BOYAYYAR ALAƘA 4

80 0 0
                                    

FREE PAGE.

Asmy b Aliyu

4..

Kusan cin karo sukayi da sauri Amaah Dikko taja da baya tare da zaro ido, bata taɓa tunanin Junaid Dikko yana gida a irin wannan lokacin ba, tun daga kanta har zuwa kafafunta yakebi da kallo, Atamfar super wax ce ajikinta wanda aka yi mata ɗinkin fitted gown ajikinta wanda ya lafe cikin jikinta haka rigar ta ɗan dage mata, har ana hango sarƙar ƙafar da ta sa ka a ƙafarta ta daban, idonsa suka sauƙa a kan sarqar kafarta ta, ya sha ganin sarqa a kafafun kadangarun bariki yana ganin kyanta ga mata, wanda yayi alƙawarin matar aurensa zatayi masa kwaliyya dashi acikin gidansu kawai idan zasu fita baya buqata, a wani irin haukace ya ɗago kansa yana kallon Amaah Dikko wacce take kanƙame jikin kofa da ɗan qaramin veil ɗinta(Chantilly) wanda ta ɗora akan kafaɗa, ya tsaida idonsa cikin fuskarta tamkar mai son gano wani abu, ganin wani mugun haske da ta qarayi har farin nata yaso yayi yawa kuma yana kashe ido, ga kananun pimples da suka fara taruwa a fuskarta da alama tana using da mayyukkan dake qara haske fata, tana ganin Junaid ya saka hannu a wandonsa yana ƙoƙarin ciro belt din jikinsa ta zubara ta yar da qaramar handbag ɗinta ta juya ta koma cikin Parlon da gudu tana kwalawa Mamma ƙira da mum ɗinta, daman Mamma na kitchen Mum dake sama ta riqa jin ihun Amaah wacce yanzun nan tayi mata sallama akan zata shiga school, da sauri take saukowa kan stairs ɗin tuni Amaah Dikko tayiwa kanta maɓoya bayan Mamma, still Junaid dikko bai fasa binta ba
"Metayi da safiyan nan zaka wani ciro belt irin ga jaka ka samu? Waini yaushe xakayi xuciya ka daina shiga sabgar ƴaƴana Junaid Dikko?" Mum tayi maganar so pissed up.
Wani irin fisgota yayi a bayan Mamma, saukar belt taji a bayanta, a fusace Namma, ke faɗin "Wai meke damunka? Me tayi maka??" Mamma ta jeho masa tambayoyin lokaci ɗaya rai a bace, shima rai a ɓace yake faɗin "Kalli da shigar da za ta je makaranta tamkar ba yar musulmi ba kalli shegen mayafin da ta saka Mamma? Kalli  ƙafanta sarqa ne ta ɗora ki kalli face ɗinta yadda ta canja Mamma? Duk farin da take dashi bata godewa Allah ba sai tayi bleaching dan tana yar iska?" ya faɗa a tsawace.
Wata daria Mum, ta fashe dashi tana tafa hannayenta tana ganin qarfin hali wai Junaid ke faɗin wasu yan iskane "Muje ki tattara mayukkun da kike shafawa ki kwasosu duka, haka duk wata tsinannar sutura da kike sakawa ki tabbata kin fito dasu yau ɗin nan."
A tsorace Amaaah ta juya ta nufi stairs sai famar hawaye take tana tsinewa Junaid Dikko aranta, wannan takura har ina? Itama Mum tama kasa magana sabida bakin ciki dan duk ihun da zatayiwa Junaid bazai saurareta ba, ita kanta tana ɗan shakkarsa.
