4

982 6 0
                                    

*SHU'UMAR MASARAUTA*

       ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.

*Masarautar Zazzau ta sauya zuwa Masarautar Huddam.*

  SHAFI NA HUƊU

   Wani irin kallo Fulani Umaima ta watsa wa Bamaguje, shi ma ya yi ƙuri yana kallon ta da daƙwa-daƙwan idanunsa jawur kamar sabon barkono, ta katse shirun da ce wa. "Ka na nufin Baiwata Maimuna ce Takawa zai kusance ta? A saboda wanne dalili kuma ba ka ganin tamkar na miƙa kai a kan hanyar da asirina zai tonu?" Bamaguje ya girgiza mata kai. "Matuƙar ina numfashi kullin za ki kasance lulluɓe cikin bargon rufin asirin da babu wani mai numfashi ya isa ya yaye miki shi, dalilin da ya sa na ce ki aiwatar da wannan aikin matuƙar Sarki Abdul'aziz ya kusanci Maimuna ta gaba da baya za ki sha gaban kowa. Wane na mai faɗa a ji a cikin ƙasar Huddam?"

"Sarki Abdul-aziz." Umaima ta amsa masa.

"Ki saurare ni da kyau. Ba akwai wata baƙar rijiya mai baƙin murfi a turakar Mai martaba ba wacce suke kallon juna ita da tsohon shuri mai tsohon tarihi?" Umaima ta gyaɗa masa kai. "Mai martaba na gama mu'amala da ita ki tabbatar kin ɗebi najasar jikinsu sai ki shafa ta akan saman murfin take murfin zai buɗe, ki zura Maimuna cikin rijiya ki koma gefe su zuba ido zai koma ya rufe kamar yadda yake da farko. Maruƙar kika aiwatar da komai yadda ya kamata za ki sha gaban duk wata hallita da ke cikin ƙasar Huddam, kwarjini da tsoronki zai mamaye zuƙatansu ta yadda kina faɗar maganar za a aiwatar miki. Sai dai akwai sharaɗi duk ranar da aka fito da Maimuna daga cikin wannan rijiyar wannan asirin ya karye, amma kuma abu ne da kamar wuya gurguwa da auren nesa domin yanzu haka rabon da a buɗe rijiyar yau kimanin shekara ɗari da hamsin kenan." Umaima ta sauke ajiyar zuciya. "

Duk wannan ban ɗauke shi abu mai wahala ba, shin ya za a yi na wuce da Maimuna har turakar Takawa ba tare da wani ya gan ni ba, kuma na sa shi ya yi mu'amala da ita?"

"Umaima a kullin kin fi son a yi miki ciki a yi miki goyo, za ki saka hannu ki ƙwaƙwalo ƙwayar idonta ki jefa a cikin wancen sihirtaccan ruwan, yadda za ta makance ta daina gani haka za ki ci karenki babu babbaka ba tare da wani ya kawo miki cikas ba. Kuma daga wannan lokacin hatta uwar da ta kawo ta duniya ba za ta sake tambayarta ba, yadda matacce ke mantawa da rayuwar baya haka duk wanda ya santa zai manta da shafinta." Umaima ta yi masa jinjina da hannu. "Na gode sosai Bamaguje faɗi kowanne irin tukwici kake buƙata." Bamaguje ya saki murmushi, "Ki je Umaima zan fanshi aikina a cikin masarautarku." Umaima na gama sauraronsa ta miƙe ta ƙarasa gaban Maimuna da ke zaune kamar butum-butumi, ƙaramar wuƙa ta saka ta ƙwaƙwalo idanunta ta watsa cikin wani koren ruwa kamar yadda Bamaguje ya faɗa mata. Ta koma gabansa ta yi masa sallama da faɗin duk abin da ake ciki za ta sake ziyartarsa. Ta rungume littafin a jikinta hannunta ɗaya riƙe da Maimuna na biye da ita kamar raƙumi da akala. Duk wani abu da take gudanarwa na siddabaru sai da ta gudanar babu jimawa sai ga su a cikin ɗakinta a tsaye. Kai tsaye uwar ɗakinta ta wuce da Maimanuna ta buɗe wani akwatinta na ƙarfe da take ajiyar abubuwanta na sirri ta ajiye littafin, sannan ta koma falo ta zauna tana ta zuba murmushi don gani take ƙiris ya rage haƙonta ya kai ga cim ma ruwa.

   Bayan fitar Fulani Umaima daga sashen Fulani babba, Jakadiya da kanta ta ɗan tattara wurin. Ta leƙa madafa tana tambayar su Baraka ko ruwan zafin ya tafasa, a daidai lokacin ta same su sun fara kwashe ruwan. Bayan an zuba aka kai banɗakin Fulani babba, shi kuma jaririn Jakadiya ta zauna ta sulle shi tas. Sai da gari ya waye tangararan sanna Jakadiya ta ɗauki Yarima ta wuce da shi turakar Mai martaba. Farinciki fal fuskarsa ya karɓi jaririn yana jin son shi a zuciyarsa don ya jima yana mafarkin samu ɗa namiji. Huɗuba ya yi masa da suna Abubakar sannan ya ba wa Jakadiya ta mayar da shi, Jakadiya na mayar da shi Fulani ta rungume jaririnta suka kwanta bacci. Jakadiya da kanta ta sanar da Baiwa Zainaba a kan duk wanda ya zo mata barka a ce masa tana hutawa. Sai a lokacin ita ma Jakadiya ta wuce can sashensu na Bayi ta samu ta yada haƙarƙarinta don ta yi ramuwar baccin daren da ba ta yi ba.

SHU'UMAR MASARAUTAR CmpltWhere stories live. Discover now