ƘARA'IN INNA DELU

67 1 0
                                    

ƘARA'IN INNA DELU
        💄💄💄💄

              NA

  MAMAN AFRAH

FCW

  *NI CE DAI NA NISHAƊANTAR DA KU A LITTAFINA ƳAR ZAMAN WANKA YANZU NA DAWO DA  ƘARA'IN INNA DELU*

ƳAR ZAMAN WANKA TA TAFI MAI ƘARA'I TA ZO
😂😂😂😂😂😂

           Page5⃣➡6⃣

   Ƙarasowa ya yi ya zauna Inna tana ta washe baki tare da masa marhabin. Bayan ya gaisheta take tambayarsa ɗan nasa ɗan gidan Maryam ɗin yake sanar da ita ai daga makaranta gidan mahaifiyarsa ya kai shi.

"Yo ke ko ruwa bakya kawo masa ba kika zauna kina wani muzurai tamkar wacce ta yi wa sarki ƙarya sai wani zumu-zumu da baki kike kamar shazumamu ya samu sikari" Cewar Inna da ta lura da ɓacin ran da maryam ɗin ke yi tun shigowar mijin nata ita dai ta san dalilinta na yin hakan. Fuuu ta tashi ruwan ta tafi ta ɗakko masa da ido ya bi ta yana mamakin sauyin da ya gani a tare da ita, a plate ta kawo masa tare da masa sannu da zuwa cikin sakin fuska ya amsa yana ɗaukan ruwan ya tilla ya sha ya mayar da ledar kan plate ɗin da yake pure water ne.

"Wannan matar taka ta koyi mugun hali wallahi"

"Mugun hali kuma Inna?"

"Eh mana kai baka lura da muzuran da take ba tun shigowarka in ba mugun hali ba mene ne, da kuma baƙin ciki ta rasa abokiyar hassadarta sai uwar da ta haifeta ai ko idanunta ka kalla za ka ga sun yi luhu-luhu, to kuka ne ta yi ta garƙamawa kamar dai ranar da ubanta Malam ya bar duniya"

"Subhanallahi mai ya yi zafi Inna" Ya tambaya da mamaki.

"Maza Maryama ki yi ta hararata amma wallahi harararki ba za ta hana ni faɗin abin da ke raina ba" Cewar Inna tana wani gatsina fuska ta maida kallonta kan mijin Maryam ɗin.

  Jin haka Maryam ta tashi da sauri ta shige ɗaki dan ta san yunzu Inna za ta fara ɓaran-ɓaramar magana kuma babu mai taka mata birki sai ta kai aya sai dai ta san yau abin kunya ne za ta gama ja mata a wajen mijinta.

"Inna idan laifi ta miki ai sai ki ja mata kunne...

"Yi shiru ɗan nan bakinka alekum, ai ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wajen faɗa maka komai da komai,dama tun tuni nake jiran zuwanka in yaso ko addu'a ce sai ka taya ni a kan Allah ya mini mafita ya ganar da yaran nan gaskiya gaskiya ce ƙarya kuma ɓata ce" Ta katse shi tana rattabo bayaninta.

"Yarinyar nan Maryama da ƴan uwanta ne suke son yin kisan kai...

"Subhanallahi, kisan kai fa Inna amma dai na tattabara ko?"

"Kai dallah ja can, ana maka maganar mutane kana maganar tsuntsaye, to bari na maka gwari-gwari  dan na tuna kisan zuciyoyi ya kamata in ce"

"Inna ban fahimta ba, sai ƙara ɓatar da  ni kike, kin ce kisan kai kin ce na zuciya...

"Na gama shiryawa" Cewar Maryam da ta ɗakko jakarta ta fito daga ɗaki dan duk abin da ake faɗa tana jin su.

"To uwa gwadaga babu inda zai je sai na gama faɗa masa abin da ke raina wato shi ne kika ɗakko wata shegiyar jakarki mai kama da zabirar aski, wai kin gama to sai dai ki jira shi ya gama shi ma"

"Haba Inna ki bari mu tafi mana yana da uzuri fa "Ta faɗa tana zunɓura baki tare da komawa ɗaki dan ta ga mijin nata ya saki baki cikin rashin fahimtar takamaiman abin da ke faruwa.

"Uzuro, na ce uzuro, ko uzuri gare shi ba ya ƙi kin nawa uzurin ba ai" Ta faɗa tana hararar Maryam ɗin har ta shige ɗaki.

"Ɗan nan ina kai ka, kana jina, Maryma da Yayunta su ne suke so su daƙushe zuciyoyi guda biyu haka kawai fa dan na ce zan yi aure, saboda son tauye mimi haƙƙi da kuma neman dalili suke so su dakatar dani wai na tsufa, dan na tarasu na sanar musu tunda na kammala takaba in yi aure, ni ma in huta idan da rabon haihuwa ma ba sai a yiwa mai ɗakin naka ƙanwa ko ƙani ba, to fir suka ƙi,  yo daɗi ta musu ake lissafani cikin zawarawa bayan ga ƴan matan nan da zawarawa sun rasa mazajen aure amma ni Allah ya bani mijina a hannu amma dan kawai su shiga haƙƙina sai su ce babu maganar aure wai sai dai in zauna in ke sallah da salatin annabi kamar da can ce musu aka yi ba na yi. Ni a ganina ai gwara dai in mutu a ɗakin aurena, in banda ƙoƙari faɗawa mijin baya tariya, meye a ido banda ruwa, abu lami ba ɗaci ba, banda ma ɗaukan alhaki ɗanka ya hanaka sunnar ma'aiki, to shi ne na ce ko kai za ka mini WALI (Alwali) Tun da su banga kyan wuri a kunnen jaka ba, sai in baka sadakin ka je ka tara mutane su ɗaura mana aurenmu ni da Jauro, ai dai in an ɗaura cikinsu babu mai sincewa tun da igiyar sakin tana hannu Jauro, shi kwa na san ko duniya za ta taru ko ana ha maza ha mata kai ko da wuƙa aka saka wa Jauro a wuya ba zai sake ni ba gwara ka je a ɗaura dan bana fatan na shiga jerin wanda za su rataye kansu saboda soyayya su mutu a jefa su a wuta ko ya ka gani Sammani meye laifina a nan" Cewar Inna tana kafe sirikin nata da ido, dan shi tun daga lokacin da ta ambaci aure ya saki baki yake kallonta dan har ta gama rattaba bayaninta mai kamar almara leɓɓansa basu haɗu ba suna nan a buɗe, tsabagen mamaki.

ƘARA'IN INNA DELUWhere stories live. Discover now