Kallo ɗaya zakayiwa ɗakin kaga ɗakin ƴar gata babu abunda Babu a dakin, tun daga Tv , fridge, a tsorace ta qarasa gaban mirror ta kwaso duka mayukkan da take using dasu, hannu Junaid ya saka ya ɗau ki daya ya shiga dubawa "Ki jawo ɗaya daga cikin trolley ɗinkin ki zuba." Babu musu tayi yadda yace dan har lokacin zafin belt ɗin da ya zuba mata bai gama sakinta ba, haka ya sakata a gaba ta fitar da duk wani sutura da tayi ɗinkin banza, haka ya tattara duka veils ɗinta ya zuba acikin bag din. Ya kalleta yace ta ɗau ki wasu kayan ta shiga bedroom ta canjasu yanzun nan babu musu tayi yadda yace, still yana tsaye yana jiranta ta fito ta saka rigar da ta cire cikin bag ɗin tamkar zatayi kuka ganin duka rabin suturarta Junaid Dikko ya kwashe, wani mayafin ta ɗauko zata saka, wani mugun kallo yayi mata yace "Daga yau daga yanzun nan na haramta maki saka mayafi idan zaki school hijab." Tamkar zatayi kuka duka hijab dinta babu ƙananu har qasa suke sallah kawai take dasu "Bani car key din motarki?" Ya faɗa fuska a ɗaure, miqa masa tayi tuni hawaye sun fara zuba cikin fuskarta da haka ya sakata gaba still har lokacin Mamma da Mum na cikin parlorn ganin Junaid Dikko ya fita da trolley ɗaya, a fusace Mum ta qaraso tana kallon Amaah tun daga sama har kasa ranta yayi balain ɓaci, a mugun tsawace take faɗin "Gidan ubanwa zaki tafi da wannan hijab ɗin ba makaranta zakije ba?" Tuni Amaah Dikko ta kasa riqe kukanta ta fashe da kuka take faɗin "Yaaya ya hanani saka mayafi."
"A saboda yana ubanki ? Maza cire shegen hijab ɗin nan tunda ke ba dangin su malam shehu bace."
"Ke wuce muje na saukeki a makaranta kina ɓata min lokaci!" Junaid Dikko ya faɗa a mugun tsawace, a wani kalar razane Amaah Dikko ta juya tabi bayansa, with so much shock Mum kebin Junaid da Amaah da kallo har suka fice daga falon, a wani irin haukace ta nufi bedroom ɗinta wayarta ta ɗauka ta shiga ƙiran Abba, banda tafasa babu abunda zuciyarta keyi. Abba yana ɗaga wayar ta fara da faɗin "Aliyu zanyi maka wata tambaya??" shi kansa Abba sai da yaji wani iri bazai iya tuna wane lokaci Mum ta ƙira sunansa kai tsaye ba "Ina jinki ai kunne ke ji." A kufule take faɗin"Da ni da kai muka haifi su Amaah ko Junaid dikko ya haifa mana su?"
"Meya faru Rafee'a?" Duk  da Abba yasan kwanan zance a fusace ta shiga yi wa Abba bayanin abunda ya faru, idan na dawo gida zamuyi magana Rafee'a "Yanzu akwai aikin da nake." Ba tare da Abba ya qara bata damar yin magana ba ya sauke wayar gefen bed Mum ta koma ta zauna ta ɗau ki ƙafa ɗaya ta ɗora a ɗaya tana wani irin girgizawa me zatayi ta kun ta tawa Junaid? Me zatayi masa yayi zuciya ya fita sabgar ƴaƴanta yadda tasan Junaid Ali Dikko da shegiyar zuciya bata yi tunanin duk maganganun da take yaba masa zai iya zuciya yabar kula ƴaƴanta, tunda ta sansa haka yake tamkar mahaifinsa da shegiyar xuciya da bakar kafiya babu wanda ya isa ya tankwasa su akan ra'ayinsu watarana ma har yafi mahaifinsa.
Har cikin makarantar ya kaita idonta har sun kumbura sabida kuka, yanzun ta ina zata fara shiga school? Da hijab har kasa ai sai ta zama abun daria da kaskantarwa ita addu'ar ta ma ɗaya Allah yasa Fu'ad bai shigo ba.
