LAST FREE FAGE

115 1 0
                                    


https://arewabooks.com/u/asmybaliyu

FREE FAGE.
Asmy b Aliyu

10.

Da kansa ya shiga restaurant yabarta a mota sanin halin Amaah ɗin ya dawo da kusan ledojin biyu a hannunsa, back seat ya buɗe ya saka ledojin, makaranta suka koma kusan a cikin motar sukaci abincin, duk yadda Fu'ad yaso ya sauketa a gida kin yadda tayi tace masa driver zaizo ya ɗauketa, sannan ta faɗa masa gobe zatazo hostel sai yazo ya ɗauketa anan ɗin. Ya rigata wucewa itama bata daɗe ba driver yazo daukarta, koda ta koma gida ta samu su Abba sun dawo ta yiwa Abba sannu da zuwa da kuma Yaya Junaid dake zaune cikin parlorn Mamma yana danna wayar hannunsa. Da ido ya bita ganin shigar dake jikinta, wani irin sanyi taji aranta daman tun a hostel ta cire veil ɗin jikinta ta mayar jaka. Washe gari ya kama Wednesday sai kusan 10 ta fita daga gidan daman kuma duk yinin ranar lecture ɗaya zasuyi 2to4. Drivern Junaid ne ya sauketa a makaranta, tun kafin su tafi dama ta shiga ɗakin Mum ta faɗa mata tayiwa driver bayanin ita zataje da yamma za'a zo da yamma a ɗauka ta suna da bikin Yar kawarta kuma Abba yasan da bikin. Haka Mum ta fita ta faɗa masa. Ƙarfe 2 suka fito daga lecture Rufy ta rakata siyayyar gift ɗin da zata bawa Fu'ad ɗin wanda daman duk qarshen wata Alh Dikko ya ware kuɗin da yake turawa duka ƴaƴan nasa har Junaid da kuma matansa, so kuɗi ba matsalar Amaah Dikko bane ba. Kusan shaddar 50k ta daukarwa Fu'ad ɗin kala biyu sai kuma Agogon Rolex da kuɗinsa ya kai 70k karshe ta haɗa masa da turarruka masu tsadar gaske, Rufy ta gyaɗa kai tana faɗin. "Lallai kina ji da Fu'ad ɗin nan Besty, irin wannan hidima haka? kusan fa 200k kika kashe masa fa." Murmushi Amaah Dikko tayi tana ɗan juya ido take faɗin. "Kin san kuɗi ba matsala ta bace kuma kin manta Fu'ad yadda yake a wajena ne?" Gyaɗa kai kurum Rufy ta shiga yi, haka suka dawo hostel ɗin, da yammah suna shirin tafiya Amaah ta sake yin wanka riga da wando ne a jikinta, sai maroon Turkish abaya da ta ɗora kanta gamida yin rolling kanta da veil ɗin abayar tayi wani irin kyau na ban mamaki. Baki Rufy ta saki tana kallon Amaah. "Kice min mafarki ne Besty, badai da wannan shigar zaki tafi birthday ɗin Fu'ad ba?" Da mamaki a fuskar Amaah ke faɗin. "Toh a ya kike so na tafi Rufy?" Tace, "Nifa na zata da riga da wandon nan kaɗai zaki tafi, wallahi baki ga yadda kikayi kyau acikinsu ba dan sun fito da ainahin surar da Allah yayi miki. Please dan Allah ki cire wannan abar da kika wani ɗora." Da mamaki Amaah ta shiga girgiza kai. "Ni ake son gani a wajen ko jikina Rufy? a hakan ma nayi ƙoƙari wannan shine karo na farko da zanje party fa." Rufy tace. "Amman wallahi xaki xama ƴar kauye a wajen." Shiru Amaah tayi ba tare da ta qara tankawa Rufaidah ba, itama Rufy ɗin bata qara magana ba. Sai kusan shida har da rabi Fu'ad ya shigo cikin makarantar, wayar Amaah ya kira yace gashi cikin makarantar, ta sauke wayar ta kalli Rufy da ta haɗe cikin riga da wando tamkar ba ƴar musulma ba, ga kalabar gashin doki da tayi dake ta faman reto a tsakiyyar bayanta. "Fu'ad ya qaraso." Rufaida ta kalleta tana faɗin. "Ku