FREE PAGE.
Assha ta koma sai kuma ta fito sanye da hijab pink har ƙasa wanda ya qarawa fuskarta wani irin kyau, a hankali ta zauna gefen yaayanta tana gaishesa. Ya amsa yana kallon fuskarta yake faɗin "Bacci kou ?" Ta ɗaga masa kai, yace "Ina maganar barci keda zaki shiga school kin san kuwa yanzu qarfe nawa?" Ta ɗan turo baki tana faɗin "Babu hutu gabaki ɗaya Yaaya, ko baccin kirki banayi ni na kosa ma na fara zuwa jami'a, sai naga dama zan shiga lecture babu mai cemin don me." Murmushi sukai daga Abba har Junaid.
Kai Junaid ya shiga kaɗa mata yana faɗin “Waya faɗa maki karatun jami'a yana da sauqi?" Assha dikko tayi Rolling eyes ɗinta tana faɗin "Ba dai ina ganin yadda Amaah keyi ba har 10 take kawai tana baccinta haka da dare sai takai 1 tana kallo, kai bawa wa ya baka ƙwarin gwiwar duka yin waɗannan abubuwan Yaya Junaid?" ta faɗa tana wani kwantar da kai, murmushi kurum Junaid yayi gamida jan dogon hancinta, sallama tayiwa yayan nata shida Abba, ta koma ɗaki dan shirin zuwa school.
Wuraren ƙarfe goma ta soma buɗe idanunta da hasken rana ya gama haske fuskarta, wata irin miqa ta saki tana lalubar inda zataji Junaid, sai dai wayam taji wurin da yake, idanu ta buɗe sannan ta miƙe zaune tana riqe kanta, a daren jiya ba ƙaramin wahala tasha hannun Junaid dikko ba duk Jarabarta da kaunarta da son sexxx idan tana gado ɗaya da Junaid dikko raina kanta takeyi har mamaki take ta yadda bata iya ɗauke buqatarsa duka, kalamansa ne suka fara dawowa cikin kunnuwanta "Kina son mu zama abu ɗaya Khairiyya amman bakya iya ɗauke bukatata? Banga amfanin wannan mugun kishin naki ba ki barni na nemi wasu matan wanda zan biyasu su sauƙe min da duk wata bukata dake manne a marata."
A halayyarta tana mugun kishin Junaid dikko, wanda shi baya so "Kishinka ba ƙaramin abu bane da zan iya ragesa lokaci ɗaya, nayi maka uzuri amman muddin ina garin Katsina baka isa ka raɓi wata maccen ba, duk ranar kuwa da naga macce ajikinka wallahi tallahi sai na kasheta!" Tana tuno wasu kalamai da ta taɓa faɗa masa a wani dare suna tare sai taji yana ƙiranta da sunan wata yarinya, ranar yaga tashin hankali da masifar Khairiyya, fuskarta ta shafa da hannayenta, hango farar takarda tai akan bedside na drawer hakan yasa ta ɗan matsa gafda wajen, hannu ta saka ta ɗauka tana warwarewa a hankali.
"Kin buɗe baki kina bacci, munyi sammako da Abba zuwa Abuja idan mun sauƙa zan ƙira take ur time." Wani murmushi take saukewa a hankali,
nan ta ɗau ki wayarta tana duba sakunan dake shigowa cikin harda alert ɗin Junaid da yayi mata na kuɗi, kai tsaye toilet ta wuce ta sakarwa kanta shower, daman sallah ba damunta yayi ba sai ma idan tana tare da Junaid ɗin ne take ƙoƙarin yi kasancewar Junaid yana da ibada sosai musamman a ɓangaren sallah zata iya bada shaidarsa ta wannan ɓangaren dan salloli biyar basa wucesa.
Sun isa Abuja sai kusan ƙarfe goma na dare ya samu ƙiran Khairiyya dan bai samu kansa ba sai bayan sallar magrib kuma suna tareda Abba har lokaci yanayin muryasa da Khairiyyah taji ne yasa ta tabbatar akwai gajiya a jikinsa dan itama bayan ta shirya aranar ta bar Katsina, a kasale tace “Mine ka gaji sosai ga muryarka nan yana shaking.” Ta faɗa masa cikin sanyin murya, babu abunda yake buqata irin wannan lokacin yaji macce ajikinsa, jira kawai yake ya samu Abba yai barci ya fita shima dan Abuja ba bakon wurinsa bane so yake ya fita ko zuwa asuba ne sai ya dawo.
“Khairiyya bacci nakeji na gaji." Ya faɗa mata cike da gajiya a muryarsa.
“Hope a gida zaka kwana ba'a hotel ba?" Tayi masa tambayar tanajin wani kishi na sake danne mata zuciya “Ina gida tare da Abba.” Yana jin yadda take sauƙe ajiyar zuciya “Toh na tayaka hira mana har ka samu barci?” Ta faɗa da kalar muryar da take yi masa magana na jan hankali “Na baka labari?”
“Khairi please!”
“Mine nasan macce kakeso yanzu, karka fara duka awanmu nawa da rabuwa ko ka manta kwana kayi aikana? Wai meyasa baka gajiya ne? Sai da na faɗa maka idan bazaka iyaba zan biyoka."
“Khairi kiyi shiru dan Allah kaina ya fara ciwo.”
