ƘARA'IN INNA DELU

59 1 0
                                    

ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄
        
         NA

  MAMAN AFRAH

FCW
        
  
  ƘARA'IN INNA DELU
         

             Page 1⃣7⃣➡1⃣8⃣

  A fusace ya shigo wurin yana shigowa ya yi wurgi da ƙarfen hannunsa rai a matuƙar ɓace. Yana shigowa idanunsa suka sauka a tsakiyar kan furfurar amaryarsa kan nan kawai yake hangowa tana daga  durƙushe Shattu da Lantana suna ta faman ta tashi amma kunyar yadda rigarta ke a ɓarke ga babu bireziya dan hannun ɗaya bireziyar ma ya maƙale a jikin ɗankunnenta, ga ihun da wajen ya karaɗe wurin ranta in ya yi dubu ya ɓaci yadda gashin kanta da ta san ko kitson kirki babu a jiki dama hular gashin da aka saka ita ce rufin asirin kan sai kuma saurayin nan ya cire mata dan ya kunyata ta a gaban jama'a.

"Ya Allah kai ka san karatun kurma, ranar ƘARA'IN nan da na ci buri a rayuwata, tun da aka ɗaura auren nan ko barcin kirki bana yi sabo da ɗoki amma a ce yau tun daga farkon shigowarmu muka sha ƙasa ni da ango na anya ba hannu aka saka mini ba, wani ɗan hana ruwa gudu, wato sa'idinawa wanda ana ruwa suna irgawa" Cewar Inna a ranta zuciyarta na ƙuna.

"Jama'a ku kauce, ku jaye ga ango nan da ƙarfin gwiwarsa ya dawo daga filin dagar ya je ya ɗauki fansa ya dawo" Cewar MC a lasifika.

"Ka ji ɗan jaraba, in banda dai neman magana fansar me na ɗauka in banda jikina da ya faɗa mini, kan nan nawa kamar na ɗauki duron kananzir, ai ba dan ba dan ba da na ce wannan ƙara'i ban ji daɗinsa ba" Ya faɗa a ransa lokacin da ya ƙaraso wajen yana aikawa MC wata muguwar harara kamar dai shi ya ce ya bi bayan saurayin.

"Ɗan tsoho ƙyamus-ƙyamus ba ni na ce ka yi auren ƙara'i ba kuma ba ni na saka ka bin saurayin nan ba, ka ga kuwa ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Ya faɗa a ransa yana saki wata ɓoyayyar dariya.

  Cikin hanzari Jauro ya nufi inda su Shattun da Inna da Lantanar suke. Su Kande da Karima kuwa sun daɗe da cikawa rigarsu iska dan tun lokacin da ta watsa manjan ta shige ƙasan kujerun da ke wajen shi sa ba a ganta ba, bayan hankalin mutane ya koma wajen Inna da saurayin  sai ta fito suka silale suka fice daga wajen, daga nan kuwa garinsu suka koma dan dama Jauro ya ce sai ranar da amarya za ta tare za ta dawo gidan da zama.

  Yana zuwa Shattun cikin sanyin murya ta ce

"Yawwa ango, ka ganta nan sai fama muke da ita ta ƙi tashi" Wani haushin Shattu ne ya cikawa Jauro ciki da ta kirashi da suna ango, dan shi a yadda jikinsa yake a damule da manja kai da cillukutu ko abokin ango bai ci a ce an kira shi ba bare ango, gashi ji ya yi kamar ya zabgawa Shattu da Lantana mari da suka bar Delunsa a wajen ai da ko cicciɓarta sun yi sun kaita wani ɗaki.

   Hannu kawai ya miƙa ba tare da ya ce uffan ba, Delu da ke durƙushe kanta a ƙasa sai ji ta yi an sure ta an yi sama da ita, sosai ta tsorata dan tunaninta wani ne cikin samarin wurin a sure ta gabaɗaya zai gudu da ita ya mata fyaɗe, dan sosai ta tsorata da lamarin abin da saurayin nan ya mata, sannan bata zaci Jauro zai iya ɗaukanta ba. Tana ɗan ɗago fuska ta sauketa a kan fuskar angon nata da ta sha manja abinta sharkaf, kamar daron da ake siyar da manjan wani tausayin kansu ne ya kama Inna Delu ganin halin da suka tsinci kansu a ciki a yau da ta kasance ranar farinciki.

"Bebi in ce dai ka sumar da shi da ƙarfen nan?" Cewar Inna tana kallonsa. Ai maganar nan da Inna ta faɗa Jauro ji ya yi wani kishi ya ƙara taso masa gashi ba ya so ya faɗa mata gaskiya ta ga ragwantarsa dan haka sai ya ce

"Ai na masa illa, ma dakyar mutane suka ƙwace shi, yana can lange-lange aka tafi da shi asibiti" Ya faɗa yana kallon gefe dan kar ta gano ƙaryar da ya sheƙa mata. Wani daɗi ne ya baibaye Inna jin an ɗau mata fansa hakan ya sanya ta ƙara jin ƙaunar Jauro a ranta.

ƘARA'IN INNA DELUWhere stories live. Discover now