3

415 9 0
                                    

*SHU'UMAR MASARAUTA*

       ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba.

  SHAFI NA UKU

  Fulani Umaima har ta zura hannu za ta ɗauko ƙahon ta busa sai kuma ta ayyana ta bari idan Maimuna ta dawo ta ji yadda ta ƙarke idan ya so sai ta ziyarci Bamaguje, saman gadonta ta faɗa ta kwanta babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.

  Sannu a hankali ta fara jin dariya sama-sama, sai dai kuma yanayin dariyar ya tababtar mata da dariyar ƙaramin yaro ce. Ba ta tsinke zaren tunaninta ba ta hango wani jariri tube tamkar a lokacin ya zo duniya, tunkaro ta yake yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya hannunsa da wata murtukekiyar igiya yana jan waɗansu murtuka-murtukan shanu, hannunsa ɗaya ɗauke da kwari da baka. A tsorace ta miƙe tana ja da baya ganin jaririn na saita ta da niyyar harba mata, jin bango ya tokare ta ta baya ya sa hankalinta ya sake kai wa matuƙar ƙololuwar tashi. Sai da yaron ya zo gabanta ya furta, "Ba yanzu ba! Zan ƙara miki lokaci." Yana gama maganar ta ga ya juya yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya.

Firgigit Fulani Umaima ta tashi daga nannauyan baccin da ya ɗauke ta har ya gayyato mata mafarkin da ke neman wargaza kwanyarta. Ajiyar zuciya take saukewa akai-akai sannan ta jingina da bango, da ta ga zaman ba zai kai ta ba ta faɗa banɗaki ta yi wanka ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba, a lokacin da tuni rana ta jima da fitowa.
   
   Kamar a mafarki haka ta ga bishiyar na sake tunkaro ta, a yadda take a zaune a ƙasa ta fara ja baya ilahirin jikinta na karkarwa. Wata irin iska mai haɗe da guguwa ce ta taso, Baiwa Maimuna ta sa hannuwa biyu ta rufe idanunta jin ƙura na shigar mata ido. Kamar an yi ruwa an ɗauke haka Maimuna ta ji wurin shiru tana buɗe idanunta ta nemi bishiyar ta rasa, a zabure ta tashi ta ci gaba da gudu kamar wacce ake bi a baya za a zare ranta. Ta jima tana abu ɗaya sannan ta ƙarasa ta bayan masarautar, a lokacin tuni gari ya waye. Sai da ta fakaici idon Dogarawan da ke gefen hanya sannan ta yi sauri ta shiga cikin gidan, tafiya take kamar za ta tashi sama don kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci kwanciyar hankali ya yi ƙaura daga gangar jiki da ruhinta. A haka da samu ta ƙarasa sashen matan sarki tana gab da shiga sashen Fulani Umaima ta ci karo da Uwar bayi, ƙare mata kallo ta yi sama da ƙasa sannan ta ce. "Maimuna daga ina kike haka?" Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, take Maimuna ta yi fiƙi-fiƙi baki na rawa ta furta. "Amm da ma... Yanzu..." Daga can baya Jakadiya ta katse ta, "Uwar Bayi tare muka kwana da ita a sashen Fulani babba yanzu haka gyare-gyare ta gama yi mana." Jinjina kai Uwar bayi ta yi sannan ta wuce, Jakadiya ta ƙarasa wurin Maimuna ta ce. "Ya kamata ki riƙa sara kina duban gatarinki, ki riƙa gayyato nutsu kina yafa wa a gangar jikinki. Kin san sarai wace ce Fulani Umaima." Ajiyar zuciya Maimuna ta sauke ta amsa wa Jakadiya sannan ta wuce sashen Fulani Umaima jiki a saɓule. Tun da ta doshi sashen take jin gabanta na faɗuwa ta rasa dalili, gani take kallo ɗaya idan Fulani ta yi mata asirinta zai iya tonuwa. A haka ta lulluɓa mayafin jarumta ta shiga cikin gidan tana karkaɗe jikinta da ya yi butu-butu da ƙasa.

  "Barka da hutawa ranki shi daɗe." Ƙuri Fulani Umaima ta yi wa Maimuna tana karantar yanayinta. "Binne jariri tamkar wacce ta yi dambe da jarumai biyar, Maimuna me yake faruwa na ga jikinki kamar wacce aka tono daga rami?" Ras! Gaban Maimuna ya faɗi, murya na rawa ta ce. "Ranki... Shi daɗe... Dama... zuwa na yi na sanar da ke an aiwatar da komai... Cikin nasara." Shekararta kusan hudu da Maimuna, ta karanci halaye da ɗabi'unta sarai. Take ranta ya yi mummunan ɓaci don ta fahimci zallar ƙarya a saman harshenta. "Me ya sa na amince za ki iya yi mini komai ban aiwatar da kaina ba?" Fulani Umaima ta yi maganar cike da murmushin yaƙe. Ɗakinta ta faɗa ta ɗauko ƙaho cikin shigar ziyarar Boka Bamaguje, ba ta tanka wa Maimuna komai ba ta miƙa mata hannu, zaro idanu Maimuna ta yi ta ji wani abu yana tsarga mata. Babu yadda za ta yi ta ɗora hannunta a kan nata, ba su jima ba sai ga su a fadar Boka Bamaguje. A wurin da ta saba zama koyaushe yanzun ma a nan ta zaune, gumi ya jiƙe jikinta sharkaf zuciyarta na dakan lugude kamar za ta hudo ƙirjinta.

SHU'UMAR MASARAUTAR CmpltWhere stories live. Discover now