“Owk sai da safe." Ta faɗa tana katse ƙiran ba tare da ta jira me zaice ba, kwanciya yayi akan bed yana rufe duka jikinsa da duvet kamar ma zazzaɓi ne yakeson rufesa dan wani irin sanyi yakeji tun daga cikin tafin ƙafarsa har tsakiyyar kansa.
Ƙarfe biyu na dare sai juyi yake a kan bed ɗinsa, yana jin yadda jikinsa ya ɗau ki wani kalar dumi ga mararsa da yaji tayi masa wani mugun nauyi, kamar wanda ya sha wani abu, a hankali ya sauko daga kan bed ɗin, dakyar ya saka casual slippers a kafansa hannunsa na dafe da wandonsa ya nufi kofa, kai tsaye kitchen ya nufa ya fara duba cikin fridge yana addu'ar samun lemun tsami, dakyar ya samu kwara biyu anan cikin kitchen ɗin ya haɗa coffee tare da jefa lemun aciki parlour ya dawo ya xauna, kusan minti goma sa'annan ya kafa kai ya wani runtse ido sai da yaji babu komai cikin cup ɗin saannan ya sauƙe, wata irin zufa ya shiga haɗawa lokaci ɗaya, anan kan doguwar sofa da yake zaune cikin parlor ya kwanta tare da jingina bayansa yana sauke wani numfashi, duka daren baccin wahala yayi sai dai still bai makara sallar asuba, ƙiran sallar farko ya buɗe idanunsa, tare sukaje massalaci da Abba, sannan tare suka dawo Abba.
Suna tafe Abba yana faɗin ya kwanta ya huta zuwa 10 zasu fita, shima zai ƙara kwanciya dan wani irin ciwon ɓarin kai kansa keyi "Ko sai kaga likita ne Abba?" Abba ya girgiza kai yana faɗin “ No! Nasan bacci ne idan na tashi zai wartsake kafin nan kayi mana order na break fast." Nan ya ɗagawa Abba kai alamar bin umurninsa sai da yabi bayan Abba har ɗakin barcinsa ya tabbatar da ya koma barci sannan ya fito ya nufi nasa ɗakin, wani wankan ya sakeyi ya saka kananun kaya ajikinsa ya ɗau ki car key, agoggo ya kalla yaga kusan ƙarfe bakwai nan ya fice daga gidan.
Kwance take tana juyi a gado a katafaren hotel ɗin da ya kama musu, wayar Junaid dikko dake gefen pillow ta ce fara ringing ɗaukar wayar tayi tana duba sunan, Khairi taga an saka ɗan taɓe baki tayi ta ɗaga wayar tana faɗin "Sorry mai wayar baya kusa ya shiga wanka." A wani irin fusace Khairiyya ke faɗin "Ke wacece kuma me kike da wayarsa da safen nan?" Khairiyya ta faɗa sounding very harsh a muryarta, har zata buɗe baki tayi magana taji qarar buɗe kofa, alamar ya fito daga wanka.
Junaid sanye yake da ƙaramin towel a waist ɗinsa sai ƙaramin dake bisa kansa yana goge gashin kansa dashi, da mamaki yake bin wayarsa da ke hannunta da kallo a wani irin fusace ya ƙaraso ya fisge wayar still Khairiyya na kan layi.
Wani mugun kallo ya watsa mata kafin ya fice daga ɗakin zuwa parlor.
"Khairiyya!" Ya faɗa can qasa maqoshi "Wacece wannan? Me take da wayarka?" Sau nawa zan riqa ansa maki wannan tambayar tunda kin san wacece ni bai zama dole kullum sai kin tambaye ni ba."
"Meyasa kakeyin haka Junaid?" Yana iya kirga sau nawa Khairiyya ta ƙira sunansa cikin rayuwarsu " Bana son rigima zuwa anjima zamuyi magana." Tun kafin ya katse wayar ta katse wayar.
A fusace ya koma ɗakin ya kalleta da masifa cikin idonsa yake faɗin "Meyasa zaki taɓa min waya?"
Ta haɗe rai tana faɗin "Ƙira fa tayi na ɗaga da niyar na faɗa mata baka kusa, shine zata riqa faɗamin bakaken maganganu, idan matar ka ce meyasa ta kasa riqeqa kake bin wasu matan?"
Yarinyar tana gama faɗa a fusace ta shige toilet, da wani irin kallo ya bita a gurguje ya shirya ya aje mata kuɗaɗenta akan bed ko sallama bai tsaya yi mata ba ya fice daga room ɗin.
Eatery ɗin dake cikin hotel ɗin ya tsiya yayi masu oder breakfast shida Abba, koda ya ƙarasa gidan kusan goma saura, addua kurum yake aransa Allah yasa Abba ba ya parlour har ya shiga cikin parlourn baiji motsin Abba ba, kan dinning ya qarasa ya aje ledojin da ya taho masu dasu sannan jiki a sanyaye ya nufi ɗakin barcinsa, kayan jikinsa ya canja ya shirya kansa cikin bakaken Japanese suit, gefen bed ya zauna yana ƙoƙarin kiran Mamma a waya line busy yaji ana nuna masa miqewa yayi tsaye gamida ficewa a ɗakin.BOYAYYAR ALAƘA is 500
Account Details
0004157137
Jaiz bank
Asma'u Buhari Aliyu
Shaidar biya ta 08086207764Katin wayar MTN ta 07043079282 shaidar biya ta 07065283730
#ASMY B ALIYU
#BA(secret Relationship)
#Junaid DikkoVIP 1K
NORMAL GROUP 500