tafi zamu taho tare da Jawad." Kasancewar Jawad ɗin abokin Fu'ad ne kuma boy friend ɗin Rufy ne. A tsorace Amaah ke faɗin. "Ba sai mu tafi tare ba sai ya samemu duk acan." Amaah Dikko ta faɗa da ɗan tsoro a murya ta. "No kawai ku tafi nayi masa alkawarin zan jirasa idan yazo ya tarar bana nan zaiji ba daɗi." Har bakin mota Rufy ta raka Amaah da duk jikinta ya gama yin sanyi, wani irin strange feeling ta rinqaji a duk kan cikin jikinta tamkar bata da lafiya. Tunda suka fito Fu'ad ke kallonta har Rufaidah ta buɗe back seat ta saka bag ɗin dake ɗauke da gifts ɗin Fu'ad ɗin. Ɗan hugging ɗinta Rufy tayi ta ɗago gamida ware mata ido tana faɗin. "ya naga jikinki duk yayi sanyi ke kin san fu'ad bazai cutar dake ba idan kin hango kalar son da yake yi miki. Dan Allah kiyi ƙoƙari kiyi enjoying wannan ranar tare dashi, karki bawa Fu'ad kunya a idonsu Mufeeda, sai na qaraso nima yanzun zan kira Jawad." Rufy ta faɗa tana buɗewa Amaah gaban motar ta shiga ta rufe ƙofar, da suka haɗa ido da Fu'ad sai ya sakarwa Rufy wani irin murmushi babban yatsansa ya juya alamar ya gode. Tunda suka ɗauki hanya bata yi masa magana ba, a karo na farko cikin rayuwarta da taji wani iri akan kebewa wuri ɗaya da Fu'ad, cikin minti talatin suka karasa cikin gidan mahaifinsa dake cikin G.r.a., banda faɗuwa babu abunda gaban Amaah yake yi kuma tsoro ya hana ta tambaya Fu'ad ɗin nan ina ne? Dan beyi kama da hotel ɗin da yake magana ba akan acan za'a yi birthday party ɗin nasa. Maigadi yazo da sauri ya buɗe masa gate, a hankali ya nufi wajen da aka tanada dan parking ɗin motoci ya kashe motar ya juya yana kallonta yana hango bayannen tsoro cikin fuskarta, lokaci ɗaya ya kamo hannunta yana murzawa cikin nasa a hankali, wani irin yanayi ta tsinci kanta cikinsa ga wani miqewa da taji tsintar jikinta nayi. "Nan ne asalin gidanmu baby tunda tsoro ya hana ko ziyara ki kawo min, kamarki ace baki san asalin gidan mahaifina ba?" A hankali ta zare hannunsa anata tana ɗan yarfi da hannun jin yadda yayi mata wani irin nauyi. Buɗe ƙofar motar yayi yana faɗin. "Muje part ɗina na canja kaya sai mu tafi." Girgiza masa kai ta shiga yi cikin rawar murya take faɗin. "Zan jiraka a mota Fu'ad." "Amaaah please!" Ya faɗa da bayyanannen sauti a muryarsa, da haka ya saka hannu ya buɗe motar ya fito ya zagaya ya buɗe mata nata ɓangaren, da ido take roqonsa lokaci ɗaya ya haɗe rai. "In har bazaki shiga part dina ba kawai muje na mayar dake gida bama sai kinje birthday ɗin ba na yafe zuwan." Ya faɗa da fushi a muryarsa ganin lokaci ɗaya yadda fuskar Fu'ad ɗin ta juye yasa ta fito daga motar, back seat ta buɗe ta ɗauki bag ɗin, hannunta ya kama suka nufi wani bangare na daban ma'akanta gidan sai gaishesa suke cike da girmamawa suna mamakin wannan kalar rayuwar da Fu'ad ɗin keyi. Har ya ƙarasa dasu ainahin part dinsa wanda baxan iya misilta muku kyansa ba kallo daya xakayiwa wurin kaga part din dangata, a falo taja ta tsaya. "Kaje ka shirya zan jiraka a falo." Ta faɗa tana kallonsa, ɗaga kai yayi kawai ya nufi hanyar stairs, sai da ya bacewa ganinta sannan ta zube a ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da parlorn tana sauke