7

559 7 0
                                    

*SHU'UMAR MASARAUTA*

       ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.

  SHAFI NA BAKWAI

      Koren macijin da Umaru ya kashe tun kafin haihuwar matar nan suka hango ya sulalo ya kafe su da ido yana kallo tamkar zai far musu da sara, suna nan cikin tsinkewar zuciya suka ga ya ƙarasa wurin jaririyar ya kanannaɗe ta, suna daga wurin da suke a gefen Umaru ya ce. "Mai gado an ya yau mun shigo dawa a sa'a kuwa?" Da sauri ta girgiza masa kai. "Tun wuri mu kama hanyar gida." Cikin sanɗa suka miƙe da niyyar tafiya sai dai bisa ga mamakinsu babu macijin babu alamarsa, don haka suka nufi hanya da niyyar tafiya.

Cak Mai gado ta tsaya tana waige. "Tsayawar me kika yi Mai gado?"

"Mai gida zuciyata ta karaya, ba zan iya tafiya na bar yarinyar can ba. Ka dubi yadda mahaifiyarta ta aminta har ta damƙa mana amanarta. Ba mu sani ba wataƙila samunta babbar rahama ne a tattare da mu, ta wani fannin ma gani nake Allah ne ya azurta mu da samunta ka duba ka gani haihuwata huɗu duk yanzu babu rayayye, idan muka bar ta a wannan ƙungurmin dajin ba mu san wacce irin rayuwa za ta gudanar ba." Jikin Umaru ya yi sanyi ya waiga yana hango jaririyar da ke tsala matsanancin kuka. "Mu je na ɗauko ta In Shaa Allah, Allah zai kare mu tun da ya ga kyakkyawar niyyarmu." Da haka suka rankaya suka wuce har gaban jaririyar suka ɗaukota, Mai gado ta kunto ɗankwalinta ta nannaɗe ta a ciki sannan suka nufi hanyar da za ta sada su da gida. Sai da fargabar da Umaru yake ciki ba wuce irin tarbar da mutanen ƙauyensu za su yi musu ba, musamman idan aka samu akasi wani al'amarin almara ya faru kamar yadda suka gani daga wurin mahaifiyarta. Sai dai sun ɗaukar wa kansu alƙwari babu wanda za su furtawa silar samuwar yarinyar don kada ta taso cikin tsangwama da ƙyara.

Masarautar Huddam

    Ɗan matashin ne mai kimanin shekara goma zaune a cikin fadar Sarki Abdul'aziz a kan shimfiɗaɗɗiyar shimfiɗar alfarma yana sanye da rantsattsiyar alkyabba. Kallon mutane yake yi ɗaiɗai fuska a murtuke babu walwala, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da mulkin gadarsa ya yi ba taka-haye ba. Gajiyar da ya yi da zaman cikin fadar ya sa ya miƙe cike da izza yana taku kamar ba zai taka ƙasar ba.

"Takawarka lafiya Yariman masarauta, a huta lafiya sarkin gobe da yardar Allah."

Fadawa suka ɗauka a lokacin da suka lura Muhsin ya miƙe da niyyar fita daga fadar, wasu daga ciki suka ƙarasa suna take masa ba. Hannu ya ɗaga haɗe da tsayawa wuri ɗaya cak, ya kusa minti ɗaya a haka sannan ya furta. "Ba na buƙatar rakiya." Lokaci ɗaya suka ja da baya sannan ya ci gaba da taku, duk hanyar da ya bi haka bayi da fadawa suke zubewa suna kwasar gaisuwa amma ko kallansu ba ya yi ballanta su saka ran zai tanka musu. Yana gab da shiga sashen mahaifiyarsa bisa tsautsayi wata baiwa ta fito da sauri don isar da saƙon Fulani Umaima, a rashin sani ta bangaje shi har sandar hannunsa ta faɗi ƙasa. Jiki na karkarwa ta zube ƙasa.

"Tuba nake shugabana, a gafarce ni uban gidana ni mai laifi ce ba tare da..." Marin da ya ɗauke kuncinta da shi ya sa haƙoranta suka datse harshenta har sai da bakinta ya fashe, idanunta suka fara zubar da ƙwalla ta sake zube wa a ƙasa tana faɗin. "Godiya nake Sarkin gobe." Ɗaga kansa ya yi ya hango wani Bafade hannunsa ɗauke da murtukekiyar bulala ya furta, "A hora ta na tsawon wuni guda da alama ba ta gama sanin a gidan masarauta take rayuwa ba tun da ba ta san aikinta ba." Yana gama maganar ya wuce ba tare da ya jira cewarsu ba.

A kishingiɗe ya tarar da mahaifiyarsa tana huatawa, wasu 'yan matan Bayi na tsugunne wurin ƙafarta suna yi mata tausa. Ganin yanayinsa ya sa ta tashi zaune haɗe da sallamarsu.

SHU'UMAR MASARAUTAR CmpltWhere stories live. Discover now