FREE PAGE.Asmy b Aliyu
1...
Mamma ta tsaresa da ido, banda faduwa babu abunda gabansa keyi yasan dai zance ɗaya ne na aurensa da Khairiyya taya zai yiwa Mammah bayanin baya yiwa Khairiyya soyayyar Aure? Da wane ido zai faɗawa Mammah ba sau ɗaya ba ba biyu ba,ba ukku ba suka kwana gado ɗaya da Khairiyya?
"Junaid ya kamata a fara maganar aurenka da Khairiyyah, ko a gidanka zata iya karasa karatunta a haka wannan zaman da kake haka yana damuna kasan lalurarka Junaid kara kayi aure ka tara zuri'a tsarkakku ba irin ya'yan bisa titi ba karka zubar da ya'yanka akan titi dan Allah Junaid." Mammah ta faɗa da wani irin karaya a muryarta, karo na farko da ya kasa kallon mahaifiyarsa karo kuma na farko da yaji wata irin kunyar Mamma da tazo ta lullubesa bawai Mammah bata san zununbin da yake aikatawa ba ne, sabida tafi kowa sanin matsalarsa shiyasa bata taɓa damuwa da kalar kaddararsa ba, tasan mazan ma akwai masu jinsi kala-kala.
Junaid Dikko yana cikin mazan da basu iya riqe kansu koda na kwana ɗaya ba tare da macce ba wata irin halitta ce ajikinsu ta daban. Ya ɗago rinannun idonsa yana kallon Mamma, da wani yanayi a muryarsa yake fadin. "Mamma ki daina damun kanki dan Allah kin san lalurarki na hawan jini, ba daga bangare na bane daga ɓangaren Kairiyya ne tace sai ta gama karatunta sai ayi maganar aure, shekara ɗaya ya rage mata." Dan Allah ki daina damar da kanki da lalurata Mamma, ki cigaba da yi min addu'a kinji Mamma."
Idan na rasaki ban san aya Rayuwa zata zomin ba.idan batare dake ba,
Ya kama hannunta ya subbaci hannun,ya sakar mata murmushinsa mai qara saka mata mugun son yaron nata da wata irin kaunarsa aranta ,ya miqe tsaye yana faɗin."mamma a haɗamin abincin dare mai rai da lafiya yau gida zan kwana ,ban shirya karbar fadan Abba, ba tunda shi kullum yaro yake dauka ta." Ya faɗa yana wani damuke fuska.
Murmushi kawai Mammah,tayi masa yasa kai ya fice daga parlorn na Mamman da wani irin takunsa mai jan hankali da wata irin izza a tattare dashi...Yana fita daga parlon kai tsaye ya nufi motarsa jaguar da aka fitar aka wanke kallon farko da zakayiwa motar kasan kuɗi sun zauna jikin motar sai ya'yan wane da wane kawai ke hawanta. Ya shiga motar ya tada da sauri maigadi ya buɗe masa get ya fice daga gidan, wayarsa ya ɗauko Iphone 14 pro max, still har lokacin maganganun Mamma, sunki fita daga kansa bai san sai yaushe zai iya buɗe baki ya faɗa mata bazai iya auren Khairiyya ba, auren su ma bazai yuyu ba, dan kuwa idonsa a buɗe nata a buɗe duk da a bangaren Khairiyya kuwa ita gani take kamar aurenta xaiyi kamar yadda Mamman keso, dialling wata lamba yayi mai ɗauke da sunan Sarah cikin kankanin lokaci aka ɗaga wayar.
"Mr. Dikko!" Ta faɗa da wata irin kasallaliyyar murya mai dauke da jan hankali,
"Ki sameni a guest house yanzu."
"Me zai hana ka biyo school ka ɗauke ni ina hostel fa, kasan kuma da nisa."
Da sauri ya katseta yana faɗin "Ki samu adaidaita." Da haka ya sauƙe wayar baya son doguwar magana, har ya karasa gidansa na sirri tunanin Mamma na ransa, sanin halin Junaid din ta shiga shirya kanta da sauri, Ruky ce ta dubeta tana faɗin “Kedai Sarah akan gayen nan sam baki da aji dama ace soyayya kuke da sauqi amma iyakarsa yayi amfani dake shi kenan amfanin ki ya qare a wurinsa sai kuma wani lokacin shaye da toka.”
Sarah ke faɗin “Ina da sa'a ma a haka tunda Junaid Dikko ya haɗa gado dani.” A fusace tabar room din nasu Ruky ta kwaɓe baki ta bita da kallo cike da wani irin kishin kawarta ta, da gaske tana da sa'a kamar yadda ta faɗa din tunda har Junaid Dikko ya haɗa gado daita.#ASMY B ALIYU
#BA(Secret Relationship)
Love, Romance and destiny
#Junaid Dikko