FREE PAGE
Ta sanyo kanta cikin parlorn shikuma ya saka nasa kan zai fito sukaci karo da juna, dan ja da baya yayi itama taja da baya ta ɗaga kanta tana kallon sa, yana sanye ne cikin shadda milk kansa babu hula kusan lokaci ɗaya suka saki murmushi, duk da yanayin da zuciyarta ke ciki “Amaah Dikko." Ya faɗa wearing a loverly smile shimfiɗe akan fuskarsa.
Yanayinta kawai ya tabbatar masa daga makaranta ta fito, kwana biyu ko gaisuwa babu daman nine ke ƙiran naki idan ban ƙira ba ke bakya taɓa tunanin ki ƙirani, ta ɗan shagwabe fuska tana kallon Abdul-hakeem Datti yadda ya tsaya a gabanta tamkar ya maidata ciki dan so, bai taɓa son wani a rayuwarsa ba baya ga iyayensa wanda bai bude idonsa da saninsu ba, kusan rayuwarsa a hannun baffansa yayi ta, abu ɗaya zai iyacewa kasancewarsa acikin zuri'a dikko family yawan ganin Amatullah Dikko a koda yaushe ya saka masa zazzafar kaunar Yarinyyar, wasu lokuttan yakan karyata kansa da haka kasancewar yasan da a kauye ne da yanzu yana da sa'an Amaah dikko tunda can auren wuri suke, kusan a idonsa Yarinyyar ta girma, bai taɓa faɗawa kowa wannan sirrin ba dan ko abokinsa Junaid da suke raba damuwarsu a tare bai taɓa sanin wanann sirrin na nasa ba dan bai taɓa furtawa ba, yasha jin yadda Junaid Dikko ke ririta kannen nasa, yasha jin sa yana faɗin kannensa bazasu kula kowa ba sai sun gama karatun jami'a hasalima shi zai zaba masu mazajen Aure, sanda yaji haka bai san sanda ya ɗaga kai ya kalli Junaid Dikko ba tuni ya harbo jirgin abokin nasa
"Meyasa kake gudun duk wata hanyar da zata ɓata kannenka? Amman kuma kai kake ɓata kannen wasu? Ko kana tunanin zunubbanka bazasu shafi kannenka ba Junaid? Lokaci yayi da zaka dawo hankalinka,
ƙannenka girma suke kullum qara tasawa suke,
zunubinka yana zagaye dasu, idan aure shine maganin matsalarka kayi auren ka samu zunubbanka su rage."
A duk lokacin da Hakeem ya ɗauko masa irin wannan zancen ji yake tamkar zuciyarsa zata rabe gida biyu, idan kuma wani ya taɓa masa kannensa fa? Dan tsaf zan iya kai karshen rayuwar duk wanda yayi kuskuren taɓa kanne na.
"Yaaya Hakeem." Kalamanta ne suka dawo dashi daga tunanin sa, ɗage mata gira yayi alamar yana jinta “Oh nikam sau wawa nake kiranka dan Allah amman duk sanda muka haɗu sai kayi min gorin bana kira."
“Ƴanxu dai na yadda kina ƙirana, ya makarantar ya kuma karatu akwai daɗi? Samarin ki kuma nawa?"
Wannan karon zuba masa idanunta tayi tana ɗan waresu akansa, ta ɗan turo baki a hankali take faɗin “Wannan tambayoyi sunyi yawa, gaskiyya zan amsa maka biyu mubar ɗaya."
Tacigaba da kallanshi tana cewa “Makaranta Alhmdullahi, karatu kuma da sauƙi, kasan mu sabon shigane sai a hankali." Ta qarasa maganar cikin sanyi muryarta dake narkar da zuciyar Abdul-hakeem,
"Baki isa ba duka zaki amsa min." Sai ta nufi cikin parlorn tana waiwayensa tana faɗin “Zuwa wani lokacin Yaaya." Da wani kallo ya bita har ta bacewa ganinsa.
Mamma ta samu a parlor wacce shigowar Abdul-hakeem ce ta fito da ita parlorn, yazo ne ya kawo mata drugs dan har lokacin wata irin mura ke damunta mai zafin gaske, Amaah ta gaisheda Mamma wacce ta bita da ido tana kallon yadda idonta suka dan faɗa "Lafiyan ki dai kou?" Mamma ta faɗa cike da kulawa tana kallon Amaah "Kaina ke ciwo." "Kije kiyi wanka kici abinci kisha magani Allah ya qara sauƙi." Ta amsawa Mamma da Ameen ta miqe tsaye ta nufi part ɗin su, kai tsaye ɗakinta ta nufa tun a mota take ƙiran wayar Fu'ad amma a kashe har wani zazzaɓi-zazaɓi taji yana ƙoƙarin rufeta lokaci ɗaya, kayan jikinta ta ɗan rage, kai tsaye toilet ta faɗa dan yin wanka, tana fitowa ta faɗa gado.
Har bayan magrib tana ta kwanciya a ɗaki kuma har lokacin wayar Fu'ad a kashe ta rasa inda zata tsoma ranta dan taji sanyi ko abinci kasa ci tayi, daman idan suna faɗa da Fu'ad kasa samun sukuni take watarana har dasu rashin lafiya, kusan soyayyar tasu rabinta faɗa ne a cikinta, kuma duka fadan da zasuyi Fu'ad ne marar gaskiyya sai dai ita ta sauƙa ta basa hakuri, ko shi yayi mata laifi bazai taɓa bata hakuri ba.Kai tsaye ya faɗa mata shi bazai iya baiwa macce hakuri dan yana sonta ba.
