6

597 9 0
                                    

*SHU'UMAR MASARAUTA*

       ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.

  SHAFI NA SHIDA

    Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta zauna a gefen gado, wani irin gumi ya fara tsattsafo mata.

"Binciken da nake kan yi dangane da abin da kike ɗauke da shi a cikin cikinki, na shafe tsawon kwanaki ina bincike har yau na gagara sanin mene ne a ciki. Kullin duhu nake mai ɗauke da rashin alkairi, duhu ne mai ɗauke da tururi da ke ƙone duk wani makusancinsa. Ba ke kaɗai ba ni kaina ina da burin sanin me za ki haifa domin amfanar gobena. Ina buƙatar Magaji a halwar tsafina Umaima."

A razane ta ɗago tana kallonsa, "Ban gane kalamanka ba Bamaguje, me ye alaƙar abin da yake cikina da gadon halwar tsafinka?" Bamaguje ya saki murmushi. "Wannan sirrintaccan sirri ne tsakanina da mahaifiyarki, ba alaƙar abin cikinki ya kamata ki tamabaya ba. Amma mu jirayi lokacin kin san ko ba daɗe ko ba jima akwai lokacin da ya za ta ɗakin ƙanwa."

Sallamar Baiwa Salame ta katse Fulani Umaima daga duniyar taunanin abin da suka tattauna da Boka Bamaguje. Ba ta amsa mata ba don haka Baiwar ta koma, Fulani Umaima ta miƙe ta ci gaba da kaiwa da kawowa damuwa cunkushe a zuciyarta. Kamar wacce aka tsokara haka ta miƙe ta ƙarasa ta ɗauko akwatin sirrinta, ta ɗauko littafin da Bamaguje ya bata. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe shafin da ta tsaya da karatu.
 
Na jima a tsugunne gaban Uwar Bayi ina tsammanin kalamanta har sai da na fara yanke ƙauna da samun abin da nake buƙata, ba zato na ji muryarta a tsakiyar kaina.

"Hidaya labarinki cike yake da almara, al'ajabi da ban mamaki. A tsammanina ni ce mace ta farko da na fara tozali da ke a cikin masarautar nan, ban sani ba ke 'yar cikinta ce ko akasin haka. Abu ɗaya na sani watarana na tafi isar da saƙon Fulani Hauwa na gan ki tsaye a jikin bishiyar kukar da ke bayan ɗakunan Bayi kina rusa kuka, gudun kada na yi latti a aiken da aka yi mini ya sa sai da na kai na dawo har lokacin ba ki daina kuka ba. Da yake a ranar an shigo da sababbin Bayi sai na yi tsammanin 'yar ɗaya daga cikinsu ce yawo ya kawo ta nan take kuka ta gaza gane hanya wurin mahaifiyarta. Sai na riƙe miki hannu muka wuce sashen Bayi na ƙaraci cigiya babu wanda yace 'yarsa ce, to da yake a cikin Bayin da aka kawo akwai wasu mata biyu da suka rasu sai na yi tsammanin mahaifiyarki na ɗaya daga cikinsu. Amma daga baya sai na ga 'yan uwansu suna cewa sam ba tare da su aka kawo ki ba, wannan dalilin ya sa kika ci gaba da zama a sashen Bayi ba tare da iyaye ba."

Kalama Uwar Bayi suka zo ƙarshe a daidai lokacin da ni kuma bakin ƙomar idaniyata ta ɓalle, sai da na yi kukana mai isata na dube ta. "Haka zan ƙare rayuwata ba tare da sanin makomata ba."

Uwar Bayi ta wara hannuwa. "Abin da na sani kaɗai na sanar da ke, idan Allah ya sa akwai rabo sai ki gansu ko a nan gaba ne." Yau ita ce rana ta farko da na ji daddaɗan kalamai daga bakin wani daga cikin Bayin da nake mu'amala da su, don haka na ƙirƙiri murmushin da bai kai zuci ba na furta. "Shi kenan ina godiya Uwar Bayi da wannan bayanin naki." Babu wanda ya sake tanka mini haka na tashi jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da wuƙa na koma mazaunina na farko na zauna ina jin zuciyata babu daɗi. Ina jin su suka ci gaba da hirarsu sai dai ko kaɗan ba na fuskantar koda kalma ɗaya, zuciyata ta yi nisan kiwo a fannin tunani da na gagara janyo ta balle ta gane in da hirarsu ta dosa.

  Wani farin tsoho mai ɗauke da farin gemu na gani yana tunkaro ni, tsananin kammanin da muke yi da shi ya sa na tsaya cak ina kallonsa. Tun da na zo duniya ban taɓa ganin mai kamceceniya da ni ba, ban yi tsammanin ya kusance ni ba don haka na ji hannuwansa a cikin nawa.

SHU'UMAR MASARAUTAR CmpltWhere stories live. Discover now