shirya kanta da sihirtattun turarrukan da Bamaguje yake haɗa mata, ta ƙarasa turakar Mai martaba. Zamanta babu jimawa suka ji wata ƙarar busar sarewa. Da sauri Fulani da leƙa kusurwar turakarsa idonta ya sauka a kan ƙaton shurin da gudajen turuwa suka zagaye da ke cikin ɗakin, gabanta ya yanke ya faɗi don ta san tun da ta ji wannan sarewar a yau mai afkuwa za ta afku. Mai martaba ya saci kallonta, haka kawai yake jin shakkarta a zuciyarsa. Amma ko shakka babu wannan busar sarewar da shuri ya saki na da alaƙa da cikin jikin Fulani babba wanda yana da yaƙini za ta iya haihuwa a cikin daren nan. Ya so ya tanka wa Fulani Umaima amma sai ya fasa, hakan ya sa ta saki murmushi cikin kissa.

"Jikina yana ba ni Fulani babba na gab da kawo mana Yarima, wannan abin farinciki ne. Tun da shuri ya saki sarewa na tabbata a yau za mu iya samun ƙaruwa a gidan nan." Faɗaɗa murmushinsa ya yi, ya janyo Fulani Umaima jikinsa ya furta. "Wannan haka ne yanzu me kike ganin ya kamata a yi?"

"Ina ganin zai fi kyau a yi dakan ɗaka shiƙar ɗaka... sai a kira Jakadiya ta zauna a wurinta koda ciwon zai tashi tana kusa da ita, a madadin a kira Ungozoma. Amma sai yadda kace ranka shi daɗe farin jakada." Fulani Umaima ta ƙarasa magana tana sunkuyar da kai ƙasa. Ajiyar zuciya Mai martaba ya yi, "Na baki wuƙa da nama mai farar zuciya Allah ya yi miki albarka." Fulani Umaima ta amsa sannan hirar tasu ta fara sauya salon faranta ran ma'aurata. Zuciyar Fulani Umaima ƙal ta je ta samu Jakadiya da zancan Takawa, Jakadiya na gama sauraronta ta yi ƙasa da murya tana ɗan waige sannan ta ce. "Wani ma ya yi rawa ma ballantana ɗan makaɗi? Ai wallahi sai mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi. Ina mai yi miki albishi tauraruwar Mai martaba gobe war haka Fulani Babba na nan cunkushe da baƙin ciki fal ƙirjinta, idan an isa a yi Yarima ba a ɗakinki ba shegiya nake." Fulani Umaima ta saki dariyar ƙeta. "Jakadiya tamkar zuma haka kike ga zaƙi ga harbi. Na aminta da ke fiye da haka ma za ki iya aikatawa."

SHU'UMAR MASARAUTAR CmpltWhere stories live. Discover now