Turo ƙofar room ɗin nata da akayi ne yasa ta qara manna kanta jikin pillow duk da ba barci take ba, tana son zama ita ɗaya, jin Mum ta ƙira sunanta ne yasa ta ɗan buɗe idonta da suka ƙanƙance, Mum ta zauna a gefen bed tana kallon Amaah ɗin da wani yanayi da take hangowa acikin fuskarta, itama Mum ɗin dawowar ta kenan fita tayi ƴar kawarta ce zatayi aure to sune manyyan iyaye a wajen "Lafia kikazo kika kwanta a ɗaki? Assha tace tun da kika dawo makaranta baki zauna parlour ba meke damunki?" Hawaye taji suna cika idonta a hankali, kirjinta har wani zafi taji yanayi mata.
Duk yadda taso Mum karta ga hawayenta kasa riqesu tayi, baki buɗe Mum ke kallon Amaah har zata buɗe baki tayi magana da sauri Amaah ta shige jikin Mum ɗin gamida fashe da kuka mai ciwo wanda ke fitowa daga can kasan zuciyarta. Mum ce ta ɗagota a ruɗe tana faɗin "Wai laifiyan ki da bazakiyi min magana ba?"
Mum ta ɗan yi maganar a fusace "Mum daman Rufy zatayi birthday jibi shine na faɗa mata gida baza'a barni ba shine tayi fushi." Shiru Mum ɗin tayi kafin tace "Saboda sakarci kan wannan maganar zaki zo ki wani ɗaga hankalinki? Wai meyasa kike abun wa waye?Jibi idan kika shiga school ɗin sai ki kwana a hostel wajen Rufaidah ɗin kuyi party ɗinku a natse. Ni nasan yadda zanyiwa Abbanku bayani." Wani sanyi Amaah taji aranta duk da tana jin qaryar da tayi tana danne mata kirji "Sai ki tashi ki fito kici abinci ga ɗinkunan ku na Anko da na karbo maku wajen Salma tace ranar Friday za'a saka ranar da ake dinner." Kusan tare suka fice ɗakin da Mum kai tsaye kitchen ta nufa, sai a lokacin ta dawo hankalinta, tasan tana jin yunwa, text tayi ma Fu'ad na ban hakuri akan zataje birthday ɗinsa_Dan Allah ka ƙirani bazan iya barci ba idan banji muryarka ba._ Har kusan qarfe 10 tana tsammanin jiran ƙiran Fu'ad ɗin dialling lambarsa tayi ta shiga sai dai line busy ake danna mata, kusan minti talatin ta qara gwada kiran still line busy, nan take zuciyarta ta bata da wata yake waya tura wayar tayi ƙarƙashin pillow tana jin wani abu na zagaye xuciyarta lokaci ɗaya, gaskiyyar Rufy ne da take faɗin Fu'ad yana da yammata sosai wanda suka fita wayewa da bariki idan zata waye ta kwato Fu'ad ɗin hannunsu toh, idan kuma zata zuba idone sai a tafi a haka, dan tana ganin kalar rayuwar da Fu'ad ɗin yake so ko ta ɓata yayi yanzu nan zata fara complain bancin yanzu kai ya waye......
"Ya dai bari idan ya aureni sai ayi haka."Amaah ta faɗa ma Rufy a wani lokaci can baya, Rufy batace komai ba sai ta taɓe baki ta ɗauke kai aranta take faɗin, mudai je zuwa Yarinyya indai Fu'ad ne duk wannan taurin kan naki zai sauke maki shi, haka zai ja ra'ayinki dan har lokacin Rufy kallon shasha take yiwa Amaah gata dai da kalar waye sai dai da suka zauna na ɗan lokaci zaka san babu wata wayewa a tareda ita.
Ssi kusan 12 ya ƙira dan har barci ya fara ɗaukarta karar wayarta ya tasheta Fu'ad ne mai ƙiran, ɗauka tayi ba tareda tayi magana ba dan har lokacin zuciyarta wani zafi-zafi take yimata "Bakiyi barci ba?" Ya tambaye ta can kasan makoshi "Har na fara kai ka tasheni, dawa kake waya Fu’ad?" Tayi tambayar da sanyi a muryarta “Da Jawad ne." Tasan karya yake yimata sai dai bata qara tada zancen ba sai cewa tai “Baka ga saqona ba?"
“Yes nagani...."
“Toh baka ce komai ba ko baka farin ciki?"
“Inayi sosai finally zaki haɗu da manyan friends ɗina."
"Uhm....” Kaɗai ta iya faɗa, hira ya riqa yimata sama-sama har sai da ya fara jin saukar numfashinta alamun bacci sannan ya katse wayar.
Washe gari da ƙarfinta ta tashi tamkar babu abunda ya faru ko da suka haɗu school da Rufy ta faɗa mata yadda sukayi da Mum daria kawai Rufy tayi tana faɗin "Da kyau yar gidana da alamar kin fara shigowa gari." Murmushi kawai tayiwa Rufaida a gefe kuma tana tunanin me zata siyawa Fu'ad a matsayin birthday gift ɗinsa, sai kusan 4 suka haɗu dashi fitowarsa kenan daga lecture daman ita yau 12 kawai suke da lecture shi ta tsaya jira, ta kwantar da kanta jikin seat na motar tana kallon cikin idanunsa "Yunwa kakeji Fu'ad kaga yadda kayi wani zuru-zuru?" Murmushinsa na gefen baki ya sakar mata ya tada motar yana faɗin "Muje muci abinci."
Gida taso tafiya amma sanin halinsa yasa tayi shiru bata qara faɗin komai ba.BOYAYYAR ALAƘA is 500
Account Details
0004157137
Jaiz bank
Asma'u Buhari AliyuKatin wayar MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730
#ASMY B ALIYU
#BA(secret Relationship)
#Amaah Dikko
#Hakeem Datti
#Fu'adVIP 1K
NORMAL GROUP 500