TRILLER

93 1 0
                                    

https://arewabooks.com/chapter?id=652902b16faabf649fa35f85


HEART BROKEN!



Zaunawa tayi daf dashi ƙafadarsu na gogar na juna ta miqa masa wayarta tana faɗin ya kalli design na card ɗin da ta zaɓa musu na bikinsu. "Mine wannan yayi duk kasa abubuwa basa sauri da yanzu an buga card ɗin nan na hana nace a jira ka." Kallonta kawai yake da wani irin expression acikin fuskarsa. Da kyar ya haɗiye wani abu da yaji ya tsaya masa arai. Ya kalleta cikin ido yake faɗin. "Amman kin san wannan wasa kike yi ko Khairiyyah? ina jin mun daɗe da gama maganar nan tun ba yanxu ba nace miki babu aure a tsakanin mu, meyasa kike da son kanki ne?" With so much shock ta buɗe ido, kallonsa take a haukace tana faɗin. "Kai zan fadawa ka daina yi min irin wannan wasan, please bana so ko ka manta da cewa an biya sadaki an kawo lefe auren mu sauran kwana goma masu zuwa." Wani murmushi Junaid yayi wanda ya tsaya iya fatar bakinsa yana girgiza kai yana faɗin. "Wai shin idan muka yi aure me zaki bani a matsayinki na amaryata Khairiyyah? Shin menene naki ne ban sani ba tun a titi? menene shi da kika hanani gani ko taɓawa Khairi?" Wannan karon idanun Khairiyyah sun kada sunyi wani irin canja kala da alamar maganganun Junaid Dikko ba ƙaramin tafasa mata zuciya sukayi ba, ɗan farin cikin dake kwance cikin fuskarta lokaci ɗaya ya ɓace bat. "Ki dawo cikin hankalinki Khairiyyah... ki dawo cikin tunaninki saboda kinsan ko kafin na sanki dama ban san maza nawa kika sani ba, ke kinfi kowa sanin cewa kafin ni kinyi mu'amala da, wasu, haka koda muna yi kina kula wasu still ba dainawa kikai ba, kuma ke kinsan bazamuyi aure ba na sha gaya miki, saboda ko a mafarki ko a gaske hakan bazai taɓa faruwa ba dan ni tuni na riga da nayi aure na Khairiyyah, so dan Allah dan Annabi kibar rayuwata kibarni haka na samu peace of mine na rayu da matata cikin kwanciyar hankali.!" Wannan karon kallonsa kawai take hawaye da gudu ke sauka cikin fuskarta tana jin zuciyarta nayi mata wani irin mugun zafi. Lokaci ɗaya ta fashe da dariya still hawaye na rolling cikin fuskarta. Kalmar yayi aure tana zauna mata wurare da dama acikin zuciyarta da wani irin ciwo mai girma. Cikin wani yanayi take cewa. "Ka dai ce min kawai baxaka aureni ba ka daina yaudarar kanka da cewar kayi aure saboda ni nasan babu macen da xatayi kasadar aurenka dan ni kawai aka halicceka Junaid Dikko, bari kaji na gaya maka babu macen da ta isa ta shiga wannan fadar taka, babu wata shegia da zata amsa sunan matar Junaid Dikko sai ni.." Ta faɗa tana zaro masa duka idanunta masu cike da rashin ganin kima. Murmushi yayi yana ta kallonta kafin yace mata. "Well Khairi ni dai nasan da gaske nake yi, so it's your own Ki Yadda Ko kada ki yadda Khairiyyah da gaske munyi auren sunna da Jiddah tsawon watanni shidda kenan, yanzu ma haka tana ɗauke da ciki na ajik....." Ai kafin ya qarasa abinda yake son amayarwa Khairiyya ta ɗaukesa da mari ta kara ɗaukesa da wani marin, with shock yake kallonta yana miqewa tsaye dan yaga kamar bata cikin hankalinta. Kafin ya yi wani abun taci kwalar rigarsa tana faɗin. "Karka ce min ka auri wata mace bani ba Junaid, kayi gaggawar ce min wasa kake yi domin kuwa wasannan ya yi matukar yin muni." Junaid kawai ya tsaya yama rasa wane irin hukuncin zai yi mata. Muryarta ya sake ji tana jijjiga shi a haukace. "Baxaka aureni ba wacece mai wannan karfin halin da har ta aure ka? ka faɗa min wacece ita?" Ta faɗa a tsawace tana wani jijjigasa tamkar mai jinnu. Hannunsa biyu yasa ya fisge hannayenta yayi masu riqon da bazata iya kwatar kanta ba, shima ransa a mugun ɓace yake faɗin. "Ki dawo cikin tunaninki Khairiyya kisan waye a gabankin." Wani uban ashar ta lailayo masa ta uwa ta uba ta fisge riqon da yayi mata ta buɗe masa ido tana faɗin. "Toh ko uwarka bata isa ta hanani aurenka ba bari kaji na gaya maka. Sannan ni da kai shege ka fasa." A fusace ya fisgota ya kaiwa fuskarta mari ya turata da dukkan karfinsa, a tsorace Mami ta riqe Khairiyyah tana kallon Junaid wanda kamanninsa suka canja lokaci ɗaya. Bai taɓa da Yasànin sanin Khairiyyah ba a cikin rayuwarsa irin wannan lokacin. Yau Mamman sa take zagi agabansa saboda ya taɓa haɗa jiki da ita ya zubar da duk wani girmansa. Hauka ta riqa yiwa Mami da kawarta dake riqe da Khairiyyah. A mugun fusace Junaid ya juya ya nufi hanyar barin parlorn yaji ance. "Dan ubanka ka dawo kaga yadda ake hauka a gidan nan, kuma ka shiryawa aurena kota arziki kota bala'i wallahi, kuma duk wanda kakeso haka za'ayi ka fadawa shegiyar ƙaruwar da ta manne maka sai na lalata rayuwarta."

FOLLOW MY ACCOUNT IN AREWA BOOK
EXCLUSIVE PAGES(arewa book)

VIP 1K
NORMAL GROUP 500

My WhatsApp number
(08086207764)





#ASMY B ALIYU

#BA(secret Relationship)

#Love, Romance and Destiny

#Junaid Dikko

#khairiyyah

#Jiddah

BOYAYYAR ALAƘA (the secret relationship)Where stories live. Discover now