Ya kashe motar ya kalleta fuskarsa babu wani walwala da wani precious acikin fuskarsa wanda ke gigita kannensa, a natse yake faɗin "Wannan ya zama ranar na farko na qarshe da zaki fita da mayafi zuwa makaranta." A duk ranar da na kamaki da mummunan shiga da sunan zuwa makaranta na rantse da Allah kin gama zuwa jami'a har abada." Kalmar data gigita Amaah Dikko kenan gyada kansa yayi yana kara tsareta da idonsa alamar da gaske yake, tuni hawaye suka fara taruwa a idanunta
"Idan an tashi ki ƙirani zanzo na daukeki daga nan zamuje ki zabi wasu kayan akai wajen mai ɗinkin." Ɗaga kai ta shigayi kurum tamkar wacce akayiwa shegen duka, sai da ya bata izini ta fice daga motar tana daga tsaye har yabar wajen, da gudu ta koma bayan bishiya ta fashe da wani irin kukan bakin ciki, wayarta ta ciro ta shiga ƙiran wayar Rufaida.
Ta na ɗauka cikin rawar murya take faɗin "Kina hostel?" Daga can bangaren Rufy ke faɗin "Yanaji muryarki wani iri baki da lafiya ne?"
"Ki amsa ni Rufy dan Allah."
"Ina hostel." Kashe wayar tayi ta maida cikin jaka, miqewa tayi tsaye tana rufe rabin fuskarta da hijab ta fara tafia a hankali zuwa hostel wajen Rufy. Amaah na shiga dakin nasu, Rufy ta wani riqe baki tana faɗin "Yau kuma Malama Amatullah kika zama?" Sai kuma ta fashe da daria tana kallon Amaah Dikko, daga sama har ƙasa dan bata ma lura da yanayin fuskar Amaah ɗin ba data canja kala sabida kuka. gefen bed Amaah ta zauna tana cire hijab ɗin jikinta sai lokacin Rufy, taga yanayin fuskar Amaah ɗin yadda ta ɗan kumbura, wani kalar zaro ido Rufy tayi tana faɗin "Ke meya sami idonki?" Hawayen bakin ciki suka yi saurin fitowa daga cikin idanun Amaah Dikko ta ɗaga kai tana kallon Rufy, wacce ke jiran karin bayanin anan ta kwashe komai ta faɗa mata yadda Junaid Dikko yayi mata, cike da jimami Rufy ke faɗin "Ni kuma kin san Allah komai na yayan nan naki burgeni yake yadda yake wani tsare gida yana muzurai, ya subahanallah komai nasa tafia yake dani, irin su kawai ki zuba ido kiga yadda zasu riqa tarairayar matar aurensu suna bata wani special kulawa babban abun jan hankalina tattare dashi, kishinsa.”
Wani irin kallo Amaah ke bin Rufy,dashi bata san waye Junaid Dikko ba shi yasa ta saki baki tana yabonsa “Ki bani wani mayafin na saka Rufaidah ki daina yimin zancen sa.” Ta faɗa sounding so very Angry a muryarta, murmushi kurum Rufy din tayi tana faɗin “Ki duba cikin kayana ki zabi kalar kayanki ni wanka zan shiga kiranki ya tsayar dani." Aran Rufy ,take faɗin"Bazan fasa yaba Junaid Dikko ba ƙawata sai dai kiyi hakuri wallahi." Ai da tana samun damar wannan guy ɗin da tayi soyayya dashi koda na wucin gadi ne, da matsayinta ya zarce wanda take dashi yanzu na soyayyah da Junaid Dikko...

#ASMY B ALIYU
#BA(secret Relationship)
#Love, Romance and Destiny
#Junaid Dikko
#Amaah Dikko

VIP 1k
NORMAL GROUP 500

BOYAYYAR ALAƘA (the secret relationship)Where stories live. Discover now