numfashin da take riqe dashi, banda faduwa babu abunda gabanta keyi, ta fito da wayarta dake cikin hangbag ɗinta taga har lokacin sallar magrib ya gabato. Sai kusan 7 har da minti goma Fu'ad ɗin ya fito cikin wandon troser da kuma farar shirt da ta kama jikinsa sosai da sarqa a wuyansa irin wanda ƴaƴan manyya ke sakawa, sai zuba kamshi yakeyi. Har ya qaraso cikin parlorn bata kallesa ba tsayawa yayi agabanta yana qare mata kallo. "Ke bazaki shirya ba?" Ta dago kanta ta zuba masa idonta ta girgiza kai tana faɗin. "A shirye nake Fu'ad dare yanayi mu tafi." Ta miqe tsaye ta miqa masa bag ɗin hannunta tana faɗin. "Ga gifts ɗinka." Ita da bag ɗin da hannunta ya haɗa ya rike kafin ya jawota cikin jikinsa duka yana sauke mata numfashi a cikin wuyan ta, duk yadda taso ta kwaci kanta kasawa tayi dan riqon da yayi mata bana wasa bane. karo na farko da wani ya riqeta kamar haka a jikinsa, banda kadawa babu abunda jikinta keyi, tana jin yadda ya riqe kugunta sosai. "Kin san ina sonki ko?" Ya faɗa da wata irin murya da Amaah ta kasa fassarawa. Ta ɗago tana kallon cikin idanunsa da suka kankance lokaci ɗaya suka canja kala da yanayin su ke baiwa Amaah Dikko tsoro. "Mu tafi Fu'ad." Ta sake faɗa cikin rawar murya. yatsansa ya saka yana zagaye bakinta dashi sai kuma ya saketa a hankali yana ɗan jada baya da murmushi akan fuskarsa yake faɗin. "Am so sorry kin san idan ina gabanki kasa controlling ɗin kaina nake yi, muje." Ya faɗa yana barin bag ɗin da ta bashi a kan kujera yace idan ya dawo zai duba. Sai da suka bar cikin gidansu Fu'ad ta samu ƴar natsuwa. (Katsina Trousit Lodge) Har ya gama parking motarsa acikin parking lot Amaah bata motsa daga inda take ba, haɗe jikinta tayi wuri ɗaya tana jin sanyi na shiga jikinta a hankali haka tana jin wani yanayi mai alamar zazzaɓi yana san sauka ajikinta. Da ido Fu'ad yake kallonta. "Are you ok?" Ya faɗa yana zuba mata idanunsa, ta kallesa tana ɗaga kanta take faɗin. "Awa ɗaya kawai Fu'ad, da kayi cutting cake zan tafi." Ta faɗa murya can ƙasa. Fu'ad ya wani yamutse fuska yana faɗin. "Kice min wasa kike min? duk tarin laifin da kikayi min na hadiye abuna banyi magana ba karki ɓata min rai." Kallonsa take alamar tana son taji laifin da tayi ya wani furzar da iska a bakinsa yana faɗin. "Kalli shigar da kika shigo wajen nan dashi, Abaya ce fa ajikin ki Amaah sai kace ba girl friend ɗina ba? any way tunda kin zo banda matsala da wannan." Ya faɗa yana balle marfin motar ya fito. Zagayowa yayi ya buɗe mata murfin motar banda faɗuwa babu abunda gabanta keyi karo na farko da ƙafarta ta tako cikin hotel da sunan zuwa birthday ɗin saurayi. Kai tsaye hannunta Fu'ad ya riqa ɗayan hannunsa kare da waya, entrance ɗin shiga hotel ɗin suka dosa......

*_Anan na kawo karshen free pgs mai son cigaban littafin ya nemini da wannan lambar_* 08086207764

BOYAYYAR ALAƘA is 500
Account Details
0004157137
Jaiz bank
Asma'u Buhari Aliyu
Shaidar biya ta 08086207764

Katin wayar MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730

#ASMY B ALIYU
#BA(secret Relationship)
#fu'ad
#Amaah Dikko

BOYAYYAR ALAƘA (the secret relationship)Where stories